PDP Ta Yi Wa Shugaba Tinubu Saukale, Ta Hango Makomarsa a Zaben 2027

PDP Ta Yi Wa Shugaba Tinubu Saukale, Ta Hango Makomarsa a Zaben 2027

  • Jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya ta taso shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a gaba kan salon mulkinsa
  • PDP ta bayyana cewa Shugaba Tinubu ya zama baƙar haja a wajen ƴan Najeriya saboda yadda yake gudanar da mulkinsa
  • Jam'iyyar PDP ta bayyana ƴan Najeriya marasa kishin ƙasa ne kawai za su sake zaɓar Shugaba Tinubu a zaɓen 2023

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar adawa ta PDP ta sake caccakar shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Jam'iyyar PDP ta bayyana Shugaba Tinubu a matsayin zaɓin da bai dace ba ga ƴan Najeriya yayin da ake tunkarar zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027.

PDP ta caccaki Shugaba Bola Tinubu
PDP ta ce Tinubu ba zai kai labari ba a 2027 Hoto: @OfficialPDPNig, @DOlusegun
Asali: Twitter

Sakataren yaɗa labarai na ƙasa na PDP, Debo Olugunagba ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a ranar Litinin, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

NNPP ta yi bayani kan sauya shekar shugabanninta azuwa ADC a Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me PDP ta ce kan Shugaba Tinubu?

Ya bayyana cewa PDP ita ce kaɗai jam’iyya da ke da ƙarfin kayar da Shugaba Tinubu da kuma jam’iyyar APC.

"PDP ita ce kaɗai jam’iyyar da za ta iya sauke APC daga mulki. Muna da goyon baya, muna da jama’a, kuma mun samu karɓuwa a faɗin ƙasa baki ɗaya."
"Babu wata unguwa ko gari da babu ƴaƴan PDP, domin kuwa PDP jam’iyyar talakawa ce. Ƴan Najeriya na matuƙar fatan dawowar PDP kan mulki."
"La’akari da kura-kurai da gazawar APC da dama, zan iya cewa babu wani ɗan Najeriya mai kishin ƙasa, ko wata ƙungiya ko wata jam’iyya da za ta goyi bayan Tinubu a 2027."
"Gaskiya ne cewa Shugaba Bola Tinubu baƙar haja ce. Don haka babu wanda ke fuskantar wahalhalu irin waɗanda muke fuskanta da zai sake kaɗa ƙuri’a gare shi."
“Tinubu baƙar haja ce kuma shugaban ƙasa ne wanda zai yi wa’adin mulki ɗaya kacal."

Kara karanta wannan

Duk da suna cikin hadaka, El Rufai da Peter Obi sun ki komawa ADC, an ji dalili

- Debo Olugunagba

PDP ta yi raga-raga da Shugaba Tinubu
PDP ta hango makomar Tinubu a 2027 Hoto: @OfficialPDPNig
Asali: Twitter

PDP ba ta damu da masu ficewa ba

Game da sauya sheƙar wasu mambobinsu zuwa jam’iyyar APC da kuma sabuwar haɗaka ƙarƙashin tutar ADC, Ologunagba ya bayyana cewa:

“Jam’iyyarmu jam’iyya ce mai ƙarfi wacce ke da karɓuwa sosai. Abin da ya kamata a fahimta shi ne cewa mutanen da suka gina jam’iyyar ba su sauya sheƙa"
"Ba su sauya sheka saboda yunwa ko rashin tsaro ba."
"Mutanen da ke da rinjaye a jam’iyyarmu, da kuma ƴan Najeriya da ba su da ra’ayin wata jam’iyya, suna fatan ceto daga PDP. Don haka, ba su sauya sheka."

Gwamna Kefas ya musanta shirin barin PDP

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya musanta jita-jitar da ke nuna yana shirin barin jam'iyyar PDP.

Gwamna Agbu Kefas ya bayyana cewa bai da wani shiri na shiga jam'iyyar haɗaka watau ADC wacce ke samun karɓuwa.

Kara karanta wannan

"Nan ba da jimawa ba," Wasu gwamnonin adawa sun shirya sauya sheƙa zuwa APC

Ya bayyana cewa biyayyarsa ga PDP ba mai yankewa ba ce kuma bai da niyyar komawa wata jam'iyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng