Shugabanin ADC a Jihohi Sun Shirya Tumbotsai, Za Su Jawo Matsala ga Tafiyar 2027

Shugabanin ADC a Jihohi Sun Shirya Tumbotsai, Za Su Jawo Matsala ga Tafiyar 2027

  • Shugabannin ADC a jihohi sun zargi David Mark da shirya juyin mulki a jam’iyya, suna cewa ana ƙoƙarin karɓe iko ba bisa ka’ida ba
  • Sun bukaci jama’a da hukumomin tsaro su hana yunkurin durƙusar da jam’iyyar, suna cewa hakan barazana ne ga dimokuraɗiyya a Najeriya
  • Lamarin na zuwa a lokacin da ADC ke kokarin hada kawunan 'yan adawa a yunkurin da ake yi na korar jam'iyyar APC daga gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT, Abuja – Rikicin da ke cikin jam’iyyar ADC ya ɗauki sabon salo a ranar Talata yayin da shugabannin jam’iyyar na jihohi suka barranta kansu ga hadakar adawa.

Sun bayyana cewa ba za su amince da jagorancin Sanata David Mark ba a kokarin kwace mulki daga APC a filin zabe.

Kara karanta wannan

Talaka bawan Allah: ADC ta fusata da Tinubu zai kashe N712bn a gyaran filin jirgin Legas

Shugaban riko na ADC, David Mark
Shugabannin ADC a jihohi sun yi watsi da jagorancin David Mark Hoto: 2027 ADC Coalition
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa wannan na kunshe a cikin sanarwa da shugaban ƙungiyar shugabannin jihohi, Elias Adokwu, da sakataren yaɗa labarai, Godwin Alaku, suka sa wa hannu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin sun bayyana jagorancin David Marka a matsayin ƙeta doka da kuma ƙoƙarin karya tsarin dimokuraɗiyya da ya kafa ADC da Najeriya.

Shugabannin jam'iyyar ADC sun fusata

The Cable ta wallafa cewa Shugabannin ADC na jihohi sun ce ba za su lamunci yunkurin hadakar adawa ba wanda suka bayyana a matsayin “dabarar juyin mulki."

Sun soki kawancen da ke ƙarƙashin David Mark da cewa yana ƙoƙarin kwace jam’iyyar ta hanyar cuɗanya da kulla yarjejeniyoyi a bayan fage.

A cewar sanarwar:

“Muna Allah wadai da wannan yunƙurin karɓe iko da karfin tsiya, wanda ba wai kawai ya sabawa dokokin dimokuraɗiyya ba ne, har ma ya zubar da ƙimarmu ta siyasa a matsayin al’umma.”

Sun bayyana ƙoƙarin kwace jam’iyyar a matsayin raini ga duka ‘yan Najeriya da suka sadaukar da kai wajen ginowa da kare dimokuraɗiyya.

Kara karanta wannan

2027: Bayan hukuncin SDP, ADC ta mika bukata ga El Rufa'i

Jam'iyyar ADC ta shiga matsala

Shugabannin sun zargi kawancen David Mark da yunƙurin karya tsarin dimokuraɗiyya domin cimma burinsu na kashin kai ta hanyar karɓar jam’iyya daga waje.

Sun jaddada cewa jam’iyyar ADC za ta ci gaba da kasancewa tsintsiya madaurinta ɗaya da ke bin tsarin doka.

'Yan hadakar adawa
Hadakar adawa ta samu matsala Hoto: ADC Coaltion 2027
Asali: Facebook

Sun yi gargaɗi da cewa:

“ADC ba a kasuwa take ba, ba za a sayar da ita ba."

Shugabannin jihohin ADC sun yi kira ga al’ummar Najeriya da kungiyoyin farar hula da su tashi tsaye wajen hana yunkurin danne dimokuraɗiyya.

Sannan suka bukaci hukumomin tsaro da su binciki wannan yunkurin da ke neman tayar da tarzoma da tabarbarewar jam’iyyar daga cikin gida.

ADC ta dura a kan gwamnatin Tinubu

A baya, mun wallafa cewa jam’iyyar adawa ta ADC ta caccaki shirin gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu na sake gyaran filin jirgin saman Murtala Muhammed da ke Legas.

Ta zargi gwamnati da rashin alkibla wajen kwasar kudin talaka da zummar yin aikin da ba zai amfani rayuwarsu ko fitar da su daga cikin mawuyacin halin da aka shiga ba.

A makon da ya gabata ne Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) ta amince da kashe Naira biliyan 712 domin aikin gyaran filin jirgin, wanda ya haɗa da saka na’urar CCTV da sauransu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.