Duk da Suna cikin Hadaka, El Rufai da Peter Obi Sun ki Komawa ADC, an Ji Dalili
- Jam'iyyar ADC ta soki yadda wasu gwamnonin APC ke takurawa jagororin ƴan adawa a Najeriya
- Sakataren ADC ya kuma yi bayani kan dalilin da ya sanya Nasir El-Rufai da Peter Obi ba su koma cikinta ba
- Mallam Bolaji Abdullahi ya bayyana cewa tsofaffin gwamnonin biyu suna cikin tafiyar haɗaka ta ƴan adawa kuma za su shigo ADC
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jam’iyyar haɗaka watau ADC ta yi Allah-wadai da takunkumin tafiye-tafiye da aka sanyawa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi.
ADC ta bayyana cewa hakan ba dimokuraɗiyya ba ne kuma yana nuna yadda salon mulkin danniya ke ƙaruwa tsakanin gwamnoni na jam’iyyar APC.

Source: Facebook
Sakataren riƙon ƙwarya na ƙasa na ADC, Mallam Bolaji Abdullahi ya bayyana hakan yayin wata ganawa da ƴan jarida a ƙarshen mako a birnin Abuja, cewar rahoton jaridar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mallam Bolaji Abdullahi ya kuma bayyana dalilin da yasa har yanzu Peter Obi da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ba su shiga jam’iyyar ta ADC a hukumance ba.
ADC ta nuna yatsa ga gwamnonin APC
Sakataren na ADC ya bayyana damuwarsa kan abin da ya kira mugun salo na gwamnonin APC na hana shugabannin jam’iyyun adawa ziyartar jihohin da suke mulki.
“Najeriya ƙasa ce mai ƴanci, kuma kowanne ɗan ƙasa na da ƴancin yin tafiya a cikinta. Ba ma buƙatar takardar izini (biza) don ziyartar jihohinmu."
- Mallam Bolaji Abdullahi
Ya zargi jam’iyyar APC da amfani da dabarun tsoratarwa da danniya kan ƴan adawa.
“Tunda APC ta kasa mayar da Najeriya ƙarƙashin jam’iyya ɗaya, sabuwar dabara da suke amfani da ita ita ce barazana da gargaɗi ga ƴan adawa da kada su shiga wasu jihohi. Hakan keta dimokuraɗiyya ne, kuma dole a ƙi yarda da shi."
- Mallam Bolaji Abdullahi
Yaushe Peter Obi, El-Rufai za su shiga ADC?
Game da jinkirin da ake samu wajen rajistar Peter Obi da El-Rufai a matsayin mambobin jam’iyyar ADC, Mallam Bolaji Abdullahi ya ce an ba su lokaci su kammala wasu ayyukan siyasa da suka rage a tsofaffin jam’iyyunsu.

Source: Twitter
“An ba su dama su kammala wasu muhimman abubuwa da suka haɗa da zaɓen cike gurbi da kuma zaɓen ƴan takarar gwamna a cikin jam’iyyun da suka fito."
- Mallam Bolaji Abdullahi
Sai dai ya tabbatar da cewa shugabannin biyu suna nan daram cikin haɗakar ADC kuma za su shiga jam’iyyar a hukumance bayan sun kammala waɗannan tsare-tsare.
ADC ta ragargaji Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jam'iyyar ADC ta taso Shugaba Bola Tinubu a gaba kan wasu naɗe-naɗen muƙamai da ya yi.
ADC ta bayyana cewa shugaban ƙasan na son ƴan Arewa su yarda da shi ne shiyasa ya dawo yana ba su muƙamai.
Sai dai ta bayyana cewa mutanen Arewa ba za su bari a yaudare su da waɗannan ƴan ƙananan muƙaman ba.
Asali: Legit.ng

