APC, PDP Sun Sha Kashi a Zaben Cike Gurbin Sanata Ubah da Ya Rasu
- Jam'iyyar APGA ta samu nasara a zaben cike gurbi na kujerar sanatan Anambra ta Kudu da aka gudanar a ranar Asabar, 17 ga watan Agustan 2025
- Dan takarar APGA, Emmanuel Nwachukwu, ya lallasa abokan hamayyarsa da suka fafata a zaben
- Hakazalika, jam'iyyar APGA ta lashe zaben cike gurbi na kujerar dan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Anambra ta Arewa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Anambra - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta sanar da sakamakon zaben cike gurbi na sanatan Anambra ta Kudu.
Hukumar INEC ta ayyana dan takarar jam'iyyar APGA, Emmanuel Nwachukwu, a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbi na kujerar Sanatan Anambra ta Kudu da aka gudanar a ranar Asabar.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta rahoto cewa hukumar zabe ta INEC ta sanar da sakamakon a ranar Lahadi, 17 ga watan Agustan 2025 a karamar hukumar Nnewi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan takarar APGA ya yi nasara a Anambra
Jami’in tattara sakamakon zaɓen a ofishin INEC na Nnewi, Farfesa Frank Ojiako, ya bayyana cewa Nwachukwu na APGA shi ne ya lashe kujerar Sanatan Anambra ta Kudu.
Nwachukwu ya samu kuri’u 90,408, inda ya doke babban abokin hamayyarsa, Cif Azuka Okwuosa, ɗan takarar APC wanda ya samu kuri’u 19,847.
Hakazalika, dan takarar jam'iyyar ADC, Donald Amangbo ya zo na uku da kuri’u 2,889.
"Ina sanar da cewa Emmanuel Nwachukwu na APGA, bisa cika sharuddan doka, an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaɓen kuma an bayyana shi a matsayin zaɓaɓɓe."
- Farfesa Frank Ojiako
Ya yaba da yadda ’yan takara suka gudanar da kansu cikin kwanciyar hankali, tare da gode wa masu zaɓe bisa fitowar da suka yi da yawa domin kada kuri’a.
Rasuwar Sanata Ifeanyi Ubah, wanda ya wakilci Anambra ta Kudu a majalisar dattawa a watan Yuli 2024, ne ya sa aka gudanar da zaɓen cike gurbi wanda jam’iyyu 12 suka shiga a ranar 16 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan
Duk da tasirin El Rufai, APC ta lashe zaben cike gurbi da tazara mai yawa a Kaduna

Source: Original
APGA ta lashe zaben dan majalisar dokokin jiha
Haka kuma, INEC ta ayyana Ifeoma Azikiwe ta APGA a matsayin wadda ta lashe zaɓen cike gurbi na kujerar majalisar dokokin jihar Anambra, mazabar Onitsha ta Arewa 1, rahoton Vanguard ya tabbatar.
Yayin sanar da sakamakon a Onitsha, jami’in tattara sakamakon zaben, Farfesa Ibiam Ekpe, ya bayyana cewa Ifeoma Azikiwe ta samu kuri’u 7,774, inda ta doke abokiyar hamayyarta, Justina Azuka ta ADC, wadda ta samu ƙuri’u 1,909.
Ya kara da cewa ɗan takarar APC, Ezennia Ojekwe, ya samu ƙuri’u 1,371, yayin da ɗan takarar YPP, Njideka Ndiwe, ya samu ƙuri’u 655.
APC ta lashe zaben cike gurbi a Jigawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar APC ta samu nasarar lashe zaben cike gurbi na mazabar Garki/Babura a jihar Jigawa.
Dan takarar APC, Alhaji Rabiu Mukhtar, ya lallasa abokin hamayyarsa na jam'iyyar PDP, Auwal Isah Manzo.
An dai gudanar da zaben don cikin gurbin da Hon. Isa Yaro, ya bari bayan rasuwarsa a watan Mayun shekarar 2024.
Asali: Legit.ng
