ADC: Sakataren Gwamnatin Buhari Ya Yi Magana kan Fatali da Jam'iyyar APC

ADC: Sakataren Gwamnatin Buhari Ya Yi Magana kan Fatali da Jam'iyyar APC

  • Tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya yi magana kan kabarin cewa ya yi watsi da jam'iyyarsa ta APC
  • Boss Mustapha ya musanta rahotannin da ke danganta shi da kawancen ‘yan adawa da kuma rungumar jam’iyyar ADC
  • Ya ce kamar kowace jam'iyya, APC na fama da ƙalubale, amma ficewa daga cikinta ba shi ne maslaha a halin da ake ciki ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Tsohon sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya karyata rahotannin da ke danganta shi da kawancen ‘yan adawa.

Haka kuma, ya musanta zargin cewa ya rungumi jam’iyyar ADC a matsayin sabuwar mafakar siyasar sa.

Tsohon Sakataren Gwamnatin tarayya, Boss Mustapha
Boss Mustapha ya yi magana kan rabuwa da APC Hoto: Adeyanju Deji
Asali: Facebook

The Cable ta ruwaito cewa, a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Boss Mustapha ya bayyana rahotannin da ake yadawa a kan lamarin a matsayin ƙarya.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba: 'Yadda Sadiq Gentle ya cika alhali muna shirin kai shi asibitin kasar waje'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sakataren gwamnatin Buhari ya magantu kan ADC

Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Boss Mustapha ya ce bai taɓa shiga tattaunawa da kowa a jam’iyyun adawa ko abokan kawancensu ba.

A cewarsa:

“Hankalina ya kai kan wani labari da ake yadawa da ke danganta ni da kawancen ‘yan adawa da kuma zaben ADC a matsayin jam’iyyata."
Ina so jama’a su sani cewa wannan labarin ƙarya ne. Ba ni a cikin kowace kawancen ‘yan adawa, kuma ban tattauna da au ba.”

'Ina APC,' Cewar tsohon Sakataren gwamnatin Buhari

Boss Mustapha ya tuna yadda ya taimaka a matsayinsa na mataimakin shugaban jam’iyyar ACN na ƙasa kafin haɗewar jam’iyyun da su ka samar da APC.

Ya ce:

“A matsayina na mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar ACN, wadda ita ce babbar jam’iyya da ke da gwamnoni shida a lokacin haɗewar da ta samar da APC, zan iya cewa ni ɗaya ne daga cikin waɗanda suka kafa jam’iyyar mai mulki."

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya ba iyalan 'yan wasan kano da su ka rasu tallafin miliyoyin Naira da filaye

“Saboda haka, ba zan iya barin jam’iyyar da na taimaka wajen kafa ta ba.”
Manyan hadakar adawa ta ADC
Boss Mustapha ya barranta kansa da ADC Horo: Atiku Abubakar
Asali: Facebook

Ya ƙara da cewa, ko da yake APC kamar kowace jam’iyya tana da ƙalubale, mafita ita ce a gyara daga ciki gida maimakon sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya.

A cewarsa:

“Idan jam’iyyarmu tana da matsala, kamar yadda sauran jam’iyyu ma ke da matsaloli, za mu tsaya a ciki mu gyara. Ba ma magance matsala ta hanyar sauya sheƙa zuwa wata jam’iyya.”

Shugabanni ADC a jihohi sun yi tutsu

A wani labarin, kun ji cewa rikicin da ya dabaibaye ADC ya ƙara ɗaukar zafi bayan shugabannin jam’iyyar na jihohi su ka ki aminta da jagorancin David Mark.

Jagororin sun bayyana matsayarsu ne a cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar shugabannin ADC na jihohi, Elias Adokwu, da sakataren yaɗa labarai, Godwin Alaku, suka sa wa hannu. Shugabannin ADC na jihohi sun bayyana kawancen da ke ƙarƙashin David Mark a matsayin “dabarar juyin mulki” don kwace tare da neman ɗaukin jami'an tsaro.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.