2027: An Fadi Abu 1 da Zai Iya ba Tinubu Nasara a Zabe, an ba Shi Shawara

2027: An Fadi Abu 1 da Zai Iya ba Tinubu Nasara a Zabe, an ba Shi Shawara

  • Wani babban jigon APC, Farfesa Haruna Yerima, ya bayyana cewa Bola Tinubu zai yi nasarar 2027 idan ya cigaba da tafiya da Kashim Shettima
  • Kungiyar Northern Ethnic Nationality Forum ta bukaci Tinubu ya sauya Shettima, inda ya ce ikirarin tsoron Musuluntarwa karya ne
  • Yerima ya kara da cewa Shettima ya cancanta, kuma Tinubu ba karamin ɗan siyasa ba ne da za a tilasta masa mataimaki

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Jigon APC a Najeriya ya ba Bola Tinubu shawara kan samun nasara a zaben 2027 da ake tunakra.

Farfesa Haruna Yerima ya ce Tinubu tare da mataimakinsa, Shettima, na iya sake lashe zaben 2027 idan aka cigaba da tsayar da tikitin Musulmi-Musulmi.

An ba Tinubu lakanin cin zaben 2027 a sauki
Jigon APC ya gargadi Tinubu kan sauya Shettima a 2027. Hoto: Kashim Shettima, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Farfesa Yerima ya bayyana hakan ne a Abuja ranar Asabar 23 ga watan Agustan 2025, cewar Daily Nigerian.

Kara karanta wannan

Kungiyar APC ta gargadi Tinubu kan sauya Shettima, ta fadi barazanar da ke tafe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiya ta ba Tinubu shawara game da Shettima

Farfesa Yerima yana mayar da martani ga wata ƙungiya 'Northern Ethnic Nationality Forum' wacce ta bukaci a cire Shettima daga matsayin mataimaki.

Ƙungiyar ta yi ikirarin cewa dole ne Tinubu ya zabi Kirista daga jihohin Plateau, Benue ko Taraba domin kawar da zargin cewa gwamnatinsa na da nufin shimfiɗa tsarin Musulunci a Najeriya.

Haka kuma, ta ce barin tikitin Musulmi-Musulmi zai baiwa adawa damar samun hujjar siyasa wajen yin yaƙin neman zabe a 2027.

2027: Martanin jigon APC kan barazana ga Tinubu

Sai dai Yerima ya bayyana wannan matsayi a matsayin “abun dariya” da kuma zargi da ba shi da tushe.

Ya ce ikirarin cewa Atiku Abubakar da Peter Obi za su kayar da Tinubu da Shettima a tikitin 2027 ba shi da wata hujja ko ingantaccen bincike na siyasa da zai tabbatar da hakan.

Kara karanta wannan

2027: Malamin addini ya 'gano' shirin Amurka domin cire Tinubu da ƙarfin tsiya

Farfesan ya bayyana cewa kungiyar ta yi amfani da bayanai marasa tushe wajen tada jijiyoyin wuya, musamman batun Musuluntarwa.

A cewarsa, shekaru biyu na shugabancin Tinubu sun nuna babu fifiko ga wata ƙungiyar addini.

An shawarci Tinubu ya ci gaba da tafiya da Shettima
Jigon APC ya gargadi Tinubu kan sauya Kashim Shettima. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Twitter

Jigon APC ya fadi alfanun tafiya da Shettima

Yerima ya ce zaɓin Shettima a matsayin mataimaki ya zo ne bayan dogon tunani da tantancewa, kuma duk wani yunƙurin tilasta wa Tinubu ya zaɓi wani daban ba zai yi tasiri ba.

Ya jaddada cewa shugaban ƙasa ba sabon ɗan siyasa ba ne da za a yaudare shi da ƙananan kungiyoyi marasa suna, Daily Post ta ruwaito.

Ya kuma gargadi ’yan siyasa da su daina haɗa addini da siyasa, yana mai cewa batun mataimaki ya ta’allaka ne da amana da ƙwarewa.

Yerima ya ce Shettima yana cika ayyukan da aka dora masa da cikakken kwarewa, jajircewa da gaskiya.

Wannan, a cewarsa, ne ya tabbatar da cewa Tinubu zai ci gaba da samun nasara a 2027 tare da Shettima.

An gargadi Tinubu kan sauya Kashim Shettima

Kara karanta wannan

Bayanai sun kara fitowa daga EFCC, an ji gaskiyar dalilin neman surukin Atiku ruwa a jallo

Kun ji cewa Kungiyar APC North Central Forum ta shiga sahun masu ba shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, shawara kan Kashim Shettima.

Shugaban kungiyar ya shawarci mai girma Bola Tinubu da ka da ya sauya Shettima don tsoron rasa kuri'un yankin Arewa ta Tsakiya.

Saleh Zazzaga ya nuna cewa ajiye Kashim Shettima na iya jawowa shugaban kasan matsala idan ya tashi neman tazarce a shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.