Wata Sabuwa: An Gano Abin da Ya Hana Atiku Shiga ADC bayan Ya Baro Jam'iyyar PDP

Wata Sabuwa: An Gano Abin da Ya Hana Atiku Shiga ADC bayan Ya Baro Jam'iyyar PDP

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar na shirin zuwa da kansa ya karbi katin zaman dan jam'iyyar haɗaka ADC a hukumance
  • Wata majiya ta kusa da Atiku ta ce Wazirin Adamawa na son karɓar kati da kansa shiyasa aka samu jinkirin sauya shekarsa zuwa ADC
  • Ya ce Atiku ya dawo Najeriya domin halartar jana'izar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, kuma tuni ya sake sa ƙafa ya bar ƙasar nan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Adamawa - Rahotanni sun tabbatar da cewa har yanzu tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, bai kammala shiga jam’iyyar haɗaka ADC a hukumance ba.

Wata majiya ta kusa da Atiku ta ce har yanzu bai shiga ADC ba bayan sanar da ficewa daga jam'iyyar PDP a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Taron APC: Tinubu ya shiga tsaka mai wuya game da zakulo magajin Ganduje

Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar.
Abin da ya jawo jinkiri a shirin Atiku na shiga ADC a hukumance Hoto: @Atiku
Source: Twitter

Majiyar ta bayyana cewa an samu jinkiri ne saboda Atiku yana shirin zuwa mazaɓarsa da kansa ya yanki katin zama ɗan ADC ba ta hannun wakili ba, in ji Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya hana Atiku zuwa wanke gashi a Kogi

Da yake magana a daren Litinin a Abuja, majiyar ta bayyana cewa tafiye-tafiyen Atiku na baya-bayan nan ne suka janyo jinkirin.

“Ya dawo Najeriya ne domin jana’izar marigayi tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a Daura, daga wata tafiyar kasuwanci da ya yi zuwa ƙasashen waje.
"Daga Daura kuma ya koma ƙasar waje domin hutun mako biyu da ya tsara,” in ji majiyar.

Yasuhe Atiku zai yanki katin jam'iyyar ADC?

Ta ƙara da cewa sauya sheƙa zuwa sabuwar jami'iyya musamman ga manyan mutane kamar Atiku, tana buƙatar mutum ya bayyana da kansa a hukumance.

“Ga mutum mai ƙima da daraja irinta Atiku Abubakar, mutane za su so ganinsa ya fito fili kowa na gani ya karɓi katin ADC tare da cika duk wasu sharuɗɗa.

Kara karanta wannan

"An yi abin kunya," ADC ta tona abin da gwamnatin Tinubu ta yi a rasuwar Buhari

"Da zarar ya dawo daga hutunsa, wannan na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ake sa ran zai fara yi,” in ji majiyar.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar.
Atiku zai je ya karɓi katin ADC da kansa a Adamuwa Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Atiku ya gama shirin shiga ADC a hukumance

Ta kuma bayyana cewa Atiku ya fahimci muhimmancin wannan mataki da tasirinsa a siyasa, musamman yayin da ake shirin tunkarar zaɓen 2027, rahoton Daily Post.

Da aka tambaye shi kan rashin shiga ADC, majiyar ta ce ana shirin gudanar da rajistar ne a wani lokaci da zai fi jawo hankalin kafafen yaɗa labarai da kuma tasiri a siyasa.

Duk da cewa ba a tabbatar da takamaiman ranar ba, majiyar ta jaddada cewa shigowar Atiku cikin ADC na tafe nan ba da jimawa ba, kuma hakan zai zama sabon babi mai muhimmanci a siyasar ‘yan adawa a ƙasar nan.

Taohon daraktar NGF ya koma ADC

A wani rahoton, kun ji cewa tsohon babban daraktan kungiyar gwamnonin PDP , kuma tsohon dan majalisar wakilai, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyya.

C.I.D. Maduabum ya ce ya bar PDP saboda jam’iyyar ta ɗauki wata hanya ta daban da ta saɓa da tafarkin da ake kai a baya.

Ya ce a yanzu, PDP ba ta da karsashi, sannan ta tsunduma a cikin.rikice-rikicen cikin gida da suka hana ta ci gaban da ake buƙata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262