"Yadda Kwankwaso Ke Yaudarar Mabiyansa 'Yan Kwankwasiyya game da NNPP"
- Shugaban tsagin NNPP, Agbo Major ya ce Rabiu Kwankwaso da magoya bayansa sun bar jam'iyyar tun bayan rushewar yarjejeniyarsu
- Ya jaddada cewa babu rarrabuwar kai a NNPP, inda shi da Boniface Aniebonam ke shugabantar kwamitocin jam’iyyar
- Major ya yi zargin cewa Kwankwaso na yaudarar ‘yan Najeriya da cewa yana cikin NNPP, alhali ba ya cikin jam’iyyar tun 2023
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Shugaban tsagin na jam’iyyar NNPP, Agbo Major, ya yi magana kan matsayar Rabiu Musa Kwankwaso a jam'iyyar.
Major ya bayyana cewa Rabiu Musa Kwankwaso da magoya bayansa sun bar cikin jam’iyyar NNPP tun rushewar yarjejeniyarsu a shekarar 2022.

Source: Facebook
An fadi yadda Kwankwaso ke 'yaudarar' mabiyansa
A cikin wata hira da aka yi da shi da TheCable ta bibiya, Major ya ce babu wani bangare ko rarrabuwar kawuna a jam’iyyar NNPP.

Kara karanta wannan
'Karshen APC ya zo,' Gwamnonin PDP sun faɗi abin zai hana jam'iyya mai mulki sake cin zaɓe
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Major ya ce tun daga lokacin ba su da wani sahihin matsayi a cikin jam’iyyar, duk kuwa da ikirarin da suke yi a bainar jama’a.
Ya ce jam’iyyar na da kwamitin gudanarwa ƙarƙashin jagorancinsa da kuma kwamitin amintattu ƙarƙashin Dr. Boniface Aniebonam wanda shi ne wanda ya kafa jam’iyyar.
Major ya karyata rahotannin cewa wasu mutane na shirin gudanar da taron kwamitin zartarwa na kasa da sunan jam’iyyar NNPP, cewar Daily Post.
Ya ce waɗannan mutane dai ‘yan Kwankwasiyya ne na Kano, ƙarƙashin Rabiu Kwankwaso, kuma suna amfani da sunan jam’iyyar wajen yaudarar jama’a.

Source: Twitter
Yadda hakadar siyasa ta wargaje a NNPP
Major ya kara da cewa ainihin gaskiyar ita ce haɗin gwiwar siyasa da ta haɗa NNPP da Kwankwasiyya a 2022 ta rabu a watan Agusta 2023.
Ya bayyana cewa shi da Aniebonam, wanda ya kafa jam’iyyar, da sauran shugabanni sun raba wannan “hadakar siyasa,” don haka Kwankwaso da magoya bayansa ba sa cikin NNPP tun daga lokacin.
Major ya kara da cewa duk da hakan, Rabiu Kwankwaso da magoya bayansa na yaudarar ‘yan Najeriya da cewa har yanzu suna cikin jam’iyyar.
Sai dai a zahiri, bisa tsarin jam’iyyar da tsarin shugabancinta, an riga an raba gari tun lokacin rushewar wannan yarjejeniya.
Ya jaddada cewa shugabancin jam’iyyar na tafiya bisa doka da tsari inda ya ce akwai tsayayyen tsarin gudanarwa ƙarƙashin kwamitin gudanarwa da kuma kwamitin amintattu.
Sannan Major Ya kara tabbatar da cewa babu wani bangare ko rarrabuwar kai a NNPP kamar yadda ake yadawa.
Buba Galadima ya ce babu Kwankwaso babu Tinubu
Kun ji cewa Buba Galadima ya bayyana cewa watakila Sanata Rabiu Kwankwaso ba zai haɗa kai da Shugaba Bola Tinubu da APC a zaben 2027 ba.
Ya ce gwamnatin Tinubu tana amfani da ’yan sanda da kotuna wajen goyon bayan Aminu Ado Bayero duk da an tsige shi daga sarauta.
Buba ya yi ikirari cewa NNPP ce za ta yanke shawarar wanda zai zama shugaban kasa a 2027, tare da jaddada ƙarfin Kwankwaso.
Asali: Legit.ng
