Yunƙurin Tsige Gwamna daga Mulki bai Yi Nasara ba, Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Yi Hukunci

Yunƙurin Tsige Gwamna daga Mulki bai Yi Nasara ba, Kotun Ɗaukaka Ƙara Ta Yi Hukunci

  • Kotun ɗaukaka kara mai zama a Akure, babban birnin jihar Ondo ta kawo ƙarshen shari'ar da aka ƙalubalanci nasarar Gwamna Lucky Aiyedatiwa
  • A zaman yanke hukunci yau Alhamis, kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Aiyedatiwa na APC a zaɓen da ya gudana a watan Nuwamba, 2024
  • Wannan nasara da gwamnan ya samu ta biyo bayan hukuncin da kotun koli da kotun sauraron ƙorafe-ƙorafen zaɓen gwamna suka yanke a baya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akure, jihar Ondo - Gwamma Lucky Aiyedatiwa ya yi nasara a ƙarar da aka ƙalubalanci sakamakon a zaben gwamnan jihar Ondo.

Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Akure, babban birnin jihar Ondo, ta tabbatar da nasarar zaben Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jam’iyyar APC mai mulki.

Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa.
Kotun daukaka ƙara ta tabbatar da nasarar APC a zaben gwamnan Ondo na watan Nuwamba, 2024 Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Source: Facebook

Gwamna Aiyedatiwa ya kara yin nasara a kotu

Kara karanta wannan

Sanatocin Arewa sun yi tir da kisan mutane a Zamfara, an aika sako ga Tinubu

Channels tv ta ruwaito cewa kotun ta yanke hukuncin cewa Aiyedatiwa, ɗan takara a inuwar APC ne ya lashe zaben gwamnan Ondo da aka yi a ranar 16 ga Nuwamba, 2024

Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ce ta bayyana Aiyedatiwa a matsayin wanda ya yi nasara bayan da ya samu kuri’u 366,781 tare da lashe dukkan kananan hukumomi 18 na jihar Ondo.

Ya doke babban abokin hamayyarsa, ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar PDP, Agboola Ajayi.

Wannan hukuncin kotun daukaka kara ya biyo bayan nasarorin da Aiyedatiwa ya samu a kotu a baya, cewar rahoton The Nation.

Wane hukunci kotun zaɓen Ondo ta yanke?

A ranar 4 ga Yuni, 2025, Kotun Sauraron Kararrakin Zaben Gwamnan Jihar Ondo ta yi watsi da korafe-korafe da dama da ke kalubalantar nasararsa.

Daga cikin ƙararrakin da kotun zaɓen ta kora har da na Agboola Ajayi wanda ya yi zargin cewa an tafka maguɗi a zaɓen gwamnan Ondo da aka kammala.

Kotun, karkashin jagorancin Mai Shari’a Benson Ogubu, ta kuma yi watsi da karar da jam’iyyun SDP, ADC, APM da AA suka shigar, tana mai karkare wa da cewa nasarar Aiyedatiwa ta tabbata bisa doka.

Kara karanta wannan

Gwamna Uba Sani ya ari bakin gwamnoni kan tazarcen Tinubu a 2027

Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa.
Gwamnan Ondo ya ƙara samun nasara a kotun ɗaukaka ƙara Hoto: Hon. Lucky Orimisan Aiyedatiwa
Source: Twitter

Abin da ya faru a Kotun Kolin Najeriya

Kafin hakan, a ranar 11 ga Maris, 2025, Kotun Koli ta kasa ta yi watsi da wata kara daban da Ajayi ya shigar yana kalubalantar sahihancin takarar Aiyedatiwa.

Kotun koli ta yanke hukunci cewa Ajayi ya shigar da karar ne bayan lokacin da doka ta tanada.

Sannan shi ba ɗan APC ba ne, don haka bai da hurumin shigar da kara kan harkokin cikin jam’iyyar, musamman batun cancantar dan takarar mataimakin gwamna da Aiyedatiwa ya zaba.

Gwamnan Ondo ya aika sako ga ƴan adawa

A wani rahoton, mun kawo maku cewa gwamnan Ondo ya buƙaci Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran ƴan adawa su marawa Shugaba Tinubu baya ya yi tazarce a 2027.

Lucky Aiyedatiwa ya jaddada da cewa tuni suka fara aiki a Kudu maso Yamma don tabbatar da ɗorewar mulkin Renewed Hope zuwa wa'adi na biyu a zaɓe mai zuwa.

A cewarsa, duba da aikin da mai girma Tinubu ya ɗauko na gyara ƙasar nan, kamata ya yi kowa ya marasa masa baya don cimma burinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: