Rigima Ta Kunno Kai a ADC, an Dakatar Shugaban Jam'iyya da wasu Manyan Jagorori 2
- Jam'iyyar hadaka ta ADC ta samu kanta a rikicin siyasa tsakanin tsofaffin 'ya'yanta da sababbin da suka shigo
- Sakataren yada labarai na ADC a Kebbi, ya sanar da dakatar da shugaba, mataimaki da sakatariyar jam'iyyar
- Ya zarge su da yin abubuwa ba tare da shawara ba tare da jawo 'yan siyasar Abuja wadanda ke son mamaye jam'iyyar
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Kebbi - Rikicin siyasa ya kunno kai a jam’iyyar ADC ta jihar Kebbi tun bayan shigowar sababbin ’yan jam’iyya.
Tsofaffin jagororin jam’iyyar ADC a jihar sun dakatar da shugaban jam’iyyar, Injiniya Sufiyanu Bala, mataimakinsa Junaidu Muhammed Mudi, da kuma sakatariyar jam’iyyar, Hauwa Muhammed.

Asali: Facebook
Sakataren yada labarai na jam’iyyar, Jamilu Muhammed, ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a birnin Kebbi, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An dakatar da shugaban ADC a Kogi
Jamilu Muhammad ya zargi kwamitin gudanarwa da Sufiyanu ke jagoranta da yanke shawara ba tare da tuntubar shugabannin jam’iyyar ba, tare da gudanar da ayyukan hukuma ba tare da samun amincewar kwamitin koli na jam’iyyar ba.
Ya ce an kira taron ne domin sanar da dakatar da Sufiyanu Bala, mataimakinsa, da sakatariyar jam’iyya, Hauwa Muhammed daga jam’iyyar nan take.
Ya kuma yi zargin cewa shugabancin nasu ne ya bai wa ’yan siyasar Abuja masu yawo damar mamaye jam’iyyar, lamarin da wadanda suka assasa jam’iyyar ke adawa da shi sosai.
"Ba za mu bari bayan gina jam’iyyar zuwa wannan matsayin ’yan siyasar Abuja su mamaye ta ba.”
- Jamilu Muhammed
Jamilu Muhammed ya bayyana cewa an yanke hukuncin dakatar da su ne a wani taro na gaggawa da shugabanni da mambobin jam’iyyar na gaskiya suka gudanar, wadanda suka kasance masu biyayya ga jam’iyyar tun kafin shigowar 'yan siyasar Abuja.
Jam'iyyar ADC ta nada shugannin riko
Jam’iyyar ta nada Abdulrazaq Abubakar Isah Iko a matsayin shugaban riko, yayin da Adamu Aliyu zai rike mukamin sakataren ADC na jihar har zuwa lokacin da za a gudanar da sabon zaben shugabanni, rahoton The Sun ya tabbatar da haka.

Asali: Facebook
Jam'iyyar ADC a Kebbi ta gargadi wadanda aka dakatar da su da su daina gabatar da kansu a matsayin ’yan jam’iyyar, tare da daina shiga harkokin jama’a ko na kashin kai da sunan jam’iyyar.
Sun kuma yi Allah wadai da tarurrukan siyasa da mambobin kwamitin da aka dakatar ke gudanarwa, suna mai cewa kamfen a yanzu ya sabawa dokar zabe, don haka jam’iyyar ba ta yarda da shi ba.
Jam’iyyar ta bukaci INEC da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki su dauki mataki kan masu karya doka.
ADC ta zargi EFCC da muzgunawa 'yan adawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta nuna rashin gamsuwarta kan tsare tsohon gwamnan jihar Sokoto da hukumar EFCC ta yi.
Jam'iyyar ADC ta yi zargin cewa hukumar EFCC ta zama karen farautar APC wajen muzgunawa 'yan hamayya.
ADC ta bayyana cewa hukumar EFCC tana tsangwamar 'yan adawa yayin da ko kadan ba ta bincikar mutanen da ke cikin jam'iyya mai mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng