Umar Damagum: PDP Ta Dauki Mataki kan Kujerar Shugabanta na Kasa
- Jam'iyyar PDP ta daga darajar Umar Iliya Damagum daga kan mukamin mukaddashin shugabanta na kasa
- A yayin taron kwamitin NEC na PDP, jam'iyyar ta tabbatar da Damagum a matsayin shugabanta na kasa
- Hakazalika, PDP ta kai tikitin takarar shugaban kasa na zaben 2027 zuwa yankin Kudancin Najeriya
Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP mai adawa a Naneriya ta karawa mukaddashin shugabanta na kasa, Umar Iliya Damagum, girma.
Jam'iyyar PDP ta tabbatar da Umar Damagum a hukumance a matsayin shugabanta na kasa.

Source: Twitter
Jaridar The Punch ta rahoto cewa jam'iyyar ta amince da hakan ne taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC) karo na 102 da aka gudanar a ranar Litinin, 25 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Damagum ya zama shugaban PDP na kasa
PDP ta yanke shawarar cewa Damagum, wanda ya shafe sama da shekara guda yana rike da mukamin shugaban rikon kwarya, a ɗaga shi zuwa cikakken shugaban jam’iyyar na kasa.
Zai rike mukamin ne zuwa babban taron zaben shugabanni na kasa da aka tsara gudanarwa a Ibadan, jihar Oyo, a ranar 15 da 16 ga watan Nuwamban 2025.
Mai ba da shawara kan harkokin shari’a na jam’iyyar PDP, Kamaldeen Ajibade, shi ne ya rantsar da shi a matsayin sabon shugaban jam’iyyar na kasa.
An naɗa Damagum a matsayin shugaban rikon kwarya na kasa a watan Maris 2023 bayan dakatar da Iyorchia Ayu.
Kafin wannan naɗi, Damagum shi ne mataimakin shugaban na jam’iyyar PDP na kasa (yankin Arewa).
PDP ta kai tikitin takarar shugaban kasa Kudu
Hakazalika kwamitin NEC na PDP ya kai tikitin takarar shugaban kasa na zaɓen 2027 zuwa yankin Kudancin Najeriya.
Sakataren yada labarai na PDP na kasa, Debo Olugunagba, ya bayyana hakan a cikin sanarwar bayan taron NEC da ya fitar, cewar rahoton jaridar The Cable.
Ya bayyana cewa tsarin rabon kujerun NWC da ake da shi a halin yanzu, zai ci gaba da kasancewa yadda yake har zuwa babban taron kasa na jam'iyyar, inda za a zabi sababbin shugabanni.

Source: Facebook
"Dukkan mukaman jam’iyyar PDP na kasa da ke yankin Arewacin kasar nan za su ci gaba da kasancewa a Arewa."
“Haka kuma dukkan mukaman jam’iyyar PDP na kasa da ke yankin Kudancin kasar nan za su ci gaba da kasancewa a Kudu."
"Tun da aka ci gaba da rike matsayin shugaban jam’iyya na kasa a Arewa, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar a babban zaɓen 2027 zai fito daga yankin Kudu."
Debo Olugunagba
Tsohon sanatan PDP ya fice daga jam'iyyar
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan da ke wakiltar Kebbi ta Arewa, Isa Galaudu, ya raba gari da jam'iyyar PDP.
Isa Galaudu ya sanar da cewa ya yi murabus daga jam'iyyar PDP bisa wasu dalilai da suka tilasta masa yin hakan.
Ya bayyana cewa jam'iyyar PDP ta kama hanyar rugujewa domin wasu 'yan siyasar jam'iyya mai mulki ne suke juya ta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

