'Dalilin da Ya Sa Bai Kamata Jonathan Ya Fafata da Tinubu ba a 2027'

'Dalilin da Ya Sa Bai Kamata Jonathan Ya Fafata da Tinubu ba a 2027'

  • Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan na ci gaba da samun shawarwari kan yin takara a zaben 2027
  • Kungiyar APCMP ta shawarci Jonathan da ya kada ya tsaya takara da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Ta bayyana cewa masu neman zuga shi ya fito takara, sun san cewa ba zai iya kayar da mai girma Bola Tinubu ba

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Kungiyar All Progressives Congress Media Network (APCMP) ta gargadi Goodluck Jonathan da kada ya tsaya takarar shugaban kasa a 2027 da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ƙungiyar ta bayyana yunkurin yin takara da Tinubu a matsayin babban haɗari, inda ta jaddada cewa shugaban kasan ya fi kowane ɗan siyasa tasiri a yanzu.

Jonathan ya samu shawara kan zaben 2027
Hotunan Goodluck Jonathan da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu Hoto: @GEJonathan, @DOlusegun
Source: Getty Images

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar APCMP, Otuekong Iniobong John, ya fitar a ranar Lahadi, 31 ga watan Agustan 2025, cewar rahoton jaridar The Nation.

Kara karanta wannan

Tsohon dan takarar shugaban kasa ya fadi kuskuren Tinubu kan zuwa Brazil

An ba Jonathan shawara kan takara da Tinubu

Ya bayyana cewa babu wani ɗan siyasa da zai iya kayar da Tinubu a kowanne irin zaɓe, yana mai danganta hakan da nasarorinsa, farin jininsa da kuma kwarewarsa a siyasa.

Ya shawarci Jonathan da kada ya yi watsi da mutuncinsa a matsayin jagoran kasa da kasa, amma ya ba da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali domin ci gaban kasar nan.

"Muna ganin wannan zai zama babban kuskuren siyasa a gare shi. Ba wai kawai zai fuskanci yiwuwar shan kaye a hannun shugaban ƙasa Tinubu ba."
"Zai iya rasa matsayinsa na jagoran kasa da kasa tare da girmamawa da karramawar da ya samu bayan ya amince da shan kayen da ya yi a 2015 kuma ya sauka daga mulki cikin kwanciyar hankali."
"Bisa la’akari da shan kayen da ya yi a matsayin shugaban kasa a 2015, yana da wuya ya iya kayar da wani shugaban ƙasa mai ci, musamman wanda ke da irin karfin siyasa da tasirin da shugaban kasa Tinubu yake da shi."

Kara karanta wannan

2027: APC ta cika baki kan yiwuwar takara tsakanin Jonathan da Shugaba Tinubu

"Muna da tabbacin cewa farin jini da nasarorin shugaban kasa Tinubu za su ci gaba da karuwa, wanda hakan zai zama babban kalubale ga duk wani ɗan hamayya.”

- Otuekong Iniobong

Kungiyar APC ta ja kunnen Jonathan

Ƙungiyar ta kuma gargadi Jonathan da kada ya faɗa tarkon waɗanda ke ƙoƙarin jawo shi cikin siyasa domin ya sake shan sabon shan kaye.

An ba Jonathan shawara kan takara da Tinubu
Hoton Goodluck Jonathan tare da Shugaba Bola Ahmed Tinubu Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter
"A matsayinsa na wanda ya nuna hikima da tawali’u a baya, musamman lokacin da ya amince da shan kaye a 2015, muna shawartar shi da ya fifita zaman lafiya da ci gaban kasa fiye da son zuciya.”

- Otuekong Inibiong

Ƙungiyar ta kuma tambayi manufar waɗanda ke kokarin jawo Jonathan cikin takarar shugaban kasa a 2027.

"Ya kamata a lura cewa waɗanda ke kulla makircin jawo Goodluck Jonathan cikin zaɓen shugaban ƙasa na 2027 sun san da kyau cewa ba zai iya kayar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba."

- Otuekong Inibiong

Keyamo ya ja hankalin PDP kan Jonathan

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya gargadi PDP kan tsayar da Goodluck Jonathan takara a zaben 2027.

Kara karanta wannan

Reno Omokri: Tinubu ya kawo tsaro a Abuja zuwa Kaduna da ke fama da 'yan ta'adda

Festus Keyamo ya bayyana cewa PDP za ta iya rasa dan takara a zaben 2027 idan ta ba Jonathan tikitinta.

Ministan ya bayyana cewa PDP na son ba Jonathan takara a zaben 2027 don gyara kuskuren da ta yi a 2023.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng