Tambuwal Ya Fadi Yadda 'Yan Adawa Za Su Iya Kifar da Tinubu a 2027

Tambuwal Ya Fadi Yadda 'Yan Adawa Za Su Iya Kifar da Tinubu a 2027

  • Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya tabo batun kokarin kifar da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027
  • Tambuwal ya bayyana cewa yana cikin kokarin da 'yan adawa suke yi na ganin sun raba Tinubu da mulkin Najeriya
  • Hakazalika, ya bayyana kuskuren da 'yan adawa za su yi wanda zai sanya Tinubu da APC su sake lashe zabe a saukake

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya yi magana kan shirin kifar da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.

Aminu Waziri Tambuwal ya bayyana cewa ya tsunduma gaba ɗaya cikin kokarin da shugabannin adawa ke yi domin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Tambuwal ya ce 'yan adawa za su iya kifar da Tinubu
Hoton Aminu Waziri Tambuwal a zauren majalisa da Shugaba Bola Tinubu yana jawabi a wajen wani taro Hoto: Aminu Waziri Tambuwal
Source: Facebook

2027: Aminu Tambuwal na son kifar da Tinubu

Tsohon gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a a yayin wata hira da aka yi da shi a tashar Channels Tv.

Kara karanta wannan

Wike ko Atiku: Tambuwal ya fadi wanda zai marawa baya don zama shugaban kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina cikin wannan tsari gaba ɗaya bisa dimokuraɗiyya da doka, wanda da ikon Allah, daga karshe zai kai ga kifar da wannan gwamnati daga mulki."
"Tare da taimakon Allah da kuma goyon bayan Najeriya, za mu kori wadannan mutane daga mulki."

- Aminu Waziri Tambuwal

Tambuwal ya kare hadakar 'yan adawa

Sanatan mai wakiltar Sokoto ta Kudu ya yi watsi da maganganun da ke cewa haɗakar jam’iyyar ADC, an yi ta ne don kare muradun Arewa.

"Shin Peter Obi dan Arewacin Najeriya ne? Shin Aregbesola ba dan jihar Osun ba ne? Me kake gaya min? Ba dukkansu suna cikin wannan haɗaka ba?”

- Aminu Waziri Tambuwal

Shin 'yan adawa za su iya kifar da Tinubu?

Ya nace cewa dole sauyin shugabanci ya kasance ta hanyar dimokuraɗiyya da tsarin kundin mulki.

"Ba dole ba ne cewa sai ya yi nasara a 2027. Shirme ne duk kokarin da ake yi na nuna cewa Bola Tinubu ba zai iya faduwa ba."

Kara karanta wannan

Minista ya fadi yadda manufofin Tinubu su ka ceto albashin ma'aikata a jihohi 27

"Za a iya kayar da shi, na yi imani da hakan. Ina aiki tare da shugabannin hadaka domin cimma hakan saboda maslahar kasar nan. Ba adawa da Bola Tinubu nake ba, sai dai yadda yake tafiyar da Najeriya.”

- Aminu Waziri Tambuwal

Tambuwal ya ba 'yan adawa shawara kan Tinubu
Hoton Aminu Waziri Tambuwal yana jawabi Hoto: Aminu Waziri Tambuwal
Source: Facebook

Tambuwal ya ba 'yan adawa shawara

Tsohon gwamnan ya kuma ce Tinubu ba zai kai labari ba idan manyan shugabannin 'yan adawa kamar tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, Atiku Abubakar, Peter Obi, da Rabiu Kwankwaso suka hada kansu.

“Zai fi sauƙi ga 'yan adawa su kafa haɗaka su kayar da Tinubu. Amma idan Tinubu, Jonathan, Atiku, Peter Obi, da Kwankwaso suka tsaya zaɓe a lokaci guda, to hakan zai saukakawa Tinubu samun nasara."
"Idan hakan ta faru, yanayin siyasa zai sauya, kuma abubuwa da dama za su shafi yadda mutane za su kada kuri’a."

- Aminu Waziri Tambuwal

Tambuwal ya sha alwashi kan gwamnatin APC

A baya rahoto ya zo cewa tshon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya ragargaji gwamnatin APC da Shugaba Bola Tinubu.

Aminu Waziri Tambuwal ya zargi Tinubu da jefa 'yan Najeriya cikin mawuyacin hali saboda yadda yake tafiyar da mulkinsa.

Tsohon gwamnan ya sha alwashin cewa za su yi duk mai yiwuwa don ganin aun kifar da gwamnatin APC a zaben 2027.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng