"Idan Ban Yi ba Zan Yi Murabus": Amaechi Ya Fadi Abin da Zai Yi Idan Ya Zama Shugaban Kasa

"Idan Ban Yi ba Zan Yi Murabus": Amaechi Ya Fadi Abin da Zai Yi Idan Ya Zama Shugaban Kasa

  • Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya sha alwashin kawo karshen cin hanci da rashawa idan ya zama shugaban kasa
  • Amaechi ya bayyana cewa a cikin watan farko da zamansa shugaban kasa, zai batar da cin hanci da rashawa
  • Hakazalika ya nuna cewa ba zai dawo da tallafin man fetur ba idan ya samu damar hawa kan madafun kasar nan

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Tsohon ministan sufuri kuma ɗan takarar shugabancin ƙasa a zaɓen 2023, Rotimi Amaechi, ya bayyana matsayarsa kan yaki da cin hanci da rashawa.

Rotimi Amaechi ya ce zai kawar da cin hanci da rashawa a Najeriya cikin watan farko na shugabancinsa idan aka zaɓe shi, ko kuma ya yi murabus daga mukaminsa.

Rotimi Amaechi zai kawo karshen cin hanci
Rotimi Amaechi ya ce zai yaki cin hanci da rashawa Hoto: @ChibuikeAmaechi
Asali: Twitter

Rotimi Amaechi ya bayyana hakan ne yayin da yake jawabi a ranar Asabar a wata tattaunawa ta X Spaces wadda jaridar Tribune ta bibiya.

Kara karanta wannan

Amaechi: Tsohon ministan Buhari ya kalubalanci 'yan siyasar Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amaechi zai yaki cin hanci

Amaechi ya yi alkawarin amfani da kuɗaɗen da aka samu daga cire tallafin man fetur wajen ci gaban ƙasar nan idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa.

"Zan kawar da cin hanci da rashawa. Ku yarda da ni, cikin watan farko na zama a ofis, cin hanci zai shuɗe. Idan bai shuɗe ba, zan miƙa takardar murabus di na, na tafi. Ba wasa nake yi ba."

- Rotimi Amaechi

Amaechi ya soki yadda gwamnatin yanzu take tafiyar da kuɗaɗen tallafin man fetur da aka cire.

Ya yi zargin cewa wasu ‘yan kaɗan daga cikin jami’an gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohi ne kawai suke cin gajiyar kuɗin, waɗanda kuma yake zargin suna yin rayuwar facaka da kudi.

"Matsalar gwamnatin yanzu ita ce amfanin cire tallafin yana shiga aljihun mutum uku ko huɗu a matakin tarayya da gwamnonin jihohi. Kuma gwamnonin suna yin shagulgula a bakin teku, suna nishadi tare da ‘yan mata.”

Kara karanta wannan

ADC: Amaechi ya kada hantar Tinubu kan zaben 2027, ya fadi illar da zai yi masa

"Hakan ba zai faru da ni ba; zan kasance ina kula da gwamnati sosai. Da gaske nake, zan sa ido kan gwamnati."

- Rotimi Amaechi

Amaechi ya yi wa 'yan Najeriya alkawari
Amaechi ya sha alwashi kan cin hanci
Asali: Facebook

Matsayar Amaechi kan tallafin fetur

Ya kuma jaddada adawarsa ga dawo da tallafin man fetur, yana kiran hakan a matsayin abu mai cutarwa ga ƙasar nan.

"Zan sa ido kan gwamnati ta. Ba zan dawo da tallafi ba, wannan ba zai yiwu ba, domin halin tattalin arzikin Najeriya ba shi da kyau. Amma na kuma ce cire tallafin bai yi nasara ba. Kuɗin suna tafiya cikin aljihun mutane.”

- Rotimi Amaechi

A cewarsa, zai tabbatar da cewa amfanin cire tallafin ya koma hannu da aljihun ‘yan Najeriya, wanda idan hakan ta tabbata, zai rage talauci kuma ya ƙara wa mutane ƙarfin sayan abubuwa.

Tatsuniya ce kawai

Tukur Lawal ya shaidawa Legit Hausa cewa kalaman na Rotimi Amaechi, ba komai ba ne illa tatsuniya irin ta 'yan siyasa.

Kara karanta wannan

Davido: Mawakin Najeriya ya yi auren kece raini, ya kashe sama da Naira biliyan 5

"Soki burutsu ne kawai irin ne 'yan siyasa da suka saba yi. Shi kan shi ai ya san ba zai iya magance matsalar ba a cikin wannan lokacin."
"Ubangidansa ma da ya fi shi gaskiya bai iya magance matsalar ba a cikin shekara takwas."

- Tukur Lawal

Amaechi ya nesanta kansa da magudin zabe

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa bai taba yin magudin zabe ba.

Amaechi ya kalubalanci 'yan siyasa kan cewa idan akwai ya san ga taba yin magudin zabe, ya fito ya gayawa duniya.

Ya nuna cewa magudin zabe yana sa jami'an gwamnatoci kwashe kusaden jama'a domin aiwatar da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel