Zaben 2027: Keyamo Ya Hango Abin da Zai Faru idan Peter Obi Ya Koma PDP
- Jigon jam’iyyar APC, Festus Keyamo, ya bayyana cewa mambobin da suka fi tsayawa kan gaskiya a cikin Obidient Movement za su yi adawa da Peter Obi idan ya koma PDP
- A cewar Keyamo, mambobin Obidient za su ɗauki irin wannan mataki a matsayin cin amana ga akidu da burin miliyoyin ’yan Najeriya da ke goyon bayan Peter Obi
- Keyamo ya tunatar da cewa Obi ya taɓa kiran manyan jam’iyyu biyu da suka yi mulkin Najeriya tun daga 1999, wato APC da PDP, a matsayin "jam'iyyun aikata laifuffuka"
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya yi magana kan yunkurin PDP na dawo da Peter Obi zuwa cikinta.
Festus Keyamo ya ce idan PDP ta yi kokarin dawo da Peter Obi, jam’iyyar na iya rashin nasara a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan
Ministan Tinubu ya hango hadarin da PDP za ta shiga idan ta tsayar da Jonathan takara a 2027

Source: Twitter
Ministan ya bayyana hakan ne a cikin wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Lahadi, 31 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP na duba yiwuwar jawo Peter Obi
A kwanakin baya, Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi, kuma shugaban kungiyar gwamnonin PDP, ya bayyana cewa jam’iyyar na la’akarin tsayar da Peter Obi, takara.
Ya ce suna la'akarin janyo shi cikin jam'iyyar don yin takarar shugaban kasa a zaben 2027.
Wannan furuci na gwamnan ya zo ne ’yan kwanaki bayan PDP ta bayyana cewa za ta kai tikitin takarar shugaban kasa zuwa ga yankin Kudu a zaben 2027.
Peter Obi dai ya kasance ɗan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP a 2022, amma daga baya ya fice daga jam’iyyar kafin babban zaɓen fidda gwani, inda ya ce akwai abubuwa a cikin jam’iyyar da ba su dace da akidunsa da halayyarsa ba.
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya koma jam’iyyar LP, inda daga bisani ya zama ɗan takarar ta na shugaban kasa a zaɓen 2023.
Keyamo ya yi nazari kan matsayar PDP
Yayin da yake tsokaci kan tsarin rabon takara da PDP ta yi, Keyamo, ya bayyana cewa idan jam’iyyar adawa ta tsayar da dan takara mai jan hankali daga wani yanki na Kudu, sauran yankunan kasar nan ba za su zabe shi ba.
Keyamo ya kara da cewa duk wani ɗan takara mai neman lashe zaɓen shugaban kasa a Najeriya yana buƙatar samun rinjaye daga akalla yankuna uku ko huɗu na kasar nan.

Source: Facebook
Ya yi gargaɗin cewa Peter Obi zai iya rasa goyon bayan magoya bayansa na gaskiya, da aka fi sani da Obidients, idan ya yanke shawarar komawa PDP.
"Mambobin da suka fi tsayawa kan akida daga cikin Obidients za su ɗauki Obi a matsayin mai komawa ga abin da ya taɓa ki, don haka ba za su ci gaba nuna masa goyon baya ba kamar baya."
- Festus Keyamo
Keyamo ya hango matsala ga PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan sufuri, Festus Keyamo, ya ce Goodluck Jonathan na iya zama matsala ga PDP a zaben 2027.
Keyamo ya bayyana cewa jam'iyyar na iya tashi babu dan takara idan ta ba Jonathan tikitinta a zaben 2027.
Ministan ya nuna cewa akwai wani gyaran da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar nan, wanda zai iya hana Jonathan yin takara.
Asali: Legit.ng

