Tajudeen Abbas na Fuskantar Matsala, Rigima na Neman Barkewa a Majalisa kan Abubuwa 2

Tajudeen Abbas na Fuskantar Matsala, Rigima na Neman Barkewa a Majalisa kan Abubuwa 2

  • Wasu 'yan Majalisar wakilai sun nuna bacin raansu kan ma'aikatan da aka dauka aiki kwanan nan da kuma ayyukan mazabu
  • Rahotanni sun nuna sun shirya tunkarar kakakin Majalisa, Rt. Hon. Tajudeen Abbas idan aka dawo hutu ranar 23 ga watan Satumba 2025
  • A cewarsu, shugabannin Majalisar na yin abubuwa da dama ba tare da tuntubarsu ba, sannan babu wasu ayyuka a mazabunsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Rahotanni sun nuna cewa wasu yan Majalisa na shirin tayar da rikici a Majalisar Wakilai da zarar sun dawo hutun shekara a watan Satumba, 2025.

Fusatattun yan Majalisar na shirin nuna adawa da kakakin Majalisar, Rt. Hon. Tajudeen Abbas kan daukar ma'aikata da kuma yanayin aikin mazabu.

Rt. Hon. Tajudeen Abbas.
Hoton kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas Hoto: @HouseNGR
Source: Twitter

Wasu daga cikin ‘yan majalisar da suka nuna bacin rai sun fara tattara abin da suka kira “laifuffukan” Kakakin Majalisa, kamar yadda Leadership ta kawo.

Kara karanta wannan

Hatsari ya rutsa da ayarin mataimakin kakakin Majalisa, an rasa rayukan 'yan uwa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan Majalisa sun fara zargin Tajudeen Abbas

Suna zargin cewa Abbas da wasu shugabanni sun tauye musu hakki wajen rabon wasu gurabe da alfarma a matsayinsu na yan Majalisa.

A halin yanzu, ‘yan majalisar suna cikin hutun shekara-shekara, wanda ya hada Majalisar Dattawa da ta Wakilai.

An dakatar da zaman majalisa ne a ranar 23 ga Yuli, inda Abbas ya shawarci ‘yan majalisa su yi amfani da hutun wajen aikin mazabu, kula da al’amuran yankunansu, da kuma duba ayyukan gwamnatin tarayya a wuraren da suka fito.

Sai dai bincike ya gano cewa wasu daga cikin ‘yan majalisar na amfani da hutun wajen hada kai da kafa kungiyoyin domin tattauna matsalolin da suka shafe su da walwalarsu.

Wane abubuwa suka fusata yan Majalisa?

Abin da ya kara fusata gungun yan majalisar shi ne kaddamar da sababbin ma'aikatan Majalisa 785 da aka dauka, wanda magatakarda ya yi kwanan nan.

Kara karanta wannan

Ana fargabar zanga zanga kan cire sarkin da ya yi abin kunya a Amurka

Wannan lamari ya sa wasu daga cikin ‘yan majalisar suka nuna bacin ransu a dandalin WhatsApp na Majalisar Wakilai, suna tambayar dalilin da yasa aka dauki ma'aikatan ba tare da tuntuɓarsu ba.

Wasu daga cikinsu sun zargi Kakakin Majalisa, Tajudeen Abbas da take hakkinsu saboda biyayyar da suke masa, suka ce sun yanke shawarar tunkararsa idan majalisa ta koma aiki a ranar 23 ga Satumba.

Haka kuma, sun bayyana damuwarsu kan rashin manyan ayyuka a mazabunsu, wanda suka ce zai iya hana su samun damar tazarce a 2027.

Majalisar Wakilan Taraya.
Hoton zauren Majalisar Wakilai ana tsakiyar zama a Abuja Hoto: @HouseNGR
Source: Facebook

Yadda yan Majalisa suka nuna bacin ransu

Wani daga cikinsu ya rubuta cewa:

"Abubuwan mamaki a majalisa ba za su kare ba. Ya za a dauki ma’aikata sama da 800 ba tare da ‘yan majalisa sun sani ba, balle su ba da sunaye daga mazabunsu?”

Sai wani ya amsa cikin zolaya:

“Wanene ya ce maka shugabannni ba su sani ba? Ai mutanensu su na cikin wadanda aka dauka.”

Wani kuma ya kara da cewa:

“Mun rasa hakkokinmu saboda biyayya. Akwai abubuwa da dama da ake yi a NASS ba tare da an kula da muradun ‘yan majalisa ba.

Kara karanta wannan

Ba dadi: 'Yan bindiga sun kashe mafarauta yayin artabu a Neja

Majalisa na tunanin hada zabe rana daya a 2027

A wani labarin, kum ji cewa Majalisar Wakilai ta fara duba kudirin sauya dokar zaɓe domin gudanar da dukkan zaɓuka a rana guda daga shekarar 2027.

Kudirin da Shugaban Kwamitin Majalisa kan Harkokin Zaɓe, Bayo Balogun ya gabatar ya bukaci sauya tsarin zabe a Najeriya.

Kudirin dokar ya tanadi biyan kuɗin rajista har Naira miliyan 50 ga kowace ƙungiyar siyasa da ke neman rijista da INEC a matsayin jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262