Fayose: Tsohon Gwamnan PDP Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Fadi Dalilin da Zai Sa Tinubu Ya Zarce

Fayose: Tsohon Gwamnan PDP Ya Yi Karatun Ta Natsu, Ya Fadi Dalilin da Zai Sa Tinubu Ya Zarce

  • Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya yi magana kan tazarcen mai girma Bola Tinubu a zaben 2027
  • Ayodele Fayose ya bayyana cewa Shugaba Tinubu zai lashe zabe a karo na biyu a shekarar 2027 duk da hadakar da aka kafa
  • Tsohon gwamnan ya nuna cewa ba zai yaudari kansa ba, domin a bayyane take cewa Tinubu zai yi nasara kan 'yan adawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ondo - Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana dalilan da suka sa yake da tabbacin cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sake lashe zaɓe a 2027.

Fayose, wanda jigo ne a jam’iyyar PDP, ya ce haɗakar da wasu jagororin ‘yan adawa ke yi a ƙasar nan ba za ta iya hana Tinubu sake lashe zaɓe ba.

Kara karanta wannan

2027: Gwamnan APC ya fadi shirin da suke yi kan hadakar 'yan adawa

Fayose ya hango tazarcen Tinubu a 2027
Fayose ya ce Tinubu zai tazarce a 2027 Hoto: Ayo Fayose, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Ya bayyana hakan ne a cikin wata hira da aka watsa a jiya a tashar FM ta Adaba 88.9 da ke Akure, babban birnin jihar Ondo, wacce jaridar The Nation ta saurara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Fayose ya ce Tinubu zai yi tazarce?

Tsohon gwamnan ya ce ba zai yaudari kansa ba domin ya san cewa Shugaba Tinubu ne zai lashe zabe a 2027.

"Ba na yaudarar kaina. Shugaba Tinubu zai ci zaɓe a 2027. Ko da yake ba ni da rajista a jam’iyyarsa (APC), amma zai lashe zaɓe kuma a sake zaɓarsa. Idan ka tuna, a 2023, jam’iyyarsa ma ba ta mara masa baya sosai ba."
"Wadanda suka ki goyon bayansa a wancan lokacin sun fito da abubuwa iri-iri domin hana shi. Ka tuna abin da tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Godwin Emefiele, ya aikata kan kudinmu domin hana shi samun nasara."
"Ko marigayi Shugaba Muhammadu Buhari ma bai tsaya masa ba, amma duk da haka ya ci zaɓe. Saboda Tinubu yana da fahimta kan siyasa da yadda ake tafiyar da ita."

Kara karanta wannan

Benue: Jam'iyyar ADC ta fayyace alakar da ke tsakaninta da Gwamna Alia

"Zai sake cin zaɓe, zan iya yin gardama da kowa. Sai waɗanda suka haɗu suna kiran kansu hadaka su ne za su iya doke shi? A’a, ba zan yaudari kaina ba."

- Ayodele Fayose

Fayose ya yabi iya siyasar Tinubu
Fayose ya hango nasarar Tinubu a 2027 Hoto: @DOlusegun
Asali: Twitter

Fayose zai ci gaba da zama a PDP

Fayose ya jaddada cewa yana nan daram a cikin jam’iyyar PDP kuma ba zai fice daga cikinta zuwa APC ba duk kuwa da matsaloli da rikice-rikicen da take fama da su.

"Don haka, ba zan sauya sheƙa ba. Ba zan koma APC ba. Idan iyalanka na cikin rikici, za ka gudu ka bar su? A’a. Zai fi kyau na zauna a ciki na yi gwagwarmaya har zuwa lokacin zaɓe.”

- Ayodele Fayose

Bwala ya magantu kam lafiyar Shugaba Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa hadimin shugaban kasa, Daniel Bwala, ya yi magana kan lafiyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Daniel Bwala ya bayyana cewa Shugaba Tinubu yana da cikakkiyar lafiya fiye da ta sauran shugabannin kasashen da suka ci gaba.

Hakazalika, ya bayyana cewa shugaban kasan ya cimma nasarori masu yawa a gwamnatinsa a cikin shekara biyu da ya kwashe a kan mulki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng