Asirin Wadanda Suka Dakatar da El Rufa'i Ya Tonu, SDP Ta Ce Sun Ci Kudin Jam'iyya
- A jiya Litinin tsagin SDP ya sanar da dakatar da Nasir El-Rufai daga jam’iyya tsawon shekara 30 bisa zargin karya da cin amana
- Reshen jam’iyyar na jihar Kaduna ya nesanta kansa daga wannan mataki, yana mai cewa har yanzu El-Rufai dan jam’iyya ne
- Rahoto ya nuna cewa SDP a Kaduna ta zargi wasu da aka dakatar daga jam’iyyar da kokarin bata sunan El-Rufa'i da kawo rikici
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kaduna - Jam’iyyar SDP ta shiga rudani sakamakon matakin da Kwamitin Gudanarwar Jam’iyyar na Kasa ya dauka na dakatar tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.
Kwamitin ya bayyana cewa El-Rufai ya yi karya wajen ikirarin zama dan jam’iyyar, cin amana da kuma kokarin karkatar da tafiyar jam’iyyar ba bisa ka’ida ba.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa reshen jam’iyyar a Kaduna ya fito karara ya nesanta kansa daga wannan mataki, inda ya ya ce har yanzu El-Rufai na cikin manyan ’yan jam’iyyar a Arewa ta Yamma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zargin da jam'iyyar SDP ta yi wa El-Rufa'i
Tsagin SDP ne ya sanar da hukuncin a ranar Litinin, inda ya bayyana cewa El-Rufai ya aikata laifuffuka da suka hada da cin amanar jam’iyya da karya kan kasancewarsa dan jam’iyyar.
Tsohon gwamnan ya sauya sheka daga APC zuwa SDP, yana mai cewa akwai sabani da ba za a iya sulhunta wa ba tsakaninsa da APC.
Dakatar da El-Rufa'i: Zargin cin kudin SDP
Sai dai, reshen jam’iyyar SDP na jihar Kaduna ya musanta labarin, yana mai cewa babu wani hukunci da jam’iyyar ta yanke na korar El-Rufai ko hana shi hulda da jam’iyyar.
Sakataren yada labarai na jam’iyyar a jihar, Darius Kurah ne ya bayyana hakan a wata hira da ya yi da manema labarai.
Ya ce wadanda suka yi wannan furuci ba su da hurumin yanke irin wannan hukunci, domin tun da farko an dakatar da su bisa zargin karkatar da kudin jam’iyya da wasu laifuffuka.

Source: Facebook
'Har yanzu El-Rufai dan jam’iyya ne,' SDP
Sakataren ya ce wadanda aka dakatar din ne ke kokarin bata sunan El-Rufai ta hanyar tallafa wa wasu don yada labaran karya da ke kokarin alakanta korarsu da tasirin El-Rufai.
Kurah ya ce:
“Ba mu da wata hujja ko bayani daga jam’iyyar da ke nuna cewa an kori Malam Nasir El-Rufai daga jam’iyya."
A karshe, Kurah ya jaddada cewa El-Rufai na da daraja a jam’iyyar SDP musamman a yankin Arewa maso Yamma, kuma bai aikata wani laifi da ya cancanci korar sa daga jam’iyya ba.
An ce Atiku ne jagoran siyasar Arewa
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo ya ayyana Atiku Abubakar a matsayin jagoran siyasar Arewa.
Dankwambo ya bayyana haka ne yayin wani taron jam'iyyar PDP da aka gudanar a jihar Gombe a ranar Lahadi.
Sanatan ya ce ko a wace jam'iyya Atiku ya ke bayan barin PDP, zai cigaba da zama jagoransu a harkokin siyasar Arewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

