'Ka Rage Girman Kai': An Shawarci Kwankwaso kan Abin da Ya Kamata Ya Yi Wa Ganduje
- Kwamred Faizu Alfindiki ya yi magana kan siyasar jihar Kano da jita-jitar sauya shekar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zuwa APC
- Alfindiki ya shawarci RabiuKwankwaso kan yadda zai samu damar shiga APC cikin sauki ta hannun tsohon shugaban APC, Abdullahi Ganduje
- Ya ce Ganduje mutum ne mai kyakkyawar zuciya wanda zai iya karɓar Kwankwaso idan ya nuna nadama kan sabanin da suka taba yi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano, Najeriya – Wani babban jigo na jam’iyyar APC, Faizu Alfindiki, ya ba Sanata Rabi'u Kwankwaso shawara kan siyasa.
Alhaji Alfindiki ya shawarci Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nemi afuwar shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje.

Asali: Twitter
An shawarci Kwankwaso ya cire girman kai
Hakan na cikin wani rubutu da Kwamred Alfindiki ya yi a shafinsa na Facebook a yau Litinin 11 ga watan Agustan 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Jigon APC ya ce idan har Kwankwaso yana son shiga jam’iyyar mai mulki dole ya yi abin da ya kamata ga Ganduje.
A cewar Alfindiki, Rabiu Kwankwaso zai samu nasarar burinsa idan ya “cire girman kai” ya nemi sulhu da Ganduje.
Yabon da Ganduje ya samu game da halayensa
Jigon APC ya bayyana Ganduje a matsayin mutum mai kyakkyawar zuciya, wanda koyaushe yake son karɓar abokan siyasa idan sun nuna nadama.
Ya kara da cewa matakan da Kwankwaso ke dauka yanzu, musamman kusancinsa da tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ba zai kawo masa kwanciyar hankali ba.
Alfindiki ya ce dukan abubuwan da yake yi shirme ne, sulhuntawa da Ganduje shi ne hanya mafi sauki da zai samu abin da yake so.
Jigon APC ya caccaki tsarin siyasar Kwankwaso
Alfindiki ya caccaki dabarun siyasar tsohon gwamnan Kano, yana mai cewa suna nuna “rudani da rashin tabbas.”
Ya gargade shi cewa:
“Ba kowane lokaci ba ne ke bukatar matakai masu tsanani musamman idan ana cikin wani yanayi.
"A bayyane yake siyasar Kwankwaso na neman durkushewa kuma babu wata alama ta cewa zai sake farfaɗo da ita."

Asali: Twitter
Ganduje: Shawarar da aka ba Sanata Kwankwaso
Ya kuma shawarce shi da ya mayar da hankali kan damar siyasa da ke Kano maimakon neman agaji a wani wuri.
Kwamred Alfindiki ya ce abin da yake nema daga Otuoke yana nan Kano idan ya nemi afuwar Ganduje cikin sauki zai same shi.
Sannan ya tabbatar da cewa jam’iyyar na da cikakken karfi a Kano ko da ba tare da Kwankwaso ba, inda ya ce matakin shiga APC yana hannunsa.
An yi magana kan shigar Kwankwaso APC
A baya, mun ba ku labarin cewa ana ci gaba da batun yiwuwar komawar madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jam'iyyar APC.
Shugaban tsagin jam'iyyar NNPP reshen jihar Kano, Jibril Doguwa ya bayyana cewa akwai yiwuwar Kwankwaso ya koma ya hade da Bola Tinubu.
Doguwa ya nuna cewa su dai za su ci gaba da zama a NNPP ko da akwai Kwankwaso da 'yan Kwankwasiyya ko babu su.
Asali: Legit.ng