PDP Ta Koka, Ta Zargi EFCC Ta Garkame Manyan 'Ya 'yanta 2 a Kaduna

PDP Ta Koka, Ta Zargi EFCC Ta Garkame Manyan 'Ya 'yanta 2 a Kaduna

  • PDP ta koka kan tsare 'yar takararta na zaɓen cike gurbin kujerar Chikun/Kajuru a majalisar wakilai, Princess Esther Ashivelli Dawaki
  • Ta ce an tsare ta da karin mutum daya, wanda ke nuna yunƙurin hana adawa tasiri a yayin zaben cike gurbin da ya gabata a wasu mazabu
  • Jam’iyyar ta yi gargaɗin cewa za ta iya fito wa da magoya bayanta domin su gudanar da zanga zangar lumana matukar ba a sake su ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar KadunaJam’iyyar adawa ta PDP reshen jihar Kaduna ta bayyana damuwa kan tsare 'yar takararta na zaɓen cike gurbin kujerar Chikun/Kajuru a majalisar wakilai, Princess Esther Ashivelli Dawaki.

Haka zalika, jam’iyyar ta ce daraktan yaƙin neman zaɓenta, Alhaji Shehu Fatangi, ma na tsare a hannun hukumar yaki da cin hanci da rashawa (EFCC).

Kara karanta wannan

ASUU: Malaman jami'a sun fara yi wa gwamnatin Tinubu zanga zanga a fadin Najeriya

Ambasada Umar Iliya Damagum
Shugaban PDP na kasa, Ambasada Umar Iliya Damagum Hoto: Umar Iliya Damagum
Source: Twitter

Jaridar Vanguard ta rawaito cewa Shugaban PDP na jihar, Sir Edward Percy Masha ne ya bayyana hakan a yayin zantawarsa da manema labarai a Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana lamarin a matsayin abin damuwa, inda ya ce hakan na nuni da yunƙurin toshe muryar adawa kafin zaɓen cike gurbi da aka gudanar a ranar 16 ga watan Agusta.

Jam'iyyar PDP ta koka da hukumar EFCC

Daily Post ta wallafa cewa jam’iyyar ta ce EFCC ta gayyaci ‘yar takararta, Princess Esther a ranar Litinin 25 ga watan Agusta, kuma tun daga lokacin tana tsare a hannun hukumar.

PDP ta kuma ce daraktan kamfenta, Alhaji Shehu Fatangi, ya shafe kwanaki 12 a tsare duk da cewar ya cika sharuddan beli.

PDP ta mika kokenta ga Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede
Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

Sir Edward ya bayyana cewa:

“Muna ganin wannan lamari abin takaici ne ƙwarai. Ya sanya tambayoyi kan yadda ake samun damar fafatawa cikin gaskiya a dimokuraɗiyya. Bukatarmu a bayyane take: a saki ‘yar takararmu da kuma daraktan kamfen ɗinmu nan take.”

Kara karanta wannan

APC ta dakatar da babban jami'in gwamnati saboda aikata zunubai masu girma

PDP ta zargi EFCC da jawo matsa matsala

Jam'iyyar PDP ta kuma zargi jami’an tsaro da kawo cikas ga ayyukan kamfen ɗinta a lokacin zaɓen, inda aka takaita wasu daga cikin shirye-shiryenta.

Shugaban jam’iyyar ya yi gargaɗi cewa idan aka ci gaba da tsare 'ya'yan jam’iyyar ba tare da waani dalilu mai karfi ba, PDP na iya ɗaukar matakin fito da magoya bayanta domin yin zanga-zangar lumana.

Jam’iyyar ta yi kira ga shugaban EFCC, Mista Olanipekun Olukoyede, da ya sa baki domin dakile rikicin da ka iya tasowa.

Ya jaddada cewa PDP a Kaduna za ta ci gaba da kare muradun dimokuraɗiyya tare da tabbatar da cewa ba a zalunta ko firgita 'ya'yanta ba.

PDP ta dauki mataki kan kujerar shugabanta

A baya, mun wallafa cewa babbar jam'iyyar hamayya ta PDP a Najeriya ta tabbatar da Umar Iliya Damagum a hukumance a matsayin shugaban jam’iyyar na ƙasa.

Damagum, wanda ya shafe sama da shekara guda yana rike da mukamin shugaban rikon kwarya na jam'iyyar, yanzu ya zama shugaban PDP na kasa mai cikakken iko.

PDP ta ce ɗaukar wannan mataki zai taimaka wajen daidaita shugabanci a cikin jam’iyyar da kuma ba ta ƙarfi yayin da take shirin fuskantar manyan zaɓe a gaba don kara wa da APC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng