'Yan Hadaka Na Shirin Sauya Jam'iyya daga ADC zuwa ADA? An Ji yadda Lamarin Yake
- An yada wasu rahotanni masu nunamambobin hadakar jam'iyyun adawa, za su yi watsi da ADC don komawa jam'iyyar ADA da ake kokarin kafawa
- Mukaddashin sakataren yada labarai na kasa na jam'iyyar ADC, Bolaji Abdullahi, ya fito ya yi magana kan wadannan rade-radi
- Bolaji Abdullahi ya nuna cewa mutanen da ke son maida Najeriya kasa mai jam'iyya daya, ba za su taba bari jam'iyyar ADC ta huta ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Mukaddashin sakataren yaɗa labarai na kasa na jam’iyyar (ADC), Bola Abdullahi, ya yi magana kan jita-jitar cewa 'yan hadaka za su koma ADA.
Bolaji Abdullahi ya karyata rahotannin da ke cewa mambobin hadaka sun yanke shawarar barin ADC don rugunmar jam'iyyar ADA, wajen kalubalantar APC a zaɓen 2027.

Source: Facebook
Mukaddashin sakataren yada labaran na kasa na ADC ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da jaridar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yada jita-jita kan makomar hadaka
Idan ba a manta ba, hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ta sanar da cewa kungiyoyi 14 daga cikin 171, da ke neman rajista a matsayin jam’iyyun siyasa ciki har da ADA, sun tsallake matakin farko na tsarin rajista.
Bayan sanarwar ta INEC, wasu rahotanni sun bayyana cewa haɗakar jam’iyyun adawa da su ka rungumi ADC tun a watan Yulin wannan shekara, za su koma ADA idan an kammala rajistar ta a matsayin jam’iyya.
Me jam'iyyar ADC ta ce kan jita-jitar?
Amma a martaninsa, Bola Abdullahi ya bayyana cewa babu kamshin gaskiya a cikin wannan jita-jita.
Mukaddashin sakataren yada labaran ya kara da cewa haɗakar ta himmatu wajen mayar da ADC babbar jam’iyya ta kasa, wadda za ta kasance ainihin madogara ta dimokuraɗiyya.
"Babu wani abu makamancin haka. Mun riga mun wuce wannan mataki. ADC ce jam’iyyarmu."
- Bolaji Abdullahi

Source: Twitter
Jam'iyyar ADC ta jefi gwamnati ta zargi
Hakazalika, Bola Abdullahi, ya zargi mutanen da ke kokarin maida Najeriya a matsayin kasa mai jam’iyya ɗaya da laifin shigar da jerin shari’o’i daban-daban a kan tafiyar hadaka.
"Mun san tun daga farko cewa abinda ya haɗa mu cikin wannan haɗaka, watau waɗannan mutanen da suka tarwatsa sauran jam’iyyun adawa, ba za su bar haɗakar ADC ta yi tafiya lafiya ba tare da kalubale ba."
- Bolaji Abdullahi
Ya ce duk da wadannan kalubalen, ADC da abokan kawancenta za su ci gaba da aiki domin kafa ingantacciyar jam’iyya ta dimokuradiyya mai karfi a fadin kasa baki daya.
INEC ta amince da shugabancin ADC
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta amince da shugabancin jam'iyyar ADC karkashin jagorancin Sanata David Mark.
Hukumar INEC ta gyara sunayen shugabannin ADC a shafinta na yanar gizo, wanda hakan ya nuna akwai alamari cewa ta amince da su.
A cikin sunayen, an ga tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark da tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, a matsayin shugaba da sakatare.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


