Amaechi: Tsohon Ministan Buhari Ya Kalubalanci 'Yan Siyasar Najeriya
- Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya nesanta kansa daga halin 'yan siyasa na yin magudi a lokacin zabe
- Rotimi Amaechi ya bayyana cewa ko kadan bai taba yin magudin zabe ba a tarihin siyasarsa
- Hakazalika ya sake nanata kudirinsa na yin shekara hudu kawai a kan mulki idan ya samu damar lashe zaben shugaban kasa a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya yi magana kan magudin zabe a Najeriya.
Rotimi Amaechi ya ce bai taɓa shiga harkar maguɗin zaɓe ba.

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wata tattaunawa a X Spaces wadda jaridar The Punch ta bibiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amaechi ya ce bai yi magudin zabe ba
Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya kalubalanci 'yan siyasa kan idan akwai wanda ya san ya taba magudin zabe, ya fito ya yi magana.
“Ina kalubalantar kowane ɗan siyasa, ko mai rai ko wanda ya riga mu gidan gaskiya, ya fito ya ce na taɓa shiga maguɗin zaɓe."
- Rotimi Amaechi
Ya yi zargin cewa mafi yawan maguɗin zaɓe yana sanya gwamnonin jihohi da karkatar da kuɗaɗen jama’a ta hannun hukumomin gwamnati, rahoton The Punch ya tabbatar.
Rotimi Amaechi ya yi alkawarin cewa ba zai taɓa shiga harkar maguɗin zaɓe ba, inda ya ce idan aka zaɓe shi shugaban ƙasa a 2027, burinsa zai kasance ne dakatar da aikata maguɗin zaɓe.
"Ina mai tabbatar muku cewa ba zan taɓa shiga kowanne irin maguɗin zaɓe ba, kuma ba zan yi ba. Abin da nake yi muku alkawari daga yanzu shi ne dakatar da maguɗi."
- Rotimi Amaechu
Ya ƙara da cewa zai nemi gafara ne kawai idan aka samu hujjar cewa ya aikata wani laifi.
“Ina kalubalantar duk wani ɗan Najeriya ya kawo hujja cewa na taɓa shiga maguɗin zaɓe, zan nemi afuwa akan hakan."
- Rotimi Amaechi

Source: Facebook
Amaechi na son ya yi wa'adi daya
A ranar 3 ga watan Yulin 2025, Amaechi ya bayyana cewa ya shirya zama shugaban ƙasa na wa’adin shekara huɗu kacal a 2027 idan ya samu tikitin tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar ADC.
Tsohon gwamnan na jihar Rivers ya ce ya shirya sauka bayan shekara huɗu a ofis domin ba da dama ga tsarin karba-karba.
"Yanzu dai, yadda Najeriya take, dole ne a kiyaye wannan yarjejeniyar wadda ke cewa Kudu shekaru takwas, Arewa shekaru takwas."
- Rotimi Amaechi
Amaechi ya shirya kayar da Tinubu a 2027
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufuri a gwamnatin marigayi, Muhammadu Buhari, Rotimi Amaechi, ya cika baki kan yin takara da Shugaba Bola Tinubu a zaben 2027.
Rotimi Amaechi ya bayyana cewa zai iya kayar da mai girma Bola Tinubu idan har ya samu tikitin takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC.
Tsohon ministan ya bayyana cewa ya san raunin shugaban kasan, saboda ida ya samu tikitin takarar ADC, zai iya doke shi.
Asali: Legit.ng

