PDP: Gwamna Bala Ya Bayyana Yiwuwar Takarar Shugaban Ƙasa tare da Seyi Makinde

PDP: Gwamna Bala Ya Bayyana Yiwuwar Takarar Shugaban Ƙasa tare da Seyi Makinde

  • Gwamna Bala Mohammed na Bauchi ya ce shi da Gwamna Seyi Makinde na Oyo za su iya tsaya wa takarar Shugaban kasa a 2027
  • Ya bayyana cewa PDP ba za ta yi kuskuren bai wa Musulmi Musulmi daga Arewa don gujewa rikicin tikitin Musulmi–Musulmi
  • Bala ya jaddada cewa PDP ba za ta maimaita abin da APC ta yi a 2023 ba, domin za ta yi la’akari da tsarin raba iko da daidaiton addini

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Bauchi – Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce shi da takwaransa na Oyo, Seyi Makinde, za su dace da tsayawa takarar Shugaban Kasa da Mataimaki a zaben 2027.

Yana wannan batu ne bayan ya tabbatar da cewa PDP ta mika neman takarar Shugaban Kasa ga Kudancin kasar nan saboda kishi, ba son zuciya ba.

Kara karanta wannan

Gwamna ya jero mutum 2 da PDP ke tunanin tsaida wa takarar shugaban kasa a 2027

Gwamnan Bauchi ya magantu kan takarar Shugaban Kasa
Hoton gwamnan Bauchi, Bala Muhammad Hoto: Senator Bala AbdulKadir Mohammed
Source: Facebook

A hirarsa a wani shirin siyasa a tashar Channels TV a ranar Alhamis, Gwamnan ya musanta rade-radin cewa an riga an ayyana shi a matsayin mataimakin Makinde.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kalaman gwamna Bala kan zaben 2027

Jaridar Punch ta wallafa cewa Gwamna Bala Mohammed ya ce ya wajaba PDP ta tsayar da ɗan takara Kirista daga Kudu tare da Musulmi daga Arewa.

Ya ce wannan zai samar da bambancin tare da kaucewa sabanin da tikitin Musulmi–Musulmi ya haifar a baya.

Ana ganin babu laifi Makinde ya yi wa PDP takara
Hoton gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde Hoto: Seyi Makinde
Source: Facebook

Bala Mohammed ya bayyana cewa:

“Tikitin Seyi Makinde–Bala Mohammed ma zai iya yin tasiri sosai. Abin da ’yan Najeriya suke buƙata shi ne ƙwarewa da gogewa, kuma mun nuna hakan a matakin gwamnatocin jihohi. Amma ba mu kaɗai ba ne, akwai zaɓuɓɓuka masu inganci a PDP. Muhimmin abu shi ne jam’iyyar ta kasance a buɗe ga kowa.”

Ya ƙara da cewa PDP ba za ta kuskura ta sake maimaita abin da ya kira “kurakuran APC” na 2023 ba, inda aka samu cece-kuce kan tikitin Musulmi–Musulmi.

Kara karanta wannan

'Mun dauki darasi,' Gwamna ya fadi babban abin da ya jawo PDP ta fadi zaben 2023

A cewar gwamnan, tsarin karba karba da daidaita addini dole ne su zama ginshiƙan zaɓin ’yan takara a 2027.

Wannan na zuwa ne a yayin da PDP ta bayyana cewa tana shiri domin ta tunkari zaben 2027 da karfinta, da niyyar fitar da APC daga ofis duk da kalubalen da ya dabaibaye ta na sauta sheka.

Gwamnan Bauchi ya magantu kan takarar PDP

A baya, mun wallafa cewa gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ta fara laluben wanda ya dace ta tsaida a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa.

A cewarsa, bayan kammala tattaunawa kan yankin da za a samo ɗan takara, jam’iyyar ta fara nazari kan manyan ’yan siyasa biyu daga Kudu waɗanda za su iya ɗaukar nauyin takarar.

Gwamna Bala ya bayyana cewa mutanen biyu da PDP ke duba wa su ne tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan, da kuma tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng