Matsala Ta Tunkaro Tinubu a APC, Tsofaffin Mambobin ANPP Sun Aika da Sakon Gargadi
- Tsofaffin mambobin jam'iyyar ANPP sun nuna rashin gamsuwarsu kan yadda ake nuna musu wariya a cikin APC
- Mambobin sun aika da sakon gargadi ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan ci gaba da zamansu a cikin APC
- Sun bayyana cewa idan ana so su ci gaba da kasancewa a APC, dole ne a ki taba kujerar mataimakin shugaban kasa daga bangarensu
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Tsofaffin mambobin jam’iyyar ANPP sun aika da sakon gargadi ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Tsofaffin mambobin na ANPP sun yi gargadin cewa za su fice daga jam’iyyar APC idan mukamin mataimakin shugaban kasa bai ci gaba da kasancewa a hannun ɓangaren su ba.

Asali: Facebook
Bangaren na ANPP sun bayyana matsayarsu ne yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin, 28 ga watan Yulin 2025, cewar rahoton jaridar The Punch.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana nuna wariya ga tsofaffin 'yan ANPP?
Yayin da suke jawabi ga ’yan jarida, mambobin karkashin kungiyar tsofaffin mambobin ANPP, sun bukaci da a basu dama da wakilci nagari a cikin gwamnatin APC, rahoton Tribune ya tabbatar.
Sun zargi ɓangarorin da suka fito daga CPC da ACN da nuna musu wariya tun bayan haɗewar da aka yi don kafa gwamnatin APC a shekarar 2015.
Yayin da yake karanta sanarwar bayan taro, jagoran kungiyar na kasa, Farfesa Vitalis Ajumbe, ya bayyana cewa dole ne mukamin mataimakin shugaban kasa ya kasance a hannun ɓangaren ANPP.
"Tikitin da kake amfani da shi zai shiga hadari idan ka zaɓi wani daga wajen ɓangaren ANPP a matsayin mataimakin shugaban kasa."
"Wannan kujera ta mataimakin shugaban kasa tana da matuƙar muhimmanci ga ɓangaren ANPP wanda shi ne na biyu mafi girma wajen kafa jam’iyyar APC.”
- Farfesa Vitalis Ajumbe
Farfesa Vitalis Ajumbe ya ƙara da cewa ɓangaren su ya fuskanci wariya a lokacin mulkin marigayi Shugaba Muhammadu Buhari, duk da cewa sun taka gagarumar rawa a haɗakar da ta samar da APC.
"Marigayi Muhammadu Buhari ya yi watsi da ANPP inda ya fara siyasarsa, kuma inda ya samu tikitin takarar shugaban ƙasa har sau biyu. Hakan bai dace ba. Ya dauke mu tamkar ba mu da amfani."
- Farfesa Vitalis Ajumbe

Asali: Facebook
Tinubu ya dora daga inda Buhari ya tsaya
Ƙungiyar ta bayyana takaicinta kan yadda duk da cewa ɓangaren ANPP ya samar da jiga-jigai irin su Kashim Shettima, Babagana Zulum da Mai Mala Buni, da kuma manyan sanatoci da tsofaffin gwamnoni, amma ba a ba su guraben mukamai a gwamnatin Tinubu ba.
"Lokacin da aka zabi Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kasa, mun yi tsammanin zai kawo sauyi. Amma abin takaici, lamarin ya ƙara tabarbarewa a karkashin ‘Renewed Hope Agenda’ dinsa."
- Farfesa Vitalis Ajumbe
Ƙungiyar ta bayyana shirin ta na fara gudanar da taron tuntuɓar jama'a a jihohi da yankuna daban-daban a makonni masu zuwa don sanar da mambobinta matakin da za su dauka na gaba.
Amaechi ya sha alwashi kan Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi, ya sha alwashin kan mai girma Bola Ahmed Tinubu.
Rotimi Amaechi ya sha alwashin kawo cikas kan tazarcen Shugaba Tinubu a zaben shekarar 2027 da ake tunkara.
Hakazalika ya yi kira ga mutanen jihar Rivers da su fito su yi rajista da jam'iyyar ADC ta 'yan hadaka.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng