2027: ADC Ta Raba Gardama kan Dan Takarar Shugaban Kasan da Take Goyon Baya

2027: ADC Ta Raba Gardama kan Dan Takarar Shugaban Kasan da Take Goyon Baya

  • Jam'iyyar hadaka watau ADC ta fito ta yi magana kan dan takarar da take goyon baya a zaben shugaban kasa na shekarar 2027
  • Sakataren ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya bayyana cewa babu dan takarar da suka fi daga cikin masu son tikitin jam'iyyar
  • Bolaji Abdullahi ya nuna a halin yanzu ba su zo kan batun wanda zai zamar musu dan takarar shugaban kasa ba a 2027

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Mukaddashin sakataren jam’iyyar ADC na kasa, Bolaji Abdullahi, ya yi magana kan batun dan takarar da suka fi so.

Bolaji Abdullahi ya ce ba a gina jam’iyyar don cika burin wani mutum ɗaya ba.

ADc ta yi magana kan dan takararta a 2027
ADC ba ta da dan takarar da take goyon baya Hoto: @atiku, @PeterObi, @chibuikeAmaechi
Source: Facebook

Bolaji Abdullahi ya bayyana haka ne a ranar Asabar a birnin Abuja, yayin taro na uku na ƙungiyar Northern Political Consultative Group (NPCG), cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa gwamnonin PDP da APC ba su sauya sheƙa zuwa jam'iyyar ADC ba'

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

ADC ba ta fara batun fitar da dan takara ba

Ya bayyana cewa jam’iyyar ADC ba ta shiga wata tattaunawa ba kan wanda zai zama ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar a zaɓen 2027 ba.

"Ba mu da wani ɗan takara da muke goyon baya. Babu wata tattaunawa da ake yi a yanzu.”
"Babu wanda ya taɓa kawo batun wanda zai zama ɗan takarar jam’iyya a 2027. Muna ganin lokaci bai yi ba. Abin da muke maida hankali a kai yanzu shi ne gina jam’iyya mai ƙarfi wadda za ta iya cika abubuwan da muka sa a gaba."

- Bolaji Abdullahi

ADC za ta kawo sabon tsari

Tsohon ministan ya ƙara da cewa jam’iyyar ADC na mai da hankali kan samar da sabon tsarin siyasa wanda ke fifita muradun ƙasa fiye da son zuciyar wani mutum.

"Ka ga, tsarin da muka tanada don gina jam’iyyar na tabbatar da cewa jam’iyyar ba za ta taƙaita a kan wani mutum ɗaya ba.”

Kara karanta wannan

Ana fargabar El Rufai, Peter Obi na iya ficewa daga hadaka saboda burin Atiku

"Kuma kamar yadda na jaddada sau da dama, ba a kafa jam’iyyar ADC don biyan burin kowa ba. ADC jam’iyya ce da ke da nufin kawo sabuwar hanya a siyasar Najeriya. Ba mu da wani tsari ko shiri da aka riga aka tanada.”

- Bolaji Abdullahi

ADC ta tabo batun yin takara a 2027
ADC ba ta goyon bayan wani dan takara don fafatawa da Tinubu Hoto: @BolajiADC
Source: Facebook

Game da kokarin jawo gwamnoni masu ci su shiga jam’iyyar, Bolaji Abdullahi ya ce jam’iyyar ADC a buɗe take ga kowa, sai dai ya lura da cewa gwamnoni da dama na fuskantar matsin lamba ka da su shigo, rahoton Tribune ya tabbatar.

Ya ce babu gwamna mai ci da zai so ya sauya sheka saboda irin kallon hadarin kajin da ake yi musu.

Tinubu ya yi wa 'yan hadakar ADC shagube

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya taso 'yan hadakar jam'iyyar ADC a gaba.

Mai girma Bola Tinubu ya yi musu shagube inda ya bayyana su a matsayin hadakar rudaddun 'yan siyasa.

Shugaban kasan ya yi kira ga sauran 'yan adawa da su shigo cikin APC domin kofofin jam'iyyar a bude suke wajen tarbar baki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng