Rigima Ta Kare, An Janye Karar da Aka Nemi Tsige Gwamna a Kotun Kolin Najeriya
- An kawo karshen shari'a kan zaben gwamnan jihar Ondo wanda aka gudanar ranar 16 ga watan Nuwamban 2025
- Dan takarar gwamnan PDP, Agboola Ajayi ya janye karar da ya shigar a gaban kotun koli bayan ya sake nazari da tunani
- Kotun mai daraja ta farko a Najeriya ta yi watsi da karar gaba daya tare da tabbatar da nasarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Ondo - Ɗan takarar jam’iyyar PDP a zaɓen gwamnan Ondo da aka gudanar ranar 16 ga Nuwamba, 2024, Agboola Ajayi, ya janye ƙarar da ya shigar a Kotun Koli.
Mista Ajayi, wanda ya rike mataimakin gwamna a mulkin marigayi Rotimi Akeredolu, ya hakura da kalubalantar nasarar da Gwamna Lucky Aiyedatiwa na APC ya samu.

Source: Twitter
Jaridar The Nation ta tattaro cewa Ajayi, shi ne babban ɗan hamayya da ya fafata da Aiyedatiwa a zaɓen da ’yan takara 16 suka shiga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An janye karar da aka shigar kan zaben Ondo
A cikin wasiƙar da ya aike wa babban rajistar Kotun Koli, Ajayi ya tabbatar cewa ko da yake an riga an shigar da ƙara a madadinsa, ya yanke shawarar janyewa.
Ya bayyana cewa ya dauki wannan mataki ne bayan yin shawarwari da iyalansa, abokansa, ’yan jam’iyya da lauyoyinsa.
"Bayan dogon nazari, mun cimma matsaya cewa ya kamata mu janye karar, don haka na yi hakan.
"Kasancewar na yi aiki a matsayin mataimakin gwamna da kuma ɗan majalisa, babban burina shi ne kyakkyawan shugabanci da zaman lafiya a jihar Ondo da Najeriya baki ɗaya.
"A cikin wannan yanayi, ina mika sakon fatan alheri ga Gwamna Lucky Orimisan Aiyedatiwa wanda ke jagorantar jiharmu, kuma zan ci gaba da bayar da gudunmawa ga cigaban Ondo da ƙasa.”*
- Agboola Ajayi.
Kotun Koli ta yanke hukuncin karshe
Bayan haka ne Kotun Kolin ta yanke hukunci watsi da karar sakamakon janyewar Ajayi tare da tabbatar da nasarar Gwamna Aiyedatiwa.

Kara karanta wannan
Malami ya shiga rikici da gwamna, ana zarginsa da ingiza ta'addanci a jihar Kebbi
Tun da farko, Kotun Daukaka Kara reshen Akure ta yi watsi da ƙarar da Ajayi ya shigar da Aiyedatiwa da mataimakinsa, Olayide Owolabi Adelami.

Source: Twitter
Kotun ta bayyana cewa Ajayi ba shi da hurumin shigar da ƙarar, sannan ƙarar ta wuce lokacin da doka ta tanada, cewar rahoton Channels tv.
Da wannan janye ƙara, an rufe shari’ar zaɓen gwamna ta 2024 a jihar Ondo, abin da ya ƙara tabbatar da sahihancin kujerar Aiyedatiwa.
Masu nazari sun bayyana cewa wannan janye ƙara ya kawo ƙarshen ɗaya daga cikin manyan shari’o’in zaɓe mafi zafi a tarihin jihar.
Gwamnan Ondo na rigima.da Minista?
A wani rahoton, kun ji cewa Ministan Harkokin Cikin Gida, Dr. Olubunmi Tunji-Ojo, ya karyata rahotannin da ke cewa akwai sabani tsakaninsa da Gwamna Aiyedatiwa.
Tunji-Ojo ya bayyana irin wannan jita-jita a matsayin maganganunnshafukan sada zumunta marasa tushe da hujja.
Ya ce babban abin da ya fi mayar da hankali a kai shi ne tallafa wa shirye-shiryen da za su ƙara nuna nasarorin Shugaba Bola Tinubu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng
