Sanata Na Shirin Barin APC Watanni bayan Komawa, an Ji Yadda Lamarin Yake

Sanata Na Shirin Barin APC Watanni bayan Komawa, an Ji Yadda Lamarin Yake

  • Sanatan da ke wakiltar Delta ta Arewa a majalisar dattawa, ya yi magana kan jita-jitar da ke cewa zai tattara 'yan komatsansa daga APC
  • Ned Nwoko ya karyata jita-jitar da ake yadawa a kansa, inda ya nuna cewa bai da wani shiri na barin jam'iyya mai rinjaye a majalisa
  • 'Dan majalisar ya nuna kudirinsa na ci gaba da aiki tare da jam'iyyar APC wacce ya sauya sheka daga cikinta zuwa a farkon shekarar 2025

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Delta - Sanata Ned Nwoko mai wakiltar Delta ta Arewa a majalisar dattawa, ya yi magana kan batun ficewa daga APC.

Darakta janar na kamfen ɗin Ned Nwoko a 2019 kuma tsohon kwamishina, Hon. Leonard Esegbue ya bayyana cewa sanatan bai da shirin ficewa daga jam'iyyar APC.

Ned Nwoko ya musanta shirin barin APC
Sanata Ned Nwoko ya ce ba zai bar APC ba Hoto: Senator Prince Ned Nwoko
Asali: Facebook

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Leonard Esegbue ya bayyana cewa jita-jitar da ke cewa Nwoko zai fice daga jam’iyyar APC ƙarya ce.

Kara karanta wannan

APC ta yi wa Tinubu alkawari yayin da ta jaddada mubaya'a ga Ganduje a Kano

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Ned Nwoko ya musanta shirin barin APC

Ya bayyana cewa masu neman batawa sanatan suna ne ke yada jita-jitar ne gangan saboda jin zafin nasarar da yake samu a siyasa.

Ya tabbatar wa jama’ar Delta ta Arewa da dukkan ’yan Najeriya cewa babu wata gaskiya a cikin wannan jita-jita, rahoton PM News ya tabbatar.

Leonard Esegbue ya bayyana cewa Ned Nwoko ya kuduri aniyar yin aiki da APC, kuma yana da cikakken goyon baya ga jam’iyyar da kuma shirinta na gaba.

Ya jaddada cewa jita-jitar cewa Ned Nwoko yana tunanin barin jam’iyyar ba ta da tushe ko makama, illa kawai kokari ne daga wasu masu neman kawo rabuwar kai tsakaninsa da shugaban kasa, Bola Tinubu.

Ned Nwoko zai ci gaba da zama a APC
Sanata Ned Nwoko bai da shirin barin APC Hoto: Senator Prince Ned Nwoko
Asali: UGC

Darakta Janar din ya roƙi masu yaɗa irin waɗannan jita-jita su daina, su mayar da hankali kan ayyukan da za su amfani al’umma, yana mai nuna buƙatar ci gaba da tattaunawar siyasa mai amfani da kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Jigon APC ya gano dalili 1 da zai hana 'yan Arewa zabar Peter Obi a 2027

Ya kuma bayar da tabbacin cewa duk wata sanarwa da za ta fito dangane da harkokin siyasar Sanata Nwoko nan gaba, za a yi ta ne karkashin APC, wanda hakan na nuna sadaukarwarsa da amincinsa ga jam’iyyar.

Ned Nwoko zai ci gaba da zama a APC

A cewarsa, wannan bayani an bayar da shi ne domin fayyace matsayin siyasar Nwoko da kuma kawar da jita-jitar da ba ta da tushe.

Idan ba a manta ba dai, Ned Nwoko ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC a ranar 5 ga Fabrairu, 2025.

Sauya sheƙar tasa ta janyo ce-ce-ku-ce a kafafen yada labarai, inda abokansa, magoya bayansa da mazauna yankinsa suka yaba da matakin, suna kiran shi mafi dacewa a lokacin.

Sanata Nwoko na son a kirkiro sabuwar jiha

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Delta ta Arewa, Ned Nwoko, ya shirya ba Gwamna Sheriff Oborevwori mamaki.

Kara karanta wannan

APC ta yi watsi da kalaman El Rufai, ta fadi dalilin da zai sa Tinubu yin tazarce a 2027

Sanatan ya bayyana cewa gwamnan na Delta mamaki ne kan batun kirkiro jihar Anioma da yake son a yi.

Ya bayyana cewa gwamnan ya fito ya gaya masa cewa ba zai goyi bayan yunkurinsa na ganin an kirkiro sabuwar jihar ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

iiq_pixel