Hadimin Tinubu Ya Kare Shugaban Kasa, Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Ake Adawa da Shi

Hadimin Tinubu Ya Kare Shugaban Kasa, Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Ake Adawa da Shi

  • Cif Bayo Onanuga ya fito ya yi magana kan zarge-zargen da ake jifar gwamnatin Mai girma Bola Tinubu da su
  • Hadimin shugaban kasan ya kare ubangidansa kan batun cewa yana nuna wariya ga yankin Arewacin Najeriya
  • Ya bayyana cewa wasu masu adawa da shugaban kasan suna yi ne kawai don ya fito daga shiyyar Kudancin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Bayo Onanuga, mai ba shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai da ya yi magana kan masu adawa da Bola Tinubu.

Bayo Onanuga ya yi zargin cewa wasu mutane na adawa da Shugaba Bola Tinubu ne kawai saboda ya fito daga yankin Kudu.

Bayo Onanuga ya kare Shugaba Tinubu
Bayo Onanuga ya yi maganganu kan Tinubu Hoto: @aonanuga1956
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce hadimin shugaban kasan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da aka yi da shi a Trust Radio.

Kara karanta wannan

'A taimaka masa kamar Buhari': An roƙawa Tinubu alfarma wurin ƴan Arewa a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Tinubu bai ware 'yan Arewa ba' - Bayo Onanuga

Onanuga ya karyata zargin nuna wariya da nuna bambanci kan yankin Arewa yana mai cewa ƙarya ce ta siyasa da aka ƙulla da gangan.

Hadimin shugaban kasan ya bayyana cewa ba daidai ba ne a ce Arewa ba ta samu isassun mukamai ko ayyukan raya ƙasa a ƙarƙashin mulkin Tinubu ba.

Ya siffanta koke-koken da kungiyar ACF ke yi dangane da wariya a mukamai a matsayin wata dabara ce ta ɓoye da nufin adawa da shugaban kasa saboda ya fito daga Kudu.

Hadimin shugaban ƙasan ya bukaci ‘yan siyasar Arewa su jira lokacinsu, kamar yadda Kudancin Najeriya ya yi haƙuri ya yi jira a lokacin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari.

"Wannan shugaban kasa ɗan Najeriya ne. Yana da ikon yin wa’adin mulki biyu kamar yadda Buhari ya yi. Kada mu sadaukar da ƙasar nan saboda son zuciyar wasu."

Kara karanta wannan

'Yadda Tinubu ya ɗauko gagarumin aiki tun na zamanin Shagari saboda ƙaunar Arewa'

- Bayo Onanuga

An kalubalanci masu sukar shugaba Tinubu

Game da zargin cewa an fi bai wa mutanen Kudu maso Yamma mukamai, Onanuga ya kalubalanci masu sukar gwamnatin da su fito da takamaiman kididdiga maimakon su dogara da surutun jama’a da ba su da tushe.

Haka kuma, ya musanta labaran da ke cewa an bar Arewa babu abubuwan more rayuwa, yana mai cewa gwamnatin Tinubu ta gaji dimbin ayyuka da ba a kammala ba ko kuma aka watsar da su.

Bayo Onanuga ya yabi Shugaba Tinubu
Onanuga ya ce Tinubu bai ware 'yan Arewa ba Hoto: @DOlusegun
Asali: Facebook
"Ya kamata a duba kididdiga da kyau. Wannan duk wata dabara ce ta siyasa da ake yi don bata sunan shugaban kasa. Akwai tituna da suka lalace a sassan ƙasar nan baki ɗaya, ba a Arewa kawai ba."

- Bayo Onanuga

Onanuga ya kuma yabi shugaban kasan kan matakan da ya dauka wajen samar da tsaro.

Minista ya ce Tinubu ya cika alkawura

A wani labarin kuma, kun ji cewa Ministan yada labarai da wayar da kan jama'a, Mohammed Idris, ya yi magana kan alkawuran da Shugaba Tinubu ya daukarwa yankin Arewa.

Kara karanta wannan

"Lokaci ya yi" Gwamnatin Tinubu ta yiwa ƴan bindiga 'tayi' a Arewacin Najeriya

Ministan ya bayyana cewa shugaban kasan ya cika alkawuran da ya daukarwa Arewa kafin zaben shekarar 2023.

Ya yi nuni sa cewa Shugaba Tinubu ya kuma dauko 'yan Arewa ya ba su mukamai masu gwabi a cikin gwamnatinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng