2027: ADC Ta Shiga Sahun Masu Zawarcin Jonathan don Yin Takara

2027: ADC Ta Shiga Sahun Masu Zawarcin Jonathan don Yin Takara

  • Ana ta maganganu kan yiwuwar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, zai fito takara a zaben shekarar 2027
  • Wata majiya a jam'iyyar ADC ta yi magana kan shirin da suke yi dnagane da tsohon shugaban kasan
  • Majiyar ta nuna cewa idan tsohon shugaban kasan ya karbi tayinsu, za su yi aiki da shi domin neman madafun ikon kasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Sunan tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya fito a cikin wadanda jam'iyyar ADC ke zawarci don yin takara a zaben 2027.

Wata kungiya mai karfi a cikin jam’iyyar ADC tana kokarin jawo Goodluck Jonathan don ya tsaya takarar shugaban kasa a zaɓen 2027.

ADC na zawarcin Goodluck Jonathan
Hoton tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Facebook

Wata majiya mai kusanci da tsohon shugaban kasan da kuma jam’iyyar ADC ta shaida wa jaridar Tribune hakan a ranar Juma’a, 29 ga watan Agustan 2027.

Kara karanta wannan

2027: APC ta cika baki kan yiwuwar takara tsakanin Jonathan da Shugaba Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jonathan na duba yiwuwar yin takara a 2027

Majiyar ta ce tsohon shugaban kasan yana cikin nazari sosai kan yiwuwar tsayawa takara a babban zaɓen shugaban kasa mai zuwa.

Majiyar ta tabbatar da cewa fitattun jiga-jigan ADC za su yi farin cikin samun Jonathan a matsayin ɗan takararsu na shugaban kasa, kuma har ma sun riga sun tuntube shi a hukumance.

Sai dai majiyar ta ce tsohon shugaban kasan yana cikin ruɗani tsakanin biyayya ga jam’iyyar PDP “wadda ta haife shi a siyasa” da kuma ADC, wadda ya ce tana da damar lashe zaɓen idan ta samu sahihin ɗan takara.

"Tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan yana cikin damuwa saboda wasu mutane da suke da alaƙa sosai da fadar Aso Rock Villa har yanzu suna da tasiri a cikin PDP, kuma akwai yiwuwar su lalata masa shiri idan ya nemi tikitin jam’iyyar."

- Wata majiya

Wace matsala Jonathan yake gudu a ADC?

Kara karanta wannan

Jonathan ya hakura da neman takarar shugaban kasa a 2027? An samu bayanai

Majiyar ta kara da cewa matsalar Jonathan kawai da ADC ita ce ba ya son yin takara da Peter Obi domin yana ganin mutanen Igbo sun nuna goyon baya a gare shi a 2015 fiye da mutanen kabilarsa ta Ijaw.

Ana zawarcin Jonathan don takara a 2027
Hoton tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Facebook

Majiyar ta jaddada cewa babu shakka Jonathan zai tsaya takara sai dai idan bai samu wata jam’iyya mai karɓarsa ba.

"Idan ya zaɓi jam’iyyarmu (ADC), za mu kai tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudu. Idan kuma bai zo wurinmu ba, ba mu da wani zaɓi illa mu nufi Arewa saboda siyasa tana kan lissafi da kuma nasara."

- Wata majiya

APC ta cika baki kan Goodluck Jonathan

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC reshen jihar Levas, ta tabo batun yiwuwar yin takara tsakanin Goodluck Jonathan da Shugaba Bola Tinubu a zaben shugaban kasa na 2027.

APC ta bayyana cewa Jonathan ba zai iya kayar da Shugaba Tinubu ba, idan suka fafata a zaben 2027.

Jam'iyyar ta yi shagube ga Jonathan, inda ta nuna cewa tsohon shugaban kasan bai ma san jam'iyyar da zai shiga ba har yanzu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng