2027: An Hango wa Uba Matsala a Kaduna da Jami'an Gwamnati Suka Ajiye Aiki
- Sauye-sauyen da aka samu a gwamnatin Uba Sani na jihar Kaduna sun jawo cece-kuce kan makomar siyasarsa kafin 2027
- Murabus da Farfesa Muhammad Sani Bello da aka fi sani da Mainan Zazzau ya yi daga gwamnatin Kaduna ya jawo cece-kuce
- Amma duk da rikice-rikicen cikin gida, APC ta lashe manyan kujeru a zaɓen cike gurbi, wanda ke nuni da sauƙin baraka
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Siyasa a jihar Kaduna ta ɗauki sabon salo, lamarin da ke jawo fargaba a kan makomar gwamnatin Uba Sani a 2027.
Murabus da wasu daga cikin manyan jami’ai daga gwamnatin Kaduna ya janyo cece-kuce, musamman ganin yadda siyasar jihar ta fara dumama gabanin babban zaɓen.

Kara karanta wannan
'Kwankwaso ba zai goyi bayan Tinubu a zaben 2027 ba,' Buba Galadima ya kawo dalilai

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa mafi girma daga cikin abin da ya ja hankali shi ne lamarin Farfesa Muhammad Sani Bello.
Farfesa wanda yake rike da sarautar Mainan Zazzau, ya ajiye mukaminsa a majalisar zartarwar Kaduna ranar 29 ga Yuli, 2025.
Wasu rahotannin kuma sun ce gwamna ya tsige shi ne bayan canza masa ma'aikata.
Rawar da Bello ya taka a gwamnatin Kaduna
Trust Radio ta ruwaito cewa Farfesa Muhammad shi ne darektan yakin neman zaɓen Uba Sani a 2023.
Haka kuma ana ganin shi ne ɗaya daga cikin ginshiƙan nasarar gwamnan, don haka, barinsa ya yi murabus ya nuna yiwuwar akwai rarrabuwar kawuna a gwamnatin.
Wasu daga cikin masu sharhi a kan siyasa sun ce ajiye aikin Farfesan na iya zama alamar barazanar rikici a sansanin gwamnan kafin babban zaɓe mai zuwa.
Sai dai, sakamakon zaɓen cike gurbi da aka gudanar a ƙarshen mako ya nuna cewa APC ta ci gaba da samun goyon baya a Kaduna har yanzu.

Kara karanta wannan
APC: Duk da lashe kujera, Ministan Tinubu ya roki INEC ta soke nasarar NNPP a Kano
A Chikun/Kajuru, Basawa da Zaria Kewaye, jam’iyyar ta yi nasara, abin da ya tabbatar da goyon bayan jama’a ga gwamnatin Sani har yanzu.
Ana ta cece-kuce kan siyasar Kaduna
Ko da yake nasarorin zaɓen cike gurbi sun rage kaifin zargin rikicin cikin gida a Kaduna, murabus ɗin Farfesa Muhammad na ci gaba da janyo cece-kuce.
Wasu na kusa da shi sun tabbatar da cewa ya yi murabus da kansa, yayin da wasu a cikin gwamnati suka dage cewa tsige shi gwamnan ya yi.

Source: Twitter
Masu fashin baƙi sun ce Farfesa Muhammad bai samu matsayin da ya dace da rawar da ya taka a zaɓen 2023 ba. Haruna Nasarawa, mai sharhi kan siyasa ya ce:
“Duk da irin ƙoƙarinsa a matsayin DG, an ba shi matsayi da bai dace da tasirinsa ba. Wannan ya jawo rashin jin daɗi. Tun da dadewa ake ta rade-radin cewa bai gamsu da kujerar ba kuma zai iya yin murabus.”
Sai dai wani babban jami’in gwamnati ya bayyana cewa babu wata matsala don Farfesa Muhammad Bello ya ajiye aiki.
Kaduna: Sauran wadanda suka bar gwamnatin Uba
Rahotanni sun nuna irinsu Benjamin Jock sun ajiye mukaminsa a gwamnatin jihar Kaduna. Jock ya kasance babban mai ba gwamna shawara.
Haka zalika Dr Shehu Makarfi, Hassan Rilwan da Umar Hassan Waziri da suka yi aiki da gwamnatin Nasir El-Rufai duk sun yi murabus.
Shi ma babban lauya, Chris Umar SAN ya hakura da kujerar da yake kai na mataimakin shugaban ma'aikata a fadar gwamnatin jihar Kaduna.
Jam'iyyar APC ta yi nasara a Kaduna
A wani labarin, mun wallafa cewa Felix Joseph Bagudu, ɗan takarar jam’iyyar APC, ya yi nasara a mazabar Chikun/Kajuru a Kaduna da kuri’u 34,580 a zaɓen cike gurbi.
Ya yi nasara a kan abokin hamayyarsa ta PDP da ƙuri’u 11,491, yayin da ADC ta kawo ƙuri’u 3,477 kacal, lamarin da ya ƙara nuna goyon bayan APC a Kaduna.
A Zaria Kewaye, Isa Haruna Ihamo na APC ya samu ƙuri’u 26,613, yayin da jam’iyyar hamayya ta PDP ta samu 5,331, ita kuma SDP ta samu kuri'a 5,721.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
