Benue: Jam'iyyar ADC Ta Fayyace Alakar da Ke Tsakaninta da Gwamna Alia

Benue: Jam'iyyar ADC Ta Fayyace Alakar da Ke Tsakaninta da Gwamna Alia

  • Jam'iyyar ADC reshen jihar Benue ta fito ta yi magana kan maganganun da ke cewa Gwamna Hyacinth Alia ne ke daukar nauyinta
  • ADC ta bayyana cewa ko kadan babu kamshin gaskiya a cikin wadannan jita-jitar da ake yadawa
  • Ta yi zargin cewa makiyanta ne ke yada labaran na karya domin cimma wata manufa ta su mara kyau

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Jam'iyyar ADC reshen jihar Benie ta karyata jita-jitar da ke cewa Gwamna Hyacinth Alia ne ke daukar nauyinta domin ya samu wurin tsayawa takara a zaben 2027.

Jam’iyyar ADC ta dora alhakin yayata wannan jita-jita kan abokan gaba da ke kokarin bata sunanta da kuma rudar da jama’a gabanin lokacin zabe.

ADC ta yi magana kan Gwamna Alia
ADC ta ce ba ta da wata alaka da Gwamna Alia Hoto: Rev. Hyacinth Iormem Alia
Source: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan bayanin na kunshe ne a cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na kwamitin gudanarwa na ADC a jihar Benue, Stevie Ayua, ya fitar a karshen mako birnin Makurdi, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Ana fargabar El Rufai, Peter Obi na iya ficewa daga hadaka saboda burin Atiku

A cewar Steve Ayua, bayan kaddamar da jam’iyyar ADC a Benue a ranar 10 ga Yuli, 2025, ta fara aiki da gaggawa wajen rajistar mambobi daga sassa daban-daban na jihar wadanda ke da sha’awar shiga cikinta.

ADC ta nesanta kanta da Gwamna Alia

Ya bayyana cewa dukkan ayyukan da jam’iyyar ke gudanarwa ana daukar nauyinsu ne ta hanyar gudummawar ‘yan jam’iyya da masu kishin jam’iyyar, ba daga wani waje ko daga Gwamna Alia ba kamar yadda masu ƙiyaya da ita ke yadawa.

"Dukkan ayyukan jam’iyyar ADC zuwa yanzu, tun daga bikin ƙaddamarwa a matakin jiha, wayar da kai, taron gangami, rajistar mambobi da kaddamar da rassan kananan hukumomi."
"Ana gudanar da su ne ta hanyar gudummawar da mambobi da shugabanni masu kishin jam’iyya ke bayarwa ba tare da wani taimako daga wajen jam’iyya ba, musamman daga Gwamna Alia."
"Muna alfahari da bayyana cewa gudanar da harkokin kuɗi da na siyasa a jam’iyyarmu muna yi ne da kanmu, kuma babu wata alaka da wasu daga waje, musamman daga Gwamna Alia ko gwamnatin jihar Benue."
"Ba mu da kuma ba za mu karɓi wani tallafi daga gwamnan jihar Benue ko wani wanda ba mambanmu ba domin tafiyar da jam’iyya ko ayyukanta."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Abba ta dura kan bangaren lafiya, za a gyara asibitoci sama da 200 a faɗin Kano

"Wannan 'yancin kan da muke da shi ke bamu damar kare mutuncinmu da kuma jajircewarmu ga jama’ar jihar Benue ba tare da wata tangarda ba."
"Saboda haka, jam’iyyar ADC reshen Jihar Benue na so ta fayyace cewa ba ta da wata alaka ko dangantaka da gwamna mai ci na jihar Benue, Rev. Fr. Hyacinth Alia na jam’iyyar APC, ko kuma gwamnatinsa."

- Steve Ayua

ADC ta magantu kan dan takararta a 2027

A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta yi magana kan dan takarar da ta fi ba fifiko a cikin masu neman kujerar shugaban kasa.

Sakataren ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa jam'iyyar ba ta da wani dan takara da ta fi fifitawa.

Ya bayyana cewa a halin yanzu ba su fara tattaunawa kan wanda za su ba tikitin jam'iyyar ba domin zaben 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng