Babu Labarin Fintiri da Atiku, INEC Ta Sanar da Sakamakon Zaɓen Cike Gurbi a Adamawa

Babu Labarin Fintiri da Atiku, INEC Ta Sanar da Sakamakon Zaɓen Cike Gurbi a Adamawa

  • Hukumar INEC ta bayyana sakamakon zaben cike gurbi da aka yi a mazabar Ganye a jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas
  • Hukumar ta bayyana Misa Musa Jauro na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbi na Ganye da kuri’u 15,923
  • Dan takarar PDP ya samu kuri’u 15,794, inda sakamakon ya kasance da banbancin kuri’u 129 kacal

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ganye, Adamawa - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta sanar da sakamakon zaben cike gurbi da aka yi a jihar Adamawa.

Hukumar ta bayyana Misa Musa Jauro na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen cike gurbi na Ganye a Jihar Adamawa.

APC ta lashe zaben cike gurbi a Adamawa
Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri da mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro, Nuhu Ribadu. Hoto: Nuhu Ribadu, Governor Ahmadu Umaru Fintiri.
Asali: Twitter

Adamawa: INEC ta sanar da sakamakon zabe

Mai sanar da sakamako, Farfesa Tukur Ahmed, yayin bayyana Musa Jauro a matsayin wanda ya yi nasara, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

ADC, PDP sun kwashi kashinsu a hannu, APC ta lashe zabe da tazara mai yawa a Ogun

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ahmed ya ce dan takarar APC ya samu kuri’u 15,923, ya doke abokin hamayyarsa na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 15,794.

Zaɓen da aka yi a jiya Asabar ya gudana a dukkan mazabu 10, inda aka bayyana shi a matsayin ɗaya daga cikin zaben da aka fafata a baya-bayan nan.

APC da PDP suka yi nasara a wurare daban-daban, amma dan takarar APC ya samu banbanci na kuri’u 129 kacal, Daily Nigerian ta tabbatar.

APC ta yi nasara a zaben Adamawa

Da wannan sakamako, an bayyana Jauro a matsayin wanda ya ci zaɓen bisa doka, wanda ya tabbatar da nasarar APC a wannan zaɓe.

Jauro, wanda shi ne yaya ga mamacin dan majalisar da ya mutu, shi ma ya tsaya takara a ƙarƙashin jam’iyyar da ɗan’uwansa ya fito.

An bayyana zaɓen cike gurbin a matsayin wanda ya gudana lafiya a dukkan mazabu 10, duk da cewa jam’iyyun biyu sun zargi juna da wasu kura-kurai a lokacin zaɓen.

Kara karanta wannan

Kano: INEC ta sanar da sakamakon zaben cike gurbi na Ghari, Tsanyawa

An fara bayyana sakamakon zabe a jihohin Najeriya
Taswirar jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabas a Najeriya. Hoto: Legit.
Asali: Original

Yadda sakamakon zaɓe ya kasance a Kano

Hakan ya biyo bayan gudanar da zabukan cike gurbi da aka yi a fadin Najeriya baki daya a ranar Asabar 16 ga watan Agustan 2025.

Hukumar INEC ta sanar da sakamakon zabukan a jihohi da dama ciki har da Kano da Edo da sauransu.

Kamar a jihar Kano, jam'iyyar NNPP mai mulkin jihar ta kashe kujerar dan majalisa yayin APC ma mai adawa ta samu nasara a mazabar Ghari/Tsanyawa.

INEC ta sanar da sakamakon zabe a Kano

Kun ji cewa Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta kammala tattara kuri'un da aka kada a zaben cike gurbin dan Majalisar Shanono/Bagwai a Kano.

Dan takarar NNPP, Ali Lawan Alhassan ne ya samu nasara da kuri'u mafi rinjaye a zaben da aka gudanar jiya Asabar, 16 ga watan Agusta, 2025.

A sakamakon da INEC ta sanar, NNPP mai mulki ta samu kuri'u 16,198 yayin da jam'iyyar adawa watau APC ta samu kuri'u 5347.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.