Atiku Ya Kawo Karshen Jita Jita kan Batun Yin Takara a Zaben 2027
- Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya bayyana matsayarsa kan yin takara a zaben shekarar 2027
- Atiku ya bayyana cewa zai sake jaraba sa'arsa wajen neman shugabancin Najeriya a zaben 2027 da ake tunkara
- Hakazalika ya bayyana cewa maganar janyewa daga takara da aka ce yana yi, ba daga gare shi ta fito ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Atiku Abubakar ya yi martani kan rahotannin da ke cewa zai iya janyewa daga takarar shugabancin kasa a 2027.
Atiku Abubakar ya bayyana cewa zai yi takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.

Source: Facebook
Mai ba da shawara kan harkokin yada labarai ga Atiku Abubakar a zaben 2023, Tunde Olusunle ne ya bayyana hakan, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An ari bakin Atiku an ci masa albasa
An dai ruwaito Atiku a karshen mako yana cewa, jajircewarsa wajen ganin an gina Najeriya mafi kyau ta fi burin da yake da shi na zama shugaban kasa.
Farfesa Ola Olateju na jami’ar Achievers University, Owo, jihar Ondo, wanda ya wakilci Atiku a wajen shigowar wasu jiga-jigan siyasa a Legas zuwa jam'iyyar ADC a karshen mako, ne ya bayyana hakan.
Ya yi nuni da cewa Atiku ba wai yana da kishin shiga fadar Aso Rock ta kowane hali ba ne.
Sai dai, a wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da Farfesa Tunde Olusunle, Atiku ya sake jaddada cewa yana nan daram a kan tafarkin siyasar da zai kai shi zuwa shugabancin kasa, rahoton The Cable ya tabbatar.
Olusunle ya ce bayan karanta rahoton a gidansa na hutu a Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE), tsohon mataimakin shugaban kasan ya bayyana cewa wannan magana da ake cewa zai iya janyewa daga takara ba daga gare shi ta fito ba.
Matsayar Atiku kan takara a 2027
"Ni ban fitar da wannan sanarwa ba, idan mutane suka wakilce ni a wuraren taro, muna tattauna tunanina kan batun kafin lokacin, da abin da zan bayar na gudunmawa, domin mu yi daidaito."
"Amma a wannan yanayin, babu irin wannan tattaunawa da aka yi da ni; Farfesa Olateju ba ya magana a madadina.”

Kara karanta wannan
Jerin sunaye: Mutane 17 yan gidan sarauta sun fara neman karagar Sarki bayan ya rasu
"Zan tsaya takara a 2027. Najeriya tana bukatar a kuɓutar da ita da gaggawa daga ‘dakin jinya’ da aka mayar da ita; lalacewar kasar nan, yawaitar talauci da wahala, bakin ciki da azaba, ba abin yarda ba ne."
"Yaɗuwar rashin gaskiya, sata ba tare da tsoro ba, da kuma rashin gaskiya, duk abubuwa ne da ya kamata su tayar da hankali ga kowanne ɗan kasa mai kishin kasa."
"Zan ba da kaina domin jagorantar ceto da gina wannan kasa da ta shiga cikin hali na ban tausayi.”
- Atiku Abubakar

Source: Facebook
Jigon PDP ya fadi kuskuren Atiku a 2023
A wani labarin kuma, kun ji cewa wano jigo a jam'iyyar PDP, Diran Odeyemi, ya bayyana cewa Atiku ya yi kuskure a zaben 2023.
Diran Odeyemi ya bayyana cewa da Atiku bai yi wannan kuskuren ba, da ya zama shugaban kasan Najeriya.
Jigon na PDP ya bayyana cewa kuskuren da Atiku ya yi shi ne, rashin daukar Peter Obi a matsayin wanda zai yi masa mataimaki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
