2027: Manyan Arewa Sun Rabu 2, Wasu na Sukar Tinubu Wasu na Goyon Baya

2027: Manyan Arewa Sun Rabu 2, Wasu na Sukar Tinubu Wasu na Goyon Baya

  • Wasu shugabannin Arewa sun ce gwamnatin Bola Tinubu na kokari, wasu kuma sun ce an yi watsi da yankin wajen rabon mukamai da ayyuka
  • Taron kwanaki biyu a Arewa House, Kaduna, ya hada manyan shugabanni, ministoci, sarakuna, da jama’a daga jihohin Arewa 19
  • Tsohon gwamnan Neja, Babangida Aliyu, da ACF sun koka da talauci, rashin tsaro da kuma yawan yara marasa zuwa makaranta a yankin Arewa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Sabani ya kunno kai a tsakanin shugabannin Arewa dangane da yadda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke tafiyar da al’amuran kasar.

A wani babban taro a Arewa House da ke Kaduna, an bayyana ra’ayoyi game da yadda ake kallon gwamnatin Tinubu a yankin Arewa.

Kwankwaso ya zargi Tinubu da nuna wariya
Kwankwaso ya zargi Tinubu da nuna wariya. Hoto: Bayo Onanuga|Saifullahi Hassan|Ismaila Uba Misilli
Source: Facebook

Punch ta fitar da rahoto kan yadda wasu ke ganin an yi watsi da Arewa, yayin da wasu ke ganin ana kokari ta hanyar nada ‘yan Arewa a mukamai da kuma yin muhimman ayyuka.

Kara karanta wannan

2027: Kungiyar ATT ta samo mafita ga Arewa kan tazarcen Shugaba Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron da ake yi da 'yan Arewa a Kaduna

Taron da gidauniyar Sir Ahmadu Bello ta shirya ya tara manyan kusoshin siyasa da al’umma daga jihohin Arewa guda 19 domin duba alkawuran da gwamnatin Tinubu ta yi.

Shugabannin da suka halarci taron sun hada da sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, da wasu ministoci da sauran manyan jami'an gwamnatin Tinubu.

Rabiu Kwankwaso ya ce an ware Arewa

Tsohon dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana a makon da ya gabata cewa gwamnatin Tinubu tana watsi da Arewa.

A cewarsa, duk da gudunmawar Arewa a zaben 2023, an fi karkata ayyuka zuwa Kudancin Najeriya, inda Shugaba Tinubu ya fito.

Akume ya ce ana damawa da Arewa

A jawabin da ya yi a Kaduna a madadin Shugaba Tinubu, Sanata Akume ya ce gwamnati na kokarin cika alkawurran da ta dauka karkashin shirin "Renewed Hope".

Kara karanta wannan

Hako fetur a Arewa: Kamfanin NNPCL ya tono rijiyoyin mai 4 a Kolmani

Ya ce cire tallafin mai na daga cikin matakan da suka taimaka wajen ceton tattalin arzikin kasa daga durkushewa.

Gwamna Inuwa ya yaba wa Tinubu

Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya na jihar Gombe, ya ce Arewa na da hakkin tambayar gwamnati abin da ta yi da goyon bayan da ta bata kuri'u a zaben 2023.

Duk da haka, gwamnan ya ce Bola Tinubu ya cika alkawuran da ya yi wa Arewa, inda ya buga misali da cigaba da hako mai a Kolmani da inganta tsaro.

Shugaban gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya
Shugaban gwamnonin Arewa, Inuwa Yahaya. Hoto: Ismaila Uba Misilli
Source: UGC

Korafin kungiyar ACF da Babangida Aliyu

Tsohon gwamnan jihar Neja, Dr Muazu Babangida Aliyu, ya caccaki shugabannin Arewa da suka zuba ido yayin da yankin ke durkushewa.

Ya ce matsalolin kamar rashin tsaro, talauci da yara marasa zuwa makaranta sun yi kamari a yankin, kuma lokaci ya yi da za a nemi mafita.

Daily Trust ta wallafa cewa shugaban Arewa Consultative Forum (ACF), Alhaji Bashir Dalhatu, ya zargi gwamnatin Tinubu da nuna halin ko in kula da matsalolin Arewa.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya fara gwangwaje jihohin Arewa da titunan jiragen kasa

Legit ta tattauna da Habu Gombe

Wani matashi a jihar Gombe da ke shiga harkokin siyasa ya bayyana wa Legit cewa ba abin mamaki ba ne idan gwamnoni suka goyi bayan Tinubu.

Habu Gombe ya bayyana cewa:

"Dole talakawa za su ji cewa gwamnatin Tinubu ba ta tafiya da su. Ya cire tallafin mai amma gwamnoni ne kawai suke cin riba sosai ba talakawa ba.
"Ya kamata a ce talakawa sun ga sauyi a kasa."

An nemi Kwankwaso ya ba Tinubu hakuri

A wani rahoton, kun ji cewa ministan ayyuka na kasa, David Umahi ya ce zargin da Rabiu Kwankwaso ya yi na cewa an ware Arewa ba gaskiya ba ne.

David Umahi ya lissafo wasu ayyuka da ya ce shugaba Bola Tinubu ya yi su a Arewacin Najeriya cikin shekara biyu.

Ministan ya bukaci Sanata Kwankwaso da ya ba shugaban kasa hakuri a kan zargin da ya yi kuma ya janye kalaman shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng