"Idan Ka Isa": Jam'iyyar LP Ta Kalubalanci Peter Obi kan Zaben 2027

"Idan Ka Isa": Jam'iyyar LP Ta Kalubalanci Peter Obi kan Zaben 2027

  • Jam'iyyar LP ta taso dan takararta na shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi, a gaba kan salon siyasarsa
  • Sakataren yada labaran jam'iyyar na kasa, Abayomi Ararambi, ya bayyana cewa ba za su yi tafiya tare da Peter Obi ba a zaben 2027
  • Hakazalika, ya nuna cewa Peter Obi sa'a kawai ya samu wajen jagorantar jam'iyyar LP a shekarar 2023

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Jam'iyyar LP ta bayyana matsayarta kan ba Peter Obi takara a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Sakataren yaɗa labarai na kasa na jam’iyyar LP Abayomi Arabambi, ya bayyana cewa ba za a ba Peter Obi tikitin takarar shugaban kasa na LP ba a zaben 2027.

Jam'iyyar LP ta kalulabanci Peter Obi ya fice daga cikinta
Hoton Peter Obi yana jawabi a wajen taro Hoto: @PeterObi
Source: UGC

Abayomi Arabambi ya faɗi hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin 'Lunchtime Politics' na tashar Channels Tv a ranar Litinin, 8 ga watan Satumban 2025.

Kara karanta wannan

2027: 'Yan siyasan Arewa da za su rasa damar takara saboda kai tikitin PDP zuwa Kudu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar LP ta raba gari da Peter Obi?

Kakakin na LP ya jaddada cewa jam’iyyar na iya wanzuwa ba tare da dan takarar na ta na shugaban kasa a zaben 2023 ba.

"Za mu gudanar da harkokin zaben 2027 ba tare da Peter Obi ba, ba zai samu tikitinmu ba."

- Abayomi Arabambi

Abayomi Ararambi ya kuma yi tsokaci kan mukaddashiyar shugabar jam’iyyar ta kasa, Nenadi Usman, da kuma Aisha Yesufu, yana zarginsu da haɗa baki da Peter Obi.

Ya bayyana cewa jam’iyyar za ta ɗauki matakan da suka dace a kansu.

LP ta kalubalanci Peter Obi kan 2027

Sakataren yada labaran ya kalubalanci Peter Obi da ya fito fili ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar.

“Shirinmu shi ne mu kawar da waɗannan mutanen da su ke da tsatstsauran ra'ayi kan siyasa. Ba mu maraba da su a cikin LP."
"Tunda yanzu sun ce za su koma ADC, muna yi musu fatan alheri. Peter Obi yana da kafa ɗaya a LP, kafa ɗaya a PDP, da kuma kafa ɗaya a ADC."

Kara karanta wannan

2027: Matasa za su haɗa kuɗi, a saya wa gwamna fom ɗin takarar shugaban ƙasa

"Idan yana da yakinin cewa shi kaɗai zai iya samun ƙuri’u miliyan bakwai a zaɓen 2027, muna ba shi shawarar ya fito ya sanar da ficewarsa daga LP."

- Abayomi Arabambi

Jam'iyyar LP ga caccaki Peter Obi
Hoton dan takarar shugaban kasa na LP a zaben 2023, Peter Obi Hoto: @PeterObi
Source: Facebook

Abayomi Ararambi ya kara da cewa goyon bayan da LP ta samu a 2023 ba saboda Peter Obi ba ne, ya samu ne saboda EndSARS.

"Peter Obi kawai mutum ne da ya bayyana sakamakon gajiyar da al’ummar Najeriya suka yi da mummunan mulkin Buhari a lokacin EndSARS."
"Ya tarar da LP a matsayin abin da zai iya amfani da shi wajen kawo canji, kuma ya samu sa’a ya zama shugaban tafiyar."

- Abayomi Ararambi

Nyesom Wike ya caccaki Peter Obi

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ragargaji Peter Obi kan zaben 2027.

Wike ya taso Peter Obi a gaba ne kan alkawarin da ya yi na yin wa'adi daya idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa.

Ministan na babban birnin tarayya Abuja ya bayyana alkwarin na Peter Obi a matsayin ba komai ba face tsabagen karya da yaudara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng