Dan Majalisa Ya ba Ɗalibai 308 Tallafin Karatu har N30m, an Fadi yadda Kowa Ya Samu

Dan Majalisa Ya ba Ɗalibai 308 Tallafin Karatu har N30m, an Fadi yadda Kowa Ya Samu

  • Dan majalisar tarayya daga Kebbi, Hon. Sani Yakubu Noma, ya tallafawa dalibai fiye da 300 da kudin makaranta domin cigaba da karatu
  • Babban amininsa, Injiniya Anas Hassan Nabala ya tabbatar da haka, yana cewa Noma na taimakawa al’umma ba tare da nuna bambanci ko wariya ba
  • Kowane dalibi daga cikin 308 ya samu akalla N100,000, abin da ya kara tabbatar da Noma a matsayin mai kishin al’ummarsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Birnin Kebbi - Al'umma da dama sun yabawa ɗan majalisar tarayya daga jihar Kebbi kan tallafawa bangaren ilimi.

Hon. Sani Yakubu Noma ya tallafawa ɗalibai akalla 308 da kudin makaranta domin cigaba da karatu a matsayin hanya mafi nagarta a rayuwarsu.

Dan majalisa ya tallafawa ɗalibai da miliyoyi a Kebbi
Dan majalisa daga Kebbi ya ba dalibai 308 tallafin karatu. Hoto: Injiniya Anas Hassan Nabala.
Source: UGC

Daga daga cikin aminansa, Injiniya Anas Hassan Nabala shi ya tabbatar da haka ga wakilin Legit Hausa a yau Lahadi 17 ga watan Agustan 2025.

Kara karanta wannan

Mamba ya rikita majalisa, an yi masa barazana da ya yi zargin biyan N3m kan kuduri

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nabala ya bayyana ƙoƙarin da san majalisar ke yi wa al'ummarsa ta kowane bangare ba tare da nuna bambanci ba.

Dan majalisar da ke wakiltar mazabar Argungu/Augie ya ba dalibai guda 308 tallafin kudin makaranta.

Dan majalisa ya tallafawa dalibai da N30m a Kebbi
Taswirar jihar Kebbi da ke Arewa maso Yammacin Najeriya. Hoto: Legit.
Source: Original

Aminin dan majalisa ya fadi alheirnsa

Aminin na sa ya ce kowane dalibi daga cikin wadanda suka ci gajiyar ya samu akalla N100,000 domin tallafawa karatunsu.

Nabala ya ce:

"Uban marayun garin Argungu ya sake halinsa, dan majalisar tarayya daga jihar Kebbi, Hon. Sani Yakubu Noma.
Dan majalisar ya gwangwaje daliban Argungu/Augie sama da dalibai 308 da kudin makaranta."

Nabala ya jinjinawa dan majalisar duba da yadda yake ba al'ummar yankinsa tallafi ba iya na bangaren karatu zalla ba.

Dan majalisa ya yiwa marayu auren gata

Mutane da dama sun yabawa dan majalisar kan irin kokari da yake yi ga yan mazabarsa inda wasu ke burin a ce duk yan majalisu a Najeriya su zama na gari kamarsa.

Kara karanta wannan

Tinubu ya sakawa kanwar Abdussamad BUA, ya ba ta mukami a gwamnatinsa

Ko a shekarar 2023 ma, Hon. Noma ya aurar da mata marayu akalla guda 100 inda ya tallafa musu wanda yana daga cikin gudunmawar da yake ba marayu.

Da yake magana a mahaifarsa ta Argungu da ke jihar Kebbi a wancan lokaci, dan majalisar ya ce shirin yi wa yan matan auren gata yana daga cikin gudunmawarsa na kula da jin dadin marayu a mazabarsa.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa an yi bikin auren ne a fadar Sarkin Argungu a ranar Asabar 25 ga watan Nuwambar shekarar 2023.

Dan majalisa daga Sokoto ya jika limamai

A baya, mun ba ku labarin cewa dan majalisar tarayya daga jihar Sokoto a Arewa maso Yammacin Najeriya, Hon. Sani Yakubu ya gwangwaje yan mazabarsa da abubuwan alheri.

Dan siyasar mai wakiltar mazabar Gudu/Tangaza ya ba da tallafin N40m da buhuna 1,000 na shinkafa ga al’ummarsa duba da halin da ake ciki na matsin tattalin arziki.

Hon. Sani Yakubu ya yi wannan abin alheri ne don saukaka wa al'umma yayin azumin watan Ramadan da ya gabata wanda yan ƙasar ke kokawa saboda halin kunci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.