Abdulmumin Jibrin Ya Yi Martani kan Korar da Jam'iyyar NNPP Ta Yi Masa

Abdulmumin Jibrin Ya Yi Martani kan Korar da Jam'iyyar NNPP Ta Yi Masa

  • Jam'iyyar NNPP a jihar Kano ta dauki matakin korar Abdulmumin Jibrin bisa zarginsa da aikata wasu laifuffuka
  • Dan majalisar mai wakiltar Kiru/Bebeji ya fito ya yi martani kan matakin da jam'iyyar ta dauka a kansa
  • Ya bayyana cewa ba a ba shi damar kare kansa ba zarge-zargen da jam'iyyar take masa kafin ta kai ga korarsa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Ɗan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Kiru/Bebeji, Abdulmumin Jibrin, ya yi martani kan korar da jam'iyyar NNPP ta yi masa.

Abdulmumin Jibrin ya bayyana mamakinsa kan matakin da jam'iyyar NNPP ta dauka na korarsa daga cikinta a jihar Kano.

Abdulmumin Jibrin ya kadu kan korarsa daga NNPP
Hoton Abdulmumin Jibrin yana jawabi a wajen wani taro Hoto: Abdulmumim Jibrin
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da dan majalisar ya sanya a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NNPP ta kori Abdulmumin Jibrin

Jam’iyyar ta sanar da dakatar da Abdulmumin Jibrin ta bakin shugabanta na jihar Kano, Hashimu Dungurawa, bisa abin da ta bayyana a matsayin yi mata zagon kasa da kuma kasa biyan kuɗaɗen jam’iyya.

Kara karanta wannan

Rikicin NNPP: Rigima ta barke a jam'iyyar Kwankwaso bayan korar da dan Majalisa a Kano

Hashimu Dungurawa ya kuma yi barazanar cewa jam’iyyar za ta kai ɗan majalisar kotu idan ya kasa biyan kuɗaɗen da ake binsa.

Wane martani dan majalisar ya yi?

Amma a martanin da ya yi, Abdulmumin Jibrin ya nemi jam’iyyar ta aiko masa da takardar kididdigar kuɗaɗen da suka rage wadanda bai biya ba.

"Ya zo a matsayin mamaki kuma abin kaduwa a gare ni jin cewa kwatsan an kore ni daga NNPP. Na yi imani cewa abin da na faɗa cikin hirar dana yi kwanaki kaɗan da suka gabata, a Turance da Hausa."
"Bai cancanci irin wannan hukunci mai tsauri ba, domin ya yi daidai da ainihin ka’idojin jam’iyyarmu da tafiyarmu wadda ke ba da damar bambancin ra’ayi a bayyane ko a ɓoye.”
“Na yi tsammanin jam’iyya za ta koyi darasi daga wannan hira. Domin sake jaddadawa, ina nan tsayin daka kan dukkan maganganun da na yi a hirarrakin."
“Ba a taɓa gayyata ta don na kare kaina ko na yi bayani ga kowace hukuma ta jam’iyya ba, wanda hakan ya saba wa muhimmin ka’ida ta ba da damar kare kai, bin tsarin doka da adalci wanda NNPP ke taƙama da shi tare da neman hakan daga wasu."

Kara karanta wannan

Bayan katoɓararsa, NNPP ta kori Jibrin Kofa daga jam'iyyar, ta jero wasu dalilai

“Duk da cewa zan fi so na zauna a NNPP na ci gaba da yin hidima ga jama’armu da kasarmu duk da sabani a kan wasu batutuwa (wadanda zan yi cikakken bayani a gaba don kauce wa yaudara ga jama’a), jam’iyya ta riga ta yanke hukunci ta kuma sanar da shi."

"Saboda haka dole na karɓi hukuncin jam’iyya da gaskiya da kuma ba tare da wata kiyayya ba."

- Abdulmumin Jibrin

Abdulmumin Jibrin ya amince da korar da NNPP ta yi masa
Hoton Abdulmumin Jibrin a zauren majalisar wakilai Hoto: Abdulmumin Jibrin
Source: Facebook

Ya yi kira ga magoya bayansa

Ya gode wa jam’iyyar bisa goyon bayan da ya samu a lokacin da yake cikinta, sannan ya bukaci magoya bayansa su biyo shi a sabuwar tafiyar siyasarsa da za a bayyana nan gaba.

"Ina maraba da dukkan magoya bayana da suka shirya su bi ni a sabuwar tafiya. Amma ga waɗanda suka zabi su zauna a NNPP, ban ɗauki kiyayya da su ba, kuma ina sa ran ci gaba da yin kyakkyawar mu’amala da su a matakin ƙananan hukumomi, jiha da kuma ƙasa baki ɗaya.”
"Zan yi nazari a hankali kan dukkan zabin da ke gabana kafin na yanke shawarar jam'iyyar da zan koma. Allah ya taimake ni."

- Abdulmumin Jibrin

NNPP ta yi watsi da korar Abdulmumin Jibrin

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban bangaren jam'iyyar NNPP a jihar Kano, ya yi fatali da batun korar Abdulmumin Jibrin.

Kara karanta wannan

Ta fara tsami tsakanin gwamna da ministan tsaro, APC ta fusata kan lamarin

Sanata Jibrin Doguwa ya bayyana cewa matakin ba sahihi ba ne domin ya sabawa doka.

Shugaban na NNPP ya bayyana cewa hukuncin korar Abdulmumin Jibrin bai inganta ba, domin ba a gina shi kan doka ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng