Dogara Ya Bankado Abubuwan da Ya Ce Buhari Ya Lalata kafin ba Tinubu Mulki
- Yakubu Dogara ya ce gwamnatin marigayi Muhammadu Buhari ta lalata tattalin arzikin kasa da buga takardun kudin masu tarin yawa
- Dogara ya bayyana cewa rancen kasashen waje da aka dauka don karfafa Naira da habaka tattalin Najeriya an yi su ne ba tare da basira ba
- Ya yabawa sababbin manufofin tattalin arziki na gwamnatin Bola Tinubu da ya ce suna kara kawo cigaba da samar da adalci da daidaito
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban majalisar wakilai, Yakubu Dogara, ya soki gwamnatin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari bisa zargin lalata tattalin arzikin Najeriya.
Dogara, wanda yanzu shi ne shugaban NCGC, ya yi wannan jawabi ne a Abuja yayin wani taro da Majalisar Wakilai ta shirya.

Source: Facebook
Tribune ta wallafa cewa ya ce matakan tattalin arzikin da aka dauka a lokacin gwamnatin Buhari sun jefa kasar cikin mawuyacin hali, musamman ta hanyar buga kudi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dogara ya zargi Buhari da buga kudi
Dogara ya bayyana cewa sama da Naira tiriliyan 22.7 aka buga aka zuba cikin tattalin arziki a lokacin Muhammadu Buhari.
Ya ce tsarin musayar kudi da aka yi a baya ya ba wasu mutane damar samun riba mai yawa ba tare da samar da wani kaya ko sabis ba.
Dogara ya yabawa gwamnatin Tinubu
A cewarsa, lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya hau mulki, tattalin arzikin Najeriya ya riga ya zama “gurbatacce” kuma yana bukatar sauyi da gaggawa.
The Guardina ta wallafa cewa Dogara ya ce daga ranar farko, shugabancin Tinubu ya dauki matakai na gyaran tattalin arziki domin kauce wa rugujewar kasa.
Ya bayyana wadannan matakai a matsayin masu muhimmanci ga ci gaban Najeriya, wanda zai shafi ilimi, kiwon lafiya, tsaro da kuma gine-gine.
Manufofin gyara harajin Tinubu
Dogara ya bayyana kafa kwamitin Shugaban Kasa kan manufofin haraji da Dr Taiwo Oyedele ke jagoranta a matsayin muhimmin mataki na sauya tsarin kasa.
Ya ce kwamitin ya fito da shawarwarin sauye-sauye masu tasiri da za su canza dokoki da ka’idojin da suka tsufa domin samar da adalci da daidaito.
Sai dai ya jaddada cewa duk wani gyara na tattalin arziki yana fuskantar kalubale daga wadanda suke cin gajiyar tsohon tsarin.

Source: Facebook
Kalubalen aiwatar da sauye-sauye
Dogara ya ce an fuskanci adawa mai tsanani daga bangarorin da ke amfana da tsofaffin dokoki da tsarin tattalin arziki.
A cewarsa, nasarar sauye-sauyen da ake son cimmawa na bukatar dabaru, jajircewa da kuma hadin kan masu ruwa da tsaki domin cimma burin kasa.
Dattawa za su yi wa Tinubu kamfen
A wani rahoton, kun ji cewa wasu dattawan APC a jihar Ondo sun yi alkawarin yi wa shugaba Bola Tinubu kamfen a 2025.
Dattawan sun bayyana cewa sun dauki damarar yi wa Bola Tinubu kamfen ne domin ya samu damar karasa ayyukan da ya fara.
Sun tabbatar da cewa za su shiga lungu da sako domin sama wa shugaban kasar kuri'a da ba za ta yi kasa da miliyan 1.5 ba.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Asali: Legit.ng

