An Jero Wuraren da Aka Samu Matsala a Zaben Cike Gurbin da Aka Yi a Kano da Jihohin Najeriya
- Kungiyar Yiaga Africa, mai sa ido kan harkokin zabe ta tabbatar da cewa zaben cike gurbin da aka yi a Najeriya ya gudana cikin kwanciyar hankali
- Sai dai kungiyar ta ce Najeriya ta wuce matakin gudanar da zabe cikin lumana kadai, ta kai matakin shirya zaben da kowa zai aminta da shi
- Ta ce har yanzun ba a iya aiwatar da tsarin tura sakamako ta intanet yadda ya kamata ba, kuma soke kuri'un da ake yi yana haifar da rudani
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kungiyar masu sa ido kan zaɓe ta Yiaga Africa ta ce an wuce matakin da Najeriya za ta yi tunanin nasara saboda an gudanar da zaɓe cikin lumana.
Kungiyar ta bayyana cewa Najeriya ta wuce wannan matakin, ta kai matsayin da za ta gudanar da sahihin zabe wanda jama'a za su gamsu kuma su amince da shi.

Kara karanta wannan
ADC ta cimma matsaya da Atiku, Peter Obi da Amaechi kan batun takara a zaben 2027

Source: Twitter
Daraktan shirye-shirye na kungiyar Yiaga Africa, Cynthia Mbamalu ce ta bayyana hakan a shirin The Morning Brief na tashar Channels TV a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi zaben cike gurbi cikin lumana
Ta bayyana cewa zabukan cike gurbi da aka yi ranar Asabar da ta gabata a Kano da wasu jihohi 12 sun kasance cikin lumana sai dai wasu mazabu da aka yi yunƙurin tayar da hankula.
“Gaba ɗaya zaben ya kasance cikin kwanciyar hankali, sai dai a wasu mazabu da aka samu matsalar ’yan daba da suka yi yunƙurin tarwatsa zaɓen a wasu rumfuna.
"Amma a zahirin gaskiya dole ne mu wuce batun shirya zaɓe cikin kwanciyar hankali kadai zuwa tsarin zaben da kowa zai aminta da shi.
"Ɗaya daga cikin manyan matsalolin da muka fara fuskanta yanzu shi ne tsarin tattara sakamakon zaɓe."
- Cynthia Mbamalu.
Yiaga Africa ta jero matsalolin da aka samu

Kara karanta wannan
'Abin da ya sa APC ta lashe mafi yawan zabukan cike gurbi da aka yi a Kano da jihohi 12'
Da take haska wuraren da aka samu matsala a zaben makon jiya, ta ce INEC ta tanadi tsarin tura sakamako ta intanet kai tsaye daga rumfunan zabe, amma an gaza aiwatarwa yadda ya kamata.
“INEC ta tanadi tsarin hada sakamakon inda tattara sakamakon ta hanyar intanet ke cikin ka’idojin zaɓe, amma matsalar ita ce yadda ake aiwatar da shi,” in ji ta.
Mbamali ta kuma ƙara da cewa yadda ake yanke hukunci kan aringizon ƙuri’u da soke zaben da aka yi a wasu wuraren na haifar da rudani.

Source: Twitter
Ana zargin jam'iyyu da kawo tangarda
Mbamalu ta kuma dora alhakin nakasa tsarin zaɓe kan jam’iyyun siyasa saboda kwadayin samun mulki ta kowane hali.
“Jam’iyyun siyasa su ya kamata su ɗauki alhakin yadda suke lalata tsarin saboda tsananin son lashe zaɓe ta ko wane hali."
“Za mu iya cewa duk yadda ake ƙara ƙoƙari don ƙarfafa tsarin zabe da haɓaka dimokuraɗiyya, barazanar da ’yan siyasa ke haifarwa na ƙara girma domin su nakasa tsarin,” in ji Mbamalu.
APC ta cika baki kan zabe a mazabu 16
A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ta ce nasarorin da ta samu a zaben cike gurbin da aka yi ya nuna yadda yan Najeriya suka gamsu da mulkin Bola Tinubu.
Jam'iyyar APC dai ta samu nasara a mafi yawan mazabun da aka gudanar da zaben cike gurbi a jihohi 13 a Najeriya.
Mai magana da yawun APC a Legas, Seye Oladejo, ya ce nasarar da jam'iyyar ta samu ya tabbatar da cewa ita ke da rinjayen magoya baya a kasar nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
