NNPP Ta Yi Bayani kan Sauya Shekar Shugabanninta zuwa ADC a Katsina

NNPP Ta Yi Bayani kan Sauya Shekar Shugabanninta zuwa ADC a Katsina

  • An yaɗa wasu rahotanni masu cewa shugabannin jam'iyyar NNPP a matakin ƙananan hukumomi 34 na Katsina sun sauya sheƙa zuwa ADC
  • Shugaban NNPP na Katsina, Alhaji Armaya'u Abdulkadir, ya fito ya yi fatali da rahotannin waɗanda aka yaɗa a kafafen yaɗa labarai
  • Ya bayyana cewa jam'iyyar APC mai mulki a jihar ce ta rasa mutanenta bayan sun koma ADC amma ba ƴan NNPP ba ne

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Katsina - Jam’iyyar NNPP ta fito ta yi magana kan jita-jitar cewa shugabanninta a matakin ƙananan hukumomi 34 na Katsina, sun koma ADC.

Jam'iyyar NNPP ta bayyana cewa babu ɗaya daga cikin shugabanninta a ƙananan hukumomi 34 na jihar Katsina da ya sauya sheƙa zuwa ADC ta ƴan haɗaka ko wata jam’iyya daban.

NNPP ta musanta sauya shekar shugabanninta
NNPP ta ce shugabanninta ba su koma ADC a Katsina ba Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso
Asali: Facebook

Shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Katsina, Alhaji Armaya’u Abdulkadir, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin a Katsina, cewar rahoton jaridar Vanguard.

Kara karanta wannan

Duk da suna cikin hadaka, El Rufai da Peter Obi sun ki komawa ADC, an ji dalili

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me NNPP ta ce kan sauya sheƙar shugabanninta?

A cewarsa, shugabannin jam’iyyar a matakin ƙananan hukumomi ba su sauya sheƙa zuwa kowace jam’iyya ba a faɗin jihar, rahoton The Guardian ya tabbatar.

Ya ce hankalin jam’iyyar ya kai kan wasu rahotanni da wasu kafafen yaɗa labarai suka wallafa kuma suka bazu a kafafen sada zumunta.

"Hankalin reshen jam’iyyar NNPP na Katsina ya kai kan wasu rahotanni da wasu kafafen yaɗa labarai suka fitar, waɗanda suka yaɗu a kafafen sada zumunta."
"Rahotannin sun bayyana cewa shugabannin NNPP na ƙananan hukumomi 34 sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar ADC."
"An ruwaito cewa sauya sheƙar ya faru ne ta hannun tsohon sakataren gwamnatin jiha, Alhaji Mustapha Inuwa, a jihar Katsina.”
“Sai dai abin da yake bayyane shi ne cewa wasu daga cikin shugabanninmu sun sauya sheƙa zuwa APC bayan zaɓen shugaban ƙasa na 2023."
"Don haka, waɗannan mutanen nan suka sauya sheƙa zuwa ADC daga APC. Saboda haka a zahiri sun sauya sheƙa ne daga APC, ba daga NNPP ba."

Kara karanta wannan

"Nan ba da jimawa ba," Wasu gwamnonin adawa sun shirya sauya sheƙa zuwa APC

- Alhaji Armaya'u Abdulkadir

ADC na ƙara samun ƙarbuwa

Batun sauya sheƙar dai na zuwa ne yayin da jam'iyyar ADC ke ƙara samun karɓuwa a tsakanin ƴan siyasa.

Jam'iyyar ADC ta zama sabuwar amarya
ADC na ci gaba da samun mambobi Hoto: @ADCNg
Asali: Twitter

Manyan ƴan siyasa dai daga jam'iyyu daban-daban na ci gaba da yin tururuwar komawa ADC wacce tauraruwarta ke haskawa a halin yanzu.

Gwamnan Taraba ya musanta shirin komawa ADC

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Taraba, Agbu Kefas, ya fito ya yi bayani kan batun shirin sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa ADC.

Gwamna Agbu Kefas ya bayyana cewa ko kaɗan bai da wani shiri na barin jam'iyyarsa ta PDP wanda ya lashe zaɓen gwamna a ƙarƙashinta a shekarar 2023.

Ya bayyana cewa zai ci gaba da zama a PDP kuma biyayyarsa ga jam'iyyar ba za ta yanke ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng