2027: Komai na Iya Faruwa da Takarar Atiku da Ake Hasashen Jonathan Zai Dawo ADC
- Tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar ya dage karɓar katin ADC saboda ana tunanin zai sauya tunani
- Hakan ya faru ne saboda rade-radin cewa tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan na iya tsayawa takara a 2027
- Wata majiya ta ce ADC na tattaunawa da Jonathan, yayin da ake cece-kuce tsakanin Atiku, Peter Obi da wasu gwamnoni kan tsari na jam’iyyar
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - An fara hasashe kan cewa akwai alamun tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi takara a 2027.
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya dage shirin karɓar katin zama mamba na ADC, duk da jita-jitar Jonathan na iya tsayawa takara a jam'iyyar.

Asali: Facebook
Ana zargin ADC na magana da Jonathan
Rahoton ya tabbatar da cewa ana zargin ADC na tattaunawa da Jonathan domin dawo wa cikinta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Atiku, wanda ya yi murabus daga jam’iyyar PDP bayan rikice-rikicen cikin gida, ya shirya shiga ADC ta hanyar karɓar katin a garinsa na Jada, Adamawa.
An shirya ba shi katin daga jami’an ADC a Jada, amma an dage bikin ranar Laraba, 6 ga Agusta, ba tare da bayani ba.
Wani jagoran ADC ya ce suna tattaunawa da tsohon shugaban kasa Jonathan kan yiwuwar tsayawa takara a 2027 a jam’iyyar ADC.

Asali: Getty Images
Matsin lamba da ake yi ga Atiku
Majiyoyi sun ce magoya bayan Atiku a ADC suna matsa wa shugabanni su bar jam’iyyar idan rikicin bai ƙare ba cikin lokaci.
Wani babban jami’in ADC ya ce suna samun martani mai kyau daga Jonathan, wanda ba zai tsaya a PDP ba saboda matsalolin jam’iyyar.
Ya ce shugabannin kawancen sun gana da Jonathan sau uku, kuma ya yaba da kokarin kawo sauyi ga kasar daga matsalolin tattalin arziki.
Kakakin Atiku, ADC sun yi martani
Mai magana da yawun ADC, Bolaji Abdullahi, ya ce jam’iyyar a bude take ga duk wani dan Najeriya da ke son ceto kasa daga wannan hali.
Sai dai kuma a bangarensa, Kakakin Atiku Abubakar, Paul Ibe, ya ce Atiku ba ya tsoron kowanne ɗan takara ciki har da Jonathan da Obi, duk kuwa da rade-radin siyasa.
Ya ce rade-radin cewa Atiku ya dakatar da shirin karɓar katin ADC saboda Jonathan ba gaskiya ba ne, rajistarsa na ci gaba yadda aka tsara.
Ibe ya ce Atiku kwararren dan siyasa me kuma zai iya gogayya da kowane dan siyasa a Najeriya.
Ana zargin Jonathan ya yiwa Obi tayin minista
A baya, mun ba ku labarin cewa ana zargin tsohon shugaban ƙasa, Goodluck Jonathan ya fara ƙoƙarin janye Peter Obi daga haɗakar ƴan adawa domin ya mara masa baya.
Dumebi Kachikwu ya yi ikirarin cewa Jonathan ya yiwa Peter Obi tayin kujerar minista mai gwaɓi domin ya janye masa takara a 2027.
Ɗan takarar ADC a 2023 ya zargi Atiku da wasu manyan Arewa da ɓata sunan duka ƴan Kudu domin cimma burinsa na hawa mulki.
Asali: Legit.ng