Ministan Tinubu Ya Hango Hadarin da PDP Za Ta Shiga idan Ta Tsayar da Jonathan Takara
- Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya tsoma baki kan siyasar jam'iyyar adawa ta PDP
- Festus Keyamo ya nuna cewa PDP na iya samun kanta cikin matsala idan ta tsayar da Goodluck Jonathan takara 2027
- Ministan ya bayyana cewa PDP na iya rasa dan takarar shugaban kasa a zaben 2027, idan har ba ta yi taka tsan-tsan ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo, ya yi tsokaci kan yiwuwar Goodluck Jonathan ya yi takarar shugaban kasa karkashin inuwar PDP a zaben 2027.
Festus Keyamo ya bayyana cewa PDP za ta iya samun kanta cikin tsaka mai wuya idan Jonathan ya zama dan takararta a 2027.

Source: Twitter
Ministan ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X a ranar Lahadi, 31 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Keyamo ya ce PDP ta yi kuskure a 2023
Festus Keyamo ya ce jam’iyyar PDP ta aikata babban “laifi” a zaɓen 2023, saboda ta kasa kai tikitin takarar shugaban kasa zuwa yankin Kudu.
Minsitan ya bayyana cewa tsarin rabon mulki bisa yanki ya zama wani babban lamari a siyasar kasar nan, kuma ba zai kare ba.
Yayin da yake magana kan shawarar PDP ta kai tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudu a 2027, ministan ya ce idan ba wani abun al'ajabi ne ya faru ba, jam’iyyar adawar na iya jira har zuwa shekarar 2031 kafin ta sake komawa kan mulki.
Batun takarar Jonathan a 2027
Festus Keyamo ya kuma bayyana ra’ayinsa game da tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, wanda ake ta rade-radin cewa zai iya zama ɗan takarar PDP a zaɓen 2027.
“Ɗaya daga cikin zababbun mutanen da PDP ke sa ran tsayarwa shi ne tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, saboda ana ganin yana da ikon yin wa’adi guda ɗaya kacal."
"Amma idan aka tsayar da shi, jam’iyyar za ta iya shiga haɗarin rasa ɗan takara gaba ɗaya bisa ga tanadin sashe na 137 (3) na kundin tsarin mulki na 1999 (gyara na huɗu)."
"Wannan gyaran kundin tsarin mulki an yi shi ne bayan hukuncin kotu da ya ba shi damar tsayawa takara a 2015. Saboda haka, har yanzu ba a yanke hukunci kan wannan sabon gyaran ba, shi ya sa na yi amfani da kalmar ‘haɗari’."
"Duk muhawarar kan ko wannan sashe na iya shafar shi ba za a yanke a dandalin sada zumunta ba, sai dai a Kotun Koli."
"Idan aka hana shi tsayawa bayan rufe wa’adin ɗora sunayen ’yan takara, kuma PDP ta bayyana a matsayin jam’iyyar da ba ta da ɗan takara."
"To kada wani ya fara ihu da cewa ‘bangaren shari'a ya gurbace’, domin jam’iyya babba irin wannan ta riga ta ga hadarin abin da zai iya faruwa ta fannin doka, amma ta yi watsi da shi da gangan."
- Festus Keyamo

Source: Facebook
ADC ta fara zawarcin Jonathan
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta fara zawarcin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.
Wata kungiya a ADC ta mika tayinta ga Jonathan kan ya shigo jam'iyyar domin a tsayar da shi dan takarar shugaban kasa a 2027.
Majiyoyi sun bayyana cewa tuni aka sanar da tsohon shugaban kasan tanadin da aka yi masa a ADC.
Asali: Legit.ng


