'Tinubu Ya Yi Amfani da Mu, Ya Cimma Burinsa': Tsohon Sanatan Zamfara Ya Bar APC
- APC ta yi rashin daya daga cikin jiga-jiganta a jihar Zamfara inda jam'iyyar ke da karfi duk da PDP ce a kan mulki
- An tabbatar da Sanata Kabiru Garba Marafa ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar APC, yana zargin Bola Tinubu
- Marafa ya ce duk da ya tabbatar da nasarar Tinubu a Zamfara, gwamnatin tarayya ta nuna halin ko in kula ga jama’ar jihar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gusau, Zamfara - Jam'iyyar APC mai adawa a jihar Zamfara ta yi rashin tsohon Sanata bayan ficewarsa daga jam'iyyar.
Tsohon Sanata na Zamfara ta Tsakiya ya Kabiru Garba Marafa, wanda ya shugabanci kamfen ɗin Tinubu/Shettima a 2023, ya sanar da ficewarsa daga APC.

Source: Facebook
Shawarar ta biyo bayan taron kwana biyu na Majalisar Tattaunawa ta Sanata Marafa, wanda ya haɗa magoya baya daga kananan hukumomi 14, cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Marafa, wanda ya wakilci Zamfara ta Tsakiya daga 2011 zuwa 2019, ya ce ya yanke shawarar hakan ne saboda salon shugabancin Tinubu na yin amfani da mutum a yar da shi.
Gudunmawar da Sanata Marafa ya ba Tinubu
Taron da aka gudanar a Kaduna a ranar 27 da 28 ga Agusta 2025, ya tattauna kan tsaro, siyasa da cigaba a Zamfara.
A ƙarshe, taron ya fitar da sanarwa da shugaba, Bashir Muhammad Mafara, da sakatare Dr. Mannir Bature Tsafe, da wasu mambobi suka sa hannu.
Sanarwar ta tuna cewa a ƙarƙashin jagorancin Sanata Marafa, Tinubu ya lashe zaɓen 2023 a Zamfara, inda Marafa ya tabbatar da ba sai Tinubu ya zo jihar ba.
Duk da irin wannan goyon baya, kungiyar ta nuna damuwa cewa gwamnatin Tinubu ta nuna halin ko in kula ga jihar Zamfara tun bayan nasararsa.
Sanarwar ta nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a Zamfara, inda rahotanni suka ce jihar ta fi kowacce a satar mutane a 2024.
Daga cikin mutane 4,722 da aka yi garkuwa da su a Najeriya, mutum 1,203 sun fito daga Zamfara, sannan an kai hare-hare a ƙauyuka 25 a mako guda.

Source: Twitter
Zargin da Sanata Marafa ya yi ga Tinubu
Kungiyar ta zargi gwamnati da amfani da jami’an tsaro wajen tabbatar da nasarar APC a zaɓen raba gardama, amma ta kasa kare rayuka daga ‘yan bindiga.
Duk da cewa Zamfara ta taimaka wajen nasarar Tinubu, jihar ta samu kujerar Ministan jiha daya kaɗai, yayin da sauran jihohi suka samu mukamai biyu.
Kungiyar ta ce ba kamar sauran jihohin da ake fama da tsaro ba, Tinubu bai ziyarci Zamfara ba kuma bai tura tallafin kudi ga jama’a ba.
Ya kuma zargi shugabancin jam’iyyar da kawar da tsari na siyasar Marafa, akasin ƙa’idojin APC na adalci, da haɗin kai, TheCable ta ruwaito wannan.
Kungiyar ta ce nan gaba za ta sanar da sabuwar tafiyar siyasa, bisa la’akari da muradun jama’ar Zamfara gaba ɗaya.
Mambobin APC 5,000 sun bar jam'iyyar a Sokoto
Mun ba ku labarin cewa magoya bayan jam'iyya mai mulki ta APC a karamar hukumar Gada, a jihar Sokoto sun sauya sheka zuwa ADC.
Wadanda suka sauya shekar sun ce sun bar APC saboda gazawar gwamnati wajen magance matsalar tsaro da tattalin arziki.
An tabbatar da cewa fiye da mutum 50,000 suka shiga ADC, yayin da Sanata Abubakar Gada ya ce jam'iyyar hadaka za ta ceto Najeriya.
Asali: Legit.ng


