Taron APC: Tinubu Ya Shiga Tsaka Mai Wuya game da Zakulo Magajin Ganduje

Taron APC: Tinubu Ya Shiga Tsaka Mai Wuya game da Zakulo Magajin Ganduje

  • Fadar shugaban ƙasa na cikin rudani wajen nemo wanda zai maye gurbin Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban APC na ƙasa
  • Masu ruwa da tsaki na APC sun kasa cimma matsaya kan wanda ya dace ya karɓi shugabancin jam’iyyar daga yankin Arewa ta Tsakiya
  • Tsofaffin ‘yan CPC na neman a ba su dama su fitar da sabon shugaban jam’iyya domin tabbatar da adalci a tsarin siyasa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Kafin taron kwamitin NEC na jam’iyyar APC da za a yi Alhamis, fadar shugaban kasa na fuskantar kalubale kan wanda zai maye gurbin Abdullahi Ganduje.

Majiyoyi sun bayyana cewa ana shirin tabbatar da Bukar Dalori a matsayin shugaban rikon kwarya, kafin a zaɓi sabon shugaba a watan Disamba.

Ana ta cuku-cukun neman magajin Ganduje a APC
Masu neman kujerar Ganduje ta APC sun kara yawa. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

Yadda addini zai yi tasiri a zaben shugaban APC

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Ɗan majalisar wakilai ya bi sahun Atiku, ya fice daga jam'iyyar PDP

Ana cewa tsohon gwamnan Nasarawa, Sanata Tanko Al-Makura, na iya rasa wannan dama saboda la’akari da addininsa a cikin jam’iyyar, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wasu jiga-jigan jam’iyyar suna ganin kamata ya yi a nada Kirista domin rage korafe-korafen da suka biyo bayan zabukan baya.

Ana kuma tunawa cewa zabin Ganduje a baya ya haifar da cece-kuce saboda ya kasance Musulmi kamar shugaban ƙasa da mataimakinsa.

Sauran masu neman kujerar daga Arewa ta Tsakiya sun haɗa da Sanata Joshua Dariye da tsohon shugaban PDP, Cif Barnabas Gemade.

Gemade daga jihar Benue ya gana da masu ruwa da tsaki a sakatariyar jam’iyyar a makon da ya gabata domin nuna sha’awar sa.

Sai dai, ana zargin tuhuma kan Dariye na iya hana shi samun amincewa, kodayake an wanke shi daga laifukan da aka tuhume shi da su.

Ana cigaba da neman magajin Ganduje a APC
APC ta kasa cimma matsaya kan wanda zai gaji kujerar Ganguje a APC. Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje.
Source: Twitter

Ana cigaba da neman magajin Ganduje a APC

Wasu gwamnoni suna son a rushe kwamitin NWC gaba ɗaya domin sake farawa daga tushe da nada sababbin jami’an jam’iyyar.

Hakanan, akwai wani yunkuri daga ministocin Muhammadu Buhari na baya da ke son su maye gurbin na yanzu da waɗanda suka fi biyayya ga gwamnoni.

Kara karanta wannan

PDP ta yi babban rashi, tsohon ministan shari'a ya sauya sheka zuwa jam'iyyar ADC

Har yanzu dai, babu cikakken matsaya daga Arewa ta Tsakiya kan wanda zai wakilci yankin domin maye gurbin Ganduje a shugabancin jam’iyya.

Wani mamba na kungiyar jiga-jigan Arewa ta Tsakiya ya ce su ba su da ɗan takara ɗaya, kuma har yanzu ba su gana don yanke hukunci ba.

Yayin da wasu ke goyon bayan Dalori ya ci gaba a matsayin riko, wasu na neman a maye gurbinsa da Kirista daga CPC ko yankin Plateau.

Ce-ce-ku-ce da Ganduje bai tarbi Tinubu a Kano ba

Kun ji cewa hankulan jama'a sun koma kan yadda Dr. Abdullahi Umar Ganduje bai samu damar tarbar Shugaba Bola Tinubu a jihar Kano ba.

Sai dai tuni tsohon shugaban ma'aikatan gwamnatin Kano Muhammad Garba ya fitar da bayanai a kan dalilan rashin ganin Ganduje.

Garba ya jaddada cewa Ganduje yana da kyakkyawar alaƙa da Tinubu, kuma murabus dinsa bai shafi haɗin kansu da jam’iyyar APC ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.