Jam'iyyar NNPP Ta Yi Wa APC illa a Mazabar Ganduje a Kano

Jam'iyyar NNPP Ta Yi Wa APC illa a Mazabar Ganduje a Kano

  • Jam'iyyar NNPP mai mulki a jihar Kano, ta samu karuwa bayan daruruwan mambobin APC sun sauya zhwa cikinta
  • Mambobin na APC sun sauya shekar ne a mazabar tsohon shugaban jam'iyyar na kasa, Abdullah Umar Ganduje, da ke karamar hukumar Dawakin Tofa
  • Tsofaffin mambobin na APC sun samu tarba daga wajen gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf a gidan gwamnatin Kano

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kano - Mambobin APC a Dawakin Tofa, mazabar tsohon shugaban jam'iyyar na ƙasa, Abdullahi Ganduje, a jihar Kano, sun sauya sheƙa zuwa NNPP.

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya karɓi waɗanda suka sauya sheƙar a fadar gwamnatin jihar Kano a ranar Juma’a.

Mambobin APC sun koma NNPP a Kano
Mambobin APC a mazabar Ganduje sun koma APC Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature, ya fitar a shafinsa na Facebook.

Kara karanta wannan

Sule Lamido ya samo mafita ga PDP kan mutanen da suka yi mata zagon kasa a 2023

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Abba ya tarbi 'yan APC zuwa NNPP

Da yake jawabi a wajen taron, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana sauya sheƙar a matsayin tabbacin amincewa da shirye-shirye da manufofin gwamnatinsa a cikin shekaru biyu da suka gabata.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tuna lokacin yaƙin neman zaɓensa na 2023, inda ya ziyarci dukkan ƙananan hukumomi 44, ciki har da Dawakin Tofa.

"Na yi alkawarin samar da ribar dimokuraɗiyya zuwa kowane yanki na jihar Kano. Dawakin Tofa muhimmin yanki ne a fafutukar mu, kuma ni ne mutum mafi farin ciki ganin wannan gagarumin sauya sheƙa daga APC zuwa NNPP."

- Gwamna Abba Kabir Yusuf

Ya lissafa wasu daga cikin ayyukan gwamnatinsa a Dawakin Tofa, ciki har da kammala hanyar kilomita biyar da tsohuwar gwamnati ta bari, tare da yin alkawarin gina sabuwar makaranta a yankin.

Gwamnan ya tabbatar wa sabbin mambobin na NNPP cewa za a haɗa su cikin jam’iyyar gaba ɗaya ba tare da nuna bambanci ko tsoro ba, tare da alkawarin isar da ƙarin ribar dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

Kanawa na cikin alheri, Tinubu zai musu jirgin kasa na Naira tiriliyan 1.5

A nasa jawabin, shugaban ƙaramar hukumar ya bayyana kammala ayyuka a makarantu 15 na firamare da tallafa wa sama da ɗalibai 1,000 a manyan makarantu.

'Yan APC sun koma NNPP a Kano
NNPP ta samu karuwa a Kano Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Tsofaffin 'yan APC sun samu tarba

Shugaban NNPP na jihar Kano, Hon. Hashim Dungurawa, ya taya masu sauya sheƙar murna tare da bayyana kwarin gwiwa cewa Dawakin Tofa za ta maimaita nasarar zaɓen 2023 da jam’iyyar ta samu a Gwale.

Cikin waɗanda suka koma NNPP akwai Hon. Nura Tumfafi, Hon. Isyaku Dahiru Kwa, Alhaji Umar Ismail, Alhaji Abba Muntari, Sani Shafiu, Hussaini Adamu, Alhaji Abdullahi Ayuba, Magaji Ruba-Ruba, Sabo Adamu, da Abdullahi Sale Turaki.

Kwanwaso zai iya barin NNPP

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban tsagin jam'iyyar NNPP na jihar Kano, ya bayyana cewa madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, zai iya komawa APC.

Jibril Doguwa ya bayyana cewa akwai yiwuwar tsohon dan takarar shugaban kasan a zaben 2023, ya yi aiki tare da Shugaba Bola Tinubu.

Hakazalika, ya bayyana cewa za su ci gaba da kasancew a NNPP, ko da akwai ko babu Kwankwaso da 'yan Kwankwasiyya a cikin jam'iyyar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng