"An Yi Watsi da Ni," Dan Majalisa Ya Tattara Kayansa Ya Fice daga Jam'iyyar APC

"An Yi Watsi da Ni," Dan Majalisa Ya Tattara Kayansa Ya Fice daga Jam'iyyar APC

  • Jam'iyyar APC ta rasa dan Majalisa daya tilo da take da shi a Majalisar Dokokin Jihar Abia, Hon. Akaliro Kelechi Anderson
  • 'Dan Majalisar ya tabbatar da sauya sheka daga APC zuwa LP a wata wasika da ya aika wa shugaban jam'iyyar na karamar hukumar Umuahia ta Arewa
  • Ya bayyana cewa ya dade yana nazari kan salon mulkin Gwamna Alex Otti, wanda kuma ya gano cewa mutum ne mai son ci gaban Abia

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Abia - Ɗan majalisar da ke wakiltar Umuahia ta Arewa a majalisar dokokin Jihar Abia, Hon. Akaliro Kelechi Anderson, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar APC zuwa LP.

Wannan lamari ya kara girgiza jam'iyyar adawa ta APC wacce ke lokarin farfadowa gabanin zaben 2027.

Hon. Akaliro Kelechi Anderson.
Hoton dan Majalisar Dokokin Abia, Hon. Akaliro Kelechi Anderson
Source: Facebook

Dan Majalisa ya mika takardar barin APC

Kara karanta wannan

"Za mu yi farin ciki," APC ta ja hankalin gwamna, ta nemi ya fice daga jam'iyyar PDP

Jaridar Leadership ta tattaro dan Majalisar ta tabbatar da komawa LP ne cikin wasikar da ya aika wa shugaban APC na karamar hukumar Umuahia ta Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hon. Akaliro ya danganta wannan mataki da ya ɗauka ga rikice-rikicen cikin gida, rabuwar kai, da kuma rugujewar tsarin shugabanci a APC ta jihar Abia.

Rahotanni sun nuna cewa Hon. Akaliro, wanda ke shugabantar kwamitin majalisa kan korafe-korafe da shari’a, shi ne kaɗai ɗan APC da aka zaɓa a zaɓen 2023.

Abin da ya sa dan Majalisar ya bar APC

Duk da haka, dan Majalisar ya koka cewa jam’iyyar APC ta yi watsi da shi tun da aka rantsar da shi.

A ruwayar Daily Post, dan Majalisar ya ce:

"Tun daga lokacin na hau mu'ki, APC a Abia ba ta taɓa gayyata ta, a hukumance ko a ɓoye zuwa wani taro ko aiki ba, hakan ya nuna ba ni da amfani da wurinsu.

Ya kuma soki yawan rikicin APC tsakanin shugabanni musamman yadda bangaorori biyu ke dakatar da juna tun daga matakin mazabu zuwa kananan hukumomi.

Hon. Akaliro ya bayyana wannan rikici da ya dabaibaye APC a matsayin “alamun rabuwar kai da ba za ta iya gyaruwa ba.”

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe Sarkin da suka yi garkuwa da shi, sun jefar da gawarsa a daji

Bayan ya gudanar da abin da ya kira tattaunawa da magoya bayansa da ma’abota siyasa a yankinsa, Akaliro ya ce ya yanke shawarar komawa jam'iyyar LP.

Gwamna Alex Otti.
Hoton gwamnan jihar Abia, Alex C. Otti Hoto: Alex C. Otti
Source: Facebook

Hon. Akaliro ya yabawa Gwamna Alex Otti

Da yake jawabi ga ’yan jarida bayan ficewarsa daga APC, Akaliro wanda aka fi sani da “The man with excess grace”, ya bayyana goyon bayansa ga Gwamna Alex Otti.

“Yau na ga haske. Tun farko na yi kan Mai Girma Dr. Alex Choma-Otti domin na fahimci inda ya nufa. A yau na yanke shawara in tafi tare da shi a LP saboda abubuwan da ya riga ya aikata don ci gaban jihar mu.
"Abia ta fara zama lamba ɗaya a fannoni da dama. Ina alfahari na bugi kirgi na ce ni ɗan Abia ne," in ji shi.

Tsohon mataimakin gwamna ya koma LP

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon mataimakin gwamnan jihar Abia, Mista Ude Chukwu ya koma jam'iyyar LP makonni bayan ya raba gari da PDP.

Chukwu, wanda ya fice daga jam’iyyar PDP kwa nan nan, ya yi aiki a matsayin Mataimakin Gwamna a karkashin tsohon Gwamna Okezie Ikpeazu.

Kara karanta wannan

An samu bayanai daga majiyar Aso Rock kan takarar Tinubu da Shettima a 2027

Ya bayyana cewa wannan sauya sheka da ya yi zuwa LP mai mulkin jihar Abia ya bude sabon babi a siyasarsa tare da magoya bayansa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262