"An Yaudari 'Yan Najeriya": Kungiya Ta Kinkimo Aiki kan Takarar Jonathan a 2027

"An Yaudari 'Yan Najeriya": Kungiya Ta Kinkimo Aiki kan Takarar Jonathan a 2027

  • Batun kiraye-kiraye ga tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, don tsayawa takara a zaben shekarar 2027 na kara girmama
  • Wata kungiyar magoya bayansa ta mika kokon bararta a gare shi kan ya tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027 da ake tunkara
  • Kungiyar ta bayyana cewa a lokacin mulkin Jonathan, rayuwa akwai sauki ba kamar yanzu ba da aka jefa 'yan Najeriya cikin yunwa

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Wata ƙungiya mai goyon bayan Goodluck Jonathan mai suna Bring Back Our Goodluck, ta bukaci da ya dawo cikin siyasa.

Kungiyar ta bukaci Jonathan da ya dawo siyasa tare da tsayawa takarar shugaban kasa a zaben 2027.

An bukaci Jonathan ya fito takara a 2027
Hoton tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan a wajen wani taro Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Facebook

Shugaban kungiyar na kasa, Dr. Grema Kyari ya bayyana hakan yayin da yake yake jawabi a taron manema labarai a Kano, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

'Ka dawo gida da gaggawa: An buƙaci Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci a jihohin Arewa 2

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An yaudari 'yan Najeriya kan Goodluck Jonathan

Kungiyar ta jaddada cewa an yaudari ‘yan Najeriya a shekarar 2015 wajen kada kuri’a domin kifar da gwamnatinsa.

Ta bayyana cewa tsohon shugaban kasan shi ne hanyar da ta fi tabbaci wajen ceto Najeriya daga yunwa, rashin tsaro da rabuwar kai da ake fama da su ƙarƙashin gwamnatin jam’iyyar APC.

Dr. Grema Kyari ya kawo hujjar cewa dawowar Jonathan ba wai kawai abin so ba ne, amma wajibi ne, inda ya kawo misalan shugabanni a duniya da suka dawo siyasa, kamar Donald Trump a Amurka da John Mahama a Ghana.

"An yaudari ‘yan Najeriya a 2015 ta hannun APC karkashin marigayi Muhammadu Buhari, Bola Tinubu, Yemi Osinbajo, da Cif Bisi Akande."
"Sun sayar wa ‘yan kasa da alkawuran karya da ba su cika ba. Maimakon ci gaba, kasar ta fada cikin yunwa, talauci da takaici."

- Dr. Grema Kyari

Kara karanta wannan

Jam'iyyar ADC ta yi martani bayan an zarge ta da yaudarar 'yan Najeriya

Meyasa ya kamata Jonathan ya yi takara?

Ƙungiyar ta nace cewa Jonathan ne ya jagoranci lokaci na karshe da Najeriya ta samu daidaiton tattalin arziki, inda aka samu farashin kayan abinci mai sauƙi, fetur mai rahusa, da shirye-shiryen karfafa matasa kamar YouWin! da SURE-P.

An ba Jonathan shawara kan zaben 2027
Hoton Goodluck Jonathan na jawabi a wajen wani taro Hoto: Goodluck Jonathan
Source: Instagram
"A lokacin Jonathan, ana sayar da buhun shinkafa kusan N7,800, yau kuwa buhu ɗaya yana kai wa tsakanin N80,000 zuwa N100,000. Miliyoyin mutane sun fada cikin yunwa."

- Dr Grema Kyari

Shugaban ƙungiyar ya ƙara da cewa halin Jonathan na kasancewa shugaba mai haɗa kan kowa, wanda ya naɗa jami’ai daga kabilu da addinai daban-daban, ya sa shi ya dace da zama wanda zai warkar da rabuwar kai a Najeriya.

Baya ga roƙon Jonathan ya tsaya takara, ƙungiyar ta kuma roki sauran manyan ‘yan adawa, ciki har da Atiku Abubakar, Rabiu Musa Kwankwaso, Peter Obi, Rotimi Amaechi, Nasir El-Rufai, da su a ajiye muradunsu don goyon bayan Jonathan.

Shehu Sani ya ba Jonathan shawara

Kara karanta wannan

ADC: An samu wanda zai dawo da tallafin man fetur idan ya zama shugaban kasa a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon sanatan Kaduna ta Tsakiya, Shehu Sani, ya shawarci Goodluck Jonathan, kan yin takara a zaben 2027.

Sanata Shehu Sani ya bukaci tsohon shugaban kasan da ka da ya nemi takarar shugabancin Najeriya.

Tsohon sanatan ya bayyana cewa abubuwa sun tabarbare a jam'iyyar PDP, ba kamar yadda Jonathan ya san ta a baya ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng