Malami Ya Debo Ruwan Dafa Kansa, 'Yan Majalisa Sun Nemi Jami'an Tsaro su Kama Shi

Malami Ya Debo Ruwan Dafa Kansa, 'Yan Majalisa Sun Nemi Jami'an Tsaro su Kama Shi

  • Rikicin siyasar jihar Kebbi ya kara kamari tun bayan farmakin da ake zargin an kai wa tsohon Antoni Janar, Abubakar Malami
  • Tawagar yan Majalisar Tarayya daga Kebbi sun yi watsi da zarge-zargen da Malami SAN ya yi wa Gwamna Nasir Idris
  • Sun bukaci hukumomin tsaro su kama tsohon babban lauyan na gwamnati domin ya yi bayani kan abubuwan da ya fada a korafinsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kebbi - Sanatoci da yan Majalisar Wakilai daga jihar Kebbi sun bukaci hukumomin tsaro su cafke tsohon Ministan Sharia kuma Antoni Janar, Abubakar Malami.

Tawagar yan Majalisar Tarayya da suka fito da Kebbi sun bukaci a gurfanar da Malami a gaban kotun kan zarge-zargen da ake masa na tayar da zaune tsaye a makon jiya.

Sanatoci da yan Majalisar Wakilai na jihar Kebbi.
Hoton Sanata Adamu Aliero tare da sauran 'yan Majalisar Tarayya daga Kebbi a Abuja Hoto: @ameen_amshi
Source: Twitter

'Yan Majalisar Tarayya na tare da Kauran Gwandu

Kara karanta wannan

Lokaci ya kare: Babban basarake ya riga mu gidan gaskiya a Arewa ana cikin taro

Sanata Mai Wakiltar Kebbi ta Tsakiya, Adamu Alieru ne ya bayyana haka da yake zantawa da manema labarai a Abuja, kamar yadda Vanguard ta rauwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A madadin duka yan Majalisar Tarayya na Kebbi, Sanata Adamu Aliero, ya yi watsi korafin da Malami ya shigar a ranar 10 ga Satumba, 2025.

Ya kuma jaddada goyon bayansu ga Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi a ƙoƙarinsa na tabbatar da tsaro da zaman lafiya a jihar.

'Yan Majalisa sun yi fatali da korafin Abubakar Malami

Sanata Aliero, wanda sauran Sanatoci biyu da ‘yan majalisar wakilai na Kebbi suka raka shi, ya ce:

“Abubakar Malami (SAN) ya zargi Gwamna Nasir Idris (Kauran Gwandu) da wasu ‘yan siyasa da shigo da ‘yan daba, mayakan haya daga ƙasashen waje da kuma safarar makamai a asirce cikin jihar Kebbi.
"Muna son fayyace cewa waɗannan zarge-zargen ba gaskiya ba ne, ba su da tushe, kuma an yi su ne saboda siyasa.
Wani yunƙuri ne na Malami, wanda yanzu ya zama jagoran jam’iyyar adawa ta bogi a Kebbi, domin ruguza zaman lafiya da ci gaban da jama’armu ke morewa ƙarƙashin jagorancin Gwamna Nasir Idris.”

Kara karanta wannan

Ganduje ya kafa kwamiti, zai binciki gwamnatin Kano kan korar kwamandojin Hisbah 44

- Innji Adamu Aliero.

An zargi Abubukar Malami da tada hankula

Sanata Aliero ya kara da cewa suna da shaida cewa a lokacin da Malami zai je ta’aziyya a Birnin Kebbi, ya ɗauko ‘yan daba daga Sokoto, Koko da Rara don su raka shi.

Ya ce a hanya suka kai hari a ofishin jam’iyyar APC na jihar da duwatsu tare da rera kalamai marasa dadi kan mai girma gwamna, in ji rahoton Daily Post.

Abubakar Malami da yan Majalisar Kebbi.
Hoton Abubakar Malami da yan Majalisar Tarayya daga jihar Kebbi Hoto: Abubakar Malami, Adamu Aliero
Source: Facebook
"Wannan ya haifar da tashin hankali tsakaninsu da magoya bayan APC, abin da bai taɓa faruwa ba a tarihin siyasar Kebbi da aka fi sani da zaman lafiya," in ji Aliero.

Bisa haka ne, Sanata Aliero ya bukaci hukumomin tsaro su gayyaci Malami domin ya yi bayani kan zarge-zargen da ya yi, sannan su gurfanar da shi a kotu.

Zargin da Malami ya yiwa gwamnan Kebbi

A baya, kun ji cewa tsohon Ministan Shari'a, Abubakar Malami ya shigar da korafi gaban mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro da shugabannin hukumomin tsaron cikin gida.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Malami ya zargi gwamna da wasu yan siyasa da alaka da 'yan Ta'adda

Malami, wanda shi ne jagoran jam’iyyar ADC a jihar Kebbi, ya shigar da korafi kan abin da ya bayyana a matsayin shirin da ake yi na tayar da hankali jama'a.

Malami ya kuma zargi Gwamna Nasir Idris da mukarrabansa da da hannu wajen kai masa hari, tare da yin zargin cewa suna da alaƙa da ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262