Ministan Tsaro Ya Faɗi a Mazaɓarsa kamar yadda Ake Yaɗawa? Badaru Ya Magantu

Ministan Tsaro Ya Faɗi a Mazaɓarsa kamar yadda Ake Yaɗawa? Badaru Ya Magantu

  • Ministan tsaro, Mohammed Badaru Abubakar ya yi martani kan jita-jitar cewa ya fadi a mazabarsa a zaben cike gurbi
  • Badaru ya karyata rade-radin cewa ya sha kaye a rumfar zabe, inda ya ce labarin karya ne babu kamshin gaskiya a ciki
  • INEC ta tabbatar da sahihin sakamakon rumfar zabe inda APC ta samu kuri’u 188, PDP 164, abin da ya tabbatar da nasarar Badaru

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Dutse, Jigawa - Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar, ya fito ya yi karin haske kan zaben cike gurbi da aka gudanar.

Badaru ya yi magana kan bayyana cewa masu ta da fitina ne suka yada sakamakon karya da ke cewa ya sha kaye a rumfar zabensa.

Badaru ya ƙaryata rahoton faduwa a mazabarsa
Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar yayin taro da jami'an tsaro a Abuja. Hoto: Defence Headquarters Nigeria.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da mai taimaka masa, Mati Ali, ya fitar a Kaduna ranar Lahadi 17 ga watan Agustan 2025, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

An samu rudani a sakamakon zaben akwatun Ministan Tsaron Najeriya, APC ta sha da kyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton da aka yada kan faduwar Badaru

Wannan martani ya biya bayan wasu rahotanni da safiyar yau da ke cewa Badaru ya sha kaye a mazabarsa da ke jihar Jigawa.

Lamarin ya jawo maganganun yayin da masoyansa ke ƙaryata labarin su kuma yan adawa ke farin ciki kan lamarin.

Martanin Badaru kan jita-jitar da kasa yaɗawa

Mati Ali ya ce sakamakon da ake yadawa ba gaskiya ba ne saboda ba ainihin mazabar Badaru ba ne.

Ya ce a cikin hankoronsu, sun hada shi da rumfa ta 001, alhali kuwa rumfarsa ta gaskiya ita ce Babura Kofar makarantar Firamaren Arewa PU 002.

Sanarwar ta ce:

“Mun samu bayanai kan yaduwar sakamakon zabe daga rumfar Babura Kofar Arewa 001, an yi makirci da shi ga Ministan Tsaro.”
Badaru ya soki masu yada rahoton cewa ya fadi a mazabarsa
Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar yayin taro da jami'an tsaro a Abuja. Hoto: HQ Nigerian Army.
Source: Facebook

An fayyace gaskiya kan rahoton faduwar Badaru

Sanarwar ta kara da cewa wannan ikirari ba gaskiya ba ne, an shirya shi da nufin bata sunan Ministan Tsaro, Mohammed Badaru Abubakar.

Kara karanta wannan

Mummunan hadari a Kano ya jawo asarar rayuka sama da 10

“Domin kawar da shakku, rumfar Minista ta gaskiya ita ce makarantar Babura Kofar Arewa PU 002, inda ya kada kuri’arsa a zaben.
“Ainihin sakamakon da INEC ta sanar shi ne: APC ta samu kuri’u 188, PDP ta samu kuri’u 164,”

- Cewar sanarwar

Sanarwar ta ce wannan sahihin sakamakon ya tabbatar da cewa Minista ya yi nasara a rumfarsa inda jam’iyyarsa APC ta samu rinjaye, cewar The Guardian.

Ta kara da cewa:

“Mun sake tabbatarwa cewa a rumfar Babura Arewa PU 002, Minista Mohammed Badaru Abubakar ya lashe zaben Garki/Babura da aka yi Asabar.
“Don haka muna kira ga jama’a, ‘yan jam’iyya da kafafen yada labarai da su yi watsi da labaran karya, su tsaya kan sahihin sakamakon INEC.”

Majalisa ta yi barazana ga mambanta a Jigawa

Mun ba ku labarin cewa Majalisar wakilai ta bukaci Hon. Ibrahim Auyo ya kawo hujja kan zargin cewa ana biyan kuɗi kafin gabatar da kudiri.

Auyo ya ce 'yan majalisa na biyan har Naira miliyan uku kafin gabatar da kudiri, tare da bin kafa daga sauran mambobi.

Kakakin majalisar ya ce idan Auyo bai gabatar da hujja ba, za a kai shi gaban kwamitin ladabtarwa na majalisar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.