El Rufai Ya Faɗi Abin Mamaki da Zai Faru a 2027, Ya Yi Hasashen na Nawa Tinubu Zai Zo
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya yi hasashen abin da zai faru a zaben shekarar 2027 da ke tafe
- El-Rufai ya ce akwai yiwuwar a tafi zagaye biyu na zaɓen shugaban kasa a 2027 saboda rashin rinjaye daga ɓangare daya
- Tsohon gwamnan ya bayyana cewa Bola Tinubu ba zai shiga zagaye na biyu ba, saboda zai tsaya na uku a cikin masu takarar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya sake ta da kura kan zaben shekarar 2027 da take tunkarowa.
El-Rufai ya bayyana cewa akwai yiwuwar a gudanar da zagaye biyu na zaɓen shugaban kasa a shekarar 2027.

Source: Twitter
El-Rufai ya magantu kan zaben 2027, Tinubu
Tsohon gwamnan ya bayyana haka ne yayin tattaunawa a shirin Sunday Politics na Channels TV a daren yau Alhamis.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
El-Rufai ya ce akwai yiwuwar babu ɗan takara da zai samu rinjaye a karon farko saboda yadda zaben zai yi zafi.
"Abin da zai iya faruwa shi ne a zaben 2027 babu wanda zai yi nasara a zagayen farko.
"Watakila za a iya tafiya zagaye na biyu kuma ba tare da Bola Tinubu za a yi zagaye na biyu ba.
"Tinubu zai zama na uku ne a zaben saboda ba shi da wata dama ta cin zabe duba da tsare-tsaren gwamnatinsa."

Source: Facebook
Shawarar El-Rufai kan hadin kai a 2027
El-Rufai ya tuna cewa a baya ya ce haɗin kan adawa zai mayar da Bola Tinubu gida Lagos a zaɓen shugaban kasa na 2027.
Tsohon gwamnan Kaduna ya kuma ce Najeriya na cikin barazana idan jam’iyyar APC mai mulki ta sake lashe zaɓen shugaban kasa na gaba.
"Ina tunanin idan aka bar gwamnatin Tinubu da APC suka ci gaba da mulki, za su lalata abin da ya rage a kasar.
"Ba dole ne mu tsira da kasarmu ba, wannan yaki ne da ya shafe mu gaba daya."
- Cewar Nasir El-Rufai
Legit Hausa ta tattauna da dan SDP
Suraj Ahmed Kari ya ce wannan magana ta El-Rufai tana kan hanya saboda babu abin da Tinubu ya tabuka a shekaru biyu a mulki.
Ya ce:
"Mu na jira mu ga wanda zai zo tallen Tinubu a 2027 saboda babu wani abin kirki da ya yi da har ya cancanci haka."
Ya bukaci hadin kan jam'iyyun adawa domin tabbatar da samun nasara a zaben 2027 tun da APC ta gaza.
El-Rufai ya zargi Uba Sani da tarwatsa taro
Kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i ya yi zargin cewa gwamnatin Uba Sani ce ta shirya kai hari a taron ƴan adawa.
Furucin tsohon gwamnan ya biyo bayan wani hari da ƴan daba su ka kai wa taron haɗin gwiwa na jam'iyyun adawa a jihar a ranar Asabar.
Da ya ke mayar da magana a fusace, Nasir El-Rufa'i ya sha alwashin kawo ƙarshen gwamnatin APC a Kaduna.
Asali: Legit.ng

